6️⃣2️⃣

2.3K 852 53
                                    

*https://my.w.tt/Jq0zlG7qs8*

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹

6️⃣2️⃣

Raina b'aci yake amma babu yadda na iya, sai na share batun shi na mai da hankali na guri guda.

  .     A wani tsautsayin da ya kuma faruwa wanda na shiga cikin al'amarin dumu dumu,  dan faruwan yaje min tashin hankali da Kawu.

         Ba komai bane sai barin da Sarah tayi na cikin da suka gama kwalafa rai a kai, sabida kafin faruwan abun nice Nazo najata Muka fita.

           Bayan dawowar mu, Ni na koma gida ita kuma ta dawo daga nan bazan iya cewa ga abinda ya faru ba.

   Sai dai wannan karon ina kwance naji an fincikoni, tare da sakar ina mari, hagu da dama.

     Sosai ya fusata, yana fadin.
"Gaya min meye na tsare miki da kike sanadin zubda min da cikin mata na"

Wallahi ji nayi kamar saukar aradu ce, domin kuwa ban san kome ba, yake tuhumata.

      Jana yayi zai fidda ni a gidan Raihanah ta sha gaban shi cikin ɓacin rai tace.
"Gidan mijina ne! Kuma gidan marikan Jannart, kai ya dace mu kora! Sannan da ka daketa meye ribarka."

"Eh ai dole ki fadi haka, tunda da bakin ki aka lalata min cikin mata na wallahi bazan yi kafara ba sai na raba abinda tayi min sai na sanyata zubda kwalla kamar yadda ta sani.

     Alhamdulillah da ban sameta a matsayin matar aurena ba, da ban san abinda zata aikata min ba, ki rubuta ki ajiye kema kin kusan kukan da kika samu muka yi.

   Mara asali da tushe, ai dole ki aikata hakan waye yasan ahalinki? Babu shi yasa masu iya magana suka ce tsintarciyar mage bata mage.

Wallahi na kuma ganin ki da mata na sai na miki abinda ko sunan namiji aka kira sai kin rufe kanki a d'aki.

  Sai na lalata miki duniyar da kike tunkawo da shi, dan haka kar na kuma ganin ki a gidana.

In ba haka ba zaki yi na dama mara amfani, jahila wacce ta manta da ikon Allah, kin zubda na farko ban yi magana ba, shine bari ki kuma na biyu, ai zuciyar zinari gare mu.

    Ance ba a sonki mara asali kawai."

Haka ya gama masifar shi ya fita, Ni kam shiru nayi ina kallon Hanyar da yabi, sam kaina ya kulle, taya zan zubda cikin Sarah?

    Me yasa hakan yake faruwa ta sanadina, marin da yayi min bai dame Ni ba kamar zargin da yake min. Ni tsorona daya kar ya rabani da ita. Domin idan ya gaya mata abinda yake zargina da aikatawa.

    Sarah bazata tab'a yafe min ba,  zama nayi a bakin gado bayan na koma daki, kuka na zauna nayi duk maganar da Mamah tayi min ban kulata ba.

     Yau nake jin kewar gida, sabida gorin da yayi min yau nake jin da zan san dangina dole na koma gare su, na gaji da gorin da Kawu yake min, ina dalili zai sanya ni. A gaba da gori ba.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz