ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹https://my.w.tt/nMtVrtRkd8
5️⃣5️⃣Yadda take bani labarin, rayuwar shi da matar shi sai ya bani tausayi, musamman yadda matar ta bada rayuwarta da kome nata akan shi, amma bai sanya shi ji soyayyarta.
Shi yasa data rasu sai da yayi jinya sosai, ya zama ko mace ya gani yana matuƙar girmama al'amarin ta.
Ya kuma dauki soyayyar duniyar nan ya daurawa Anih Fatimah khatoon. Yana matukar son Yarinyar kamar me.
Haka kawai naji a raina, zan iya kare rayuwata dashi, a hankali na isa kafad'arta na sauke kaina ina ina murmushi na rufe fuskana nace.
"Mama! Zan zauna dashi a haka."
Dariya tayi sosai sannan tace.
"Allah ya shirya min ke! Nima zanyi farin cikin kasancewar ki dashi.Aryan Sultan, kiyi hakuri da abinda bakina zai fada amma iya gaskiya zan fada miki, Aryan karshe ne. Domin kuwa Mutum ne da yasan ciwon kan shi, ya kuma san darajar Mutane.
Kozan kwana na wuni bazaki fahimci kome ba, kiyi ƙoƙarin gano abinda yake da ra'ayi akai."
Kusan har muka gama aikin kome sannan na wuce d'akinmu.
Tunda na zauna nake nazarin abinda Mama ta gaya min. Shiru nayi ina nazarin fuskar shi. Wanda banga kome akai na sai nagartan shi. Da kamala.
Na hango abubuwa da lokacin bazai bani damar nayi dogon magana akai ba, amma gaskiya ya hadu ba karya Aryan Fari ne, dogo mai matsakaicin jiki.
Fuskar shi dogo ce, wacce ta kawatu da dogon hanci, tare da wani saje wanda ya haɗa da yar gashin bakin shi.Ajiyar zuciya na sauke, tare da jin wani irin abu ya tsaya min, da na tuna yanayin shi da Kawu na.
---
Karfe goma na safe, su Kawu suka iso, daga tashar jirgin motar ma'aikatar su tazo daukar su.Tunda ya shiga, ya zauna kamar wanda aka mishi wani laifi, ya fara cin magani.
Karfe sha daya da rabi suka isa gidan su wanda yake, Agege.
Gidan ya haɗu sosai, domin kuwa akwai kome a cikin gidan, dan haka abinda ya fara, zuwa yayi ya nima musu abinda zasu ci.
Yana kawowa, ya samu Nanah tana barci.
Wanka yayi tare da mik'ewa shima, domin sunyi sallah tun a jirgin kasa.---
Daura...
"Hmm Allah ya ki yashe mu tab'ewa.Ratsa unguwa, a haifi kamarka!"
Wani irin kallon Fulani tayiwa Jakadiya.
"Me haka yake nufi?!"
Gyara zama Jakadiya tayi, sannan ta shiga rabtab'o bayani.
"Wato Fulani Rumana!"Dakatar da ita, Fulani tayi cikin zafin rai tace.
"Karki kuma kawo min abinda zai dame ni, ke bakin ki bayi fadin Alkhairi ne? Baki da burin sai fadar sharri.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...