Kuka Afnan ta shiga yi tana nuna Yaseer din da ya shigo wanda shi ma kansa mutuwar tsaye ya yi yana kallonta, sai dai sanin abunda ya aikata ne ya san ya ya yi tamkar bai taɓa ganin wata irin halittarta a duniya ba.
Ganin haka nan ya sanya Afnan ta yi kansa tare da riƙe kwalar rigarsa kallo ɗaya zaka yi mata ka gane ba ta cikin hayyacinta.
"Wallahi Allah shi ya yi min fyaɗe. Mommy shine wanda nake baku labari, kuma shi ne ya ce ya fasa aure na bayan ya yaudare ni. Wallahi Yaya Ibrahim shine ba ƙarya nake yi ba. Wayyo Allah na Yazeed ka cuce ni ka ci amanta"Ganin haukarta ta yi masa yawa yasa ya buge mata hannayen da ta riƙe rigarsa da ita.
"Ke kinada hankali kuwa? Ke wace ce, meye haɗina dake da zakimin sharri? And who is the damn Yazeed you are referring me to"
Ya faɗa cikin ɗaga sauti yana mai ture ta, ta faɗi ƙasa."Calm dawn Yaseer, zo ka zauna ina tunanin bata da hankali yarinyar ko kuwa ta samu ruɗani ne a zuciya. Yanzu ta ƙare fadin cewa Yazeed ne ya mata fyaɗe kuma ganinka yasa ta ce kai ne and most confusing part tana kiran ka sunan da ba naka ba. Police zan kira su zo su fitar min da su daga gida" cewar Alhaji idanuwansa kan Afnan da ke tashe da ƙasa tana kuka.
Jin abunda ya ce ne ya sanya Afnan ɗin sake sanya wata uwar ƙara tare da fashewa da wani matsananci kuka, mai ratsa zuciyar mai sauraro.
Sosai abun ya ɗaure mata kai. Cikin ranta tambayar kanta take yi, me ke shirin faruwa da ita ne? me yasa Yazeed zai mata haka? ta ya ya Yazeed ɗin da ta sani zai koma mata wani Yaseer? Anya kuwa ba mafalki take yi ba!
Gigitaccen marin da aka ɗauketa da shi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta. Sake ɗaga hannu ya yi ya sake ɗauketa da wani marin Wanda saida taga wuta. Ji yake yi yau ko kasheta zai iya yi saboda wannan tozarcin da ta ke shirin yi musu wato bata ma san wanda ya yi mata ciki ba it mean karuwanci take abunda ya tsargu cikin kansa kenan.
Nuna ta ya yi da yatsa cikin tsananin fushi da ɓacin rai.
"Kin cuce mu Afnan, kin cuce kanki, kin kuma cuce kauna da tarbiyar da mahaifinmu ya baki" ya ƙarasa maganar cikin wani irin rauni.Mommy kam tunda ta zauna banda hawaye ba abunda take yi. Duniyar baki dayanta ta yi mata zafi.
Miƙewa ta yi tsaye tana dubin su Yazeed ɗin da suka zuba ma ikon Allah ido suna kallo.
"Dan Allah bayin Allah ku yi haƙuri da Abunda ya faru, ku yi haƙuri ban san ta inda zan fara neman gafararku ba. Ku yi haƙuri kar abun nan ya kai ga police sunan mahaifinta ya ɓaci na roƙeku da girman Allah ku yi haƙuri" ta fada daƙyar tana jan nunfashi saboda ƙarancin sa a tare da ita.jin yanda take maganar ne ya sanya Ibrahim ya yi saurin dubanta sai dai afin kace me ɗaga kafarta keda wuya ta sulale ta faɗi ƙasa somamma. Da sauri Ibrahim ya yi kanta da yana jijjigata.
Afnan da ke tasaye baki ɗaya kasa yin komai ta yi ɗakin kansa duhu ya ke yi mata. wata irin juwa take gani, ga wani irin matsanancin ciyon marar da ya taso mata lokaci ɗaya.
wata irin ƙara ta ƙwala tare da zubewa ƙasa. Nan take jini ya fara bin ƙafafuwanta.
Ibrahim kam ya ruɗe iya ruɗewa rasa ma ya yi ko kanwa zai yi, ga mahaifiyarsa ga ƙanwarsa. Haƙiƙa duk tsanar da ya yiwa Afnan sai ya ji yanayin da take ciki tana buƙatar taimako.
Ruwa Yaseer ya yi saurin kawo masa ya zuba wa Mommy amma ko alamar motsi ba ta yi ba. Ganin haka yasan ya, Ibrahim ɗin cewa.
"pls Yazeed Ku taimakaa min mu kaisu asibiti dan girma Allah"Yazeed da har zuwa lokacin haushin Afnan yake ji sosai cikin ransa saboda ta yi mishi abunda ba a taɓa yi masa irinsa ba, duk da cewa an masa makamancinsa amma ko alama bai kai wanda ta yi masa ba.
Yaseer kuwa wani irin tausayinta ne ya kama duk sassa da ilahirin jikinsa. Sai dai ba yanda ya iya. Saboda ya san ba yanda za ayi yace shi ya yi mata ciki a zauna lfy.
Alhaji kansa jikinsa ya yi sanyi ganin wannan tashin hankalin. Shi ya yiwa su Yazeed magana kan su taimakesu.
Cikin motar Ibrahim aka sanya momy yayin da aka sanya Afnan cikin motar Yaseer suka nuface asibiti.
Direct emergency aka nufa da su don ceto rayuwarsu bama kaman Afnan da taketa bleeding.
Cikin ikon Allah momy ta farfado sai dai jininta ya hau sosai don harma yafi na Daddy hawa.