ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦhttps://my.w.tt/ngUvKpKtO7
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹3️⃣6️⃣
Kamar mai martaba yasan shirin Jamal, bai kuma bin takan shi ba,
Sai da yazo gaishe shi sannan yace mishi.
"Kasan makaho baya sanin ana kallon shi..."Gyada kai yayi, cikin nazarta maganar Abban shi, kafin ya d'ago kan shi cikin nutsuwa, idanun shi na iyalin kwalla yace.
"Abba na tuna!"
Murmushi Mai martaba ba yayi, sannan yace.
"Ko kadan ban rike ka ba, amma kasan idan farauta taki maka, kunkuru ma tsare ma harinka yake, sabida baka yiwa tafiyarka shiri na musamman ba"Bai ce kome ba, dan bashi da abincewa.
Haka mai martaba ya gama mishi wanka me kama da jurwaye.---
"Rumanah! Itace matsalar mu, domin bamu isa cutar da yaron nan ba, matukar muka ce zamu yi haka toh tabbas wukar yankar giwa."Tana kishingide ta sake murmushi sannan tace.
"Ba girma gare shi ba"Jakadiya ta karshe da cewa.
"Sai kaifin Bala'i! Yaron nan yana da, taurin kai, duk abinda ya same shi bai sanya shi ya furta yana son Yarinyar ba, dukda da kuwa ta..."D'aga mata hannu Fulani tai, tare da take fuskarta, sannan ta nuna mata hanya dole Jakadiya ta bar cikin zauren, ranta yana kara b'aci. Wato dan an sami damarta shine bari a dinga wulakantata.
Fita tai tana kwafa tare da cikin alwashin sai ta rama abinda aka mata.....
Zaune yake a gaban Rumanah, ya tallafi fuskar shi da hannun shi duk biyu daga ita har shi an rasa wanda zaiwa wani magana.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.
" Bahaushe yayi gaskiya da yace!
Sai wani ya rasa, wani ke samu, toh k'i dinbun Alkhairi dake tattare da yarinyar gashi nan an baka mata hudu lokaci guda.Sannan shima Jalaludeen ai ba haka ake rayuwa ba, taya kana matashin ka, ace zayi maka Auren gata, ai bai dace ayi irin wannan abin ba, lokacin sun wuce.
Dukda ba zai rasa dalilin shi nayi haka ba, amma mata hudu a lokaci guda, ba abu me sauki bane.
Idan shi yayi haka ne, dan ya horaka ai haka ya isheka ishara, Yarinyar nan tayi maka biyayya, ka hanata sauraron kowa, amma daga baya kace kai nan duniya baka sonta, wallahi baka kyauta ba.
Yau gashi abinda ake gudu ya faru, da baka san waye mahaifinka bane shi yasa kake tunanin zai janye maganar shi, baya saka doka ya karya.Kuma baya magana biyu, gaskiyar da ya faɗa itace gaskiya..bai yi Kuskure a hukuncin shi ba, sabida iya gaskiya ya bika da ita.
Nayi Imani da Allah, da yau kayi hakuri ka fadi JANNART kake so, babu wata macen da zai kara maka ita.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...