🌹🥀🌷
*ƘWARƘWARAH*
🌼🏵️🌺{ITAMA MATAR SARKI CE}
_LOVE TRIANGLE♥️_
Mai_Dambu
Oum-Muwaddah5️⃣
Tafiya ta kama sarki Jalaludeen zuwa bakin iyakar inda yake mulka, tafiyar da kai shi har iyakar Nijar a tafiyar ne ya had'u da wasu fulani, dake mutum ne me daɗin zama, abinda ya zaunar da shi bayan ya sayi nono, ba komai bane sai Rumanah! Dan tunda suka haɗu ya ganta da kayan saƙi, tunda ya ganta hankalin shi ya tafi gareta, dan ganin farko ya fad'a sonta, amma babu yadda ya iya dan matan shi huɗu ne, kuma ya rufe kofa.Sarkin Pada shi ya bashi shawara ya karb'eta a saɗakarshi, dukda yaso k'in amincewa, sai da sarkin Pada ya samu nasara akan shi, har ya nemi ta, su kuma iyayen ta suka bashi ita.
Lokacin bata wucce shekaru sha huɗu ba, haka yazo ya sakata a cikin matan shi dukda ita bata cikin su.
Sai da ya barta ta cika shekara sha bakwai, sannan ya sanya Jakadiya ta kawo mishi, ita.
..... Har wani al'amari me girma ya shiga tsakaninsu.
A sannu komai yake tafiya, bayan lokaci me tsayi dan har Sarki Jalaludeen ya cire tsammani da samun d'a namiji sai gashi Fulani ta Haifa ita kuma Rumana ta rasu.
A Ƴaƴan shi mata tara ne sai Jamal na goman su.
Rukayyah,Hadizah, UmmulKhair, Zakiyah, Raihanah, Hafsah, Sai Ummi Salmah, A'isha, Sai Jamalah, Jamal,
-----
Kwalla ya goge sannan ya ajiye alkalami hannun shi, yana me kurawa Table din d'akin kallo.
Murmushi yayi, a yaran shi yafi son Jamal da Jamalah, sai Raihanah sune kad'ai yake jin dadin su, amma Rukayyah da sauran Yan uwanta baya jin daɗin su, asalima nunawa suke yafi kaunar su Jamal ko. Sam baya jin dad'i irin kallon da amma zai cigaba da musu addu'a.
------
Tun bayan sallah Isha na kwanta ina goge kwalla na, gefe d'aya ina tuna iya rayuwar da muka yi da Annah, a hankali barci ya fara dauka na, har dai yayi nasarar
Yin gaba dani.Ji nayi an tab'a ni, a hankali na buɗe ido, fili na gani sai wata mace da wasu gungun mutane sun kewaye wani mutum me sanye da fatar b'auna, sai kan shi da ya makala. Kan damisa, yana tsaye, juyawa take tana niman tsira babu hanya,
"Lallai Zulumi! Ka aikata kusakura wanda zai jagoranci al'ummar kasar ka, ka kyale ni na tafi inda maka fito."
Dariya ya saka sosai sannan yace.
"Ziriya! Ban tab'a alkawari ban cika ba"Kuka tasaka sannan ta zub'e kan gwiwar ta, ta shiga rera kuka .
Shigowar wani dattijo sanye Da Kayan saki da hula me habb'ar kada, yasa kowa ya juya.
"A'ah! Zulum! Ita din tankar Abin bauta ce! Dan haka ka kyale mu zamu bar maka kasar ka."Dariya ya saka har da mutanen da suke gurin, sannan yace.
"Dole sai na cimma burina! Dan na mai da ita ƙwarƙwarah ta, har na tsawon kwanaki yanzun kuma zan karasa abinda nayi niyya, dakaru ku kame min Sarkin bokaye."Daga nan ban kuma fahimtar abinda ya faru ba, sai dai naga wata mata tabi wani hanya na daban dan haka nayita Binta, sanye take da doguwar riga Ja idan tana tafiya rigar na jan kasa sannan yana fidda ruwan jini....
Yadda take tafiya a hankali gashinta har gadon Bayan ta, ga wani irin kambu na zinariya akanta, a haka muka Kure bango masarautar, inda naga wani kyakyawar doki fari tass dashi, sai wani kujerar zinari, ga wasu mutane a durkushe a gabanta, zama tayi a kujerar.
Kanta da a sunkuye gashinta ya rufe fuskarta.

YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...