KYAUTA TA HUƊU

916 98 5
                                    

https://my.w.tt/rGAadG5E59
MAGAJIN IZZAH!!!

   {CIGABA KWARKWARAH}

  

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
  Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

      Fatan Alkhairi gare ki Mame na group ɗin Bagudu 😍🌹
_Gare ku masoya na rage muku daga 400 zuwa 300 kamar yadda wasu suka buƙata zan kara yawan free Pages din zuwa goma Insha Allah_
     

HUƊU

Cikin lokaci ƙalilan na fara koyarwa, bawai dan albashin ba a'a, sai dai haka yana matukar rage min kewar Muhid, sosai na maida hankali na sosai akan abinda nake.

              Shi yasa sam ban kuma damuwa da kowa ba, sai dai haka kawai muna cikin wannan yanayin Sai ga Baraq ya shigo rayuwata.

           Tun daga ranar da na ganshi, a daren na kwana ina mafarkin shi, inda nake ganin shi kwance cikin jini.

Washi gari haka na tashi babu walwala, tunda na nufi makarantar na daure fuskana tam, duk yadda naso kauce Mishi sai da ya shige min.

                  Haka muka tashi ban sake mishi fuska ba, duk yadda naso kar na shiga rayuwar shi, ina Baraq ya gama shigewa rayuwata. Shi yasa naki shi yayi juyin duniyar akan naso shi naki.

     Yakan sani a gaba yana kallon tare da ce min.
"Fatimah meye laifina?! Ko dan bamu da arziki ne?!"

     Girgiza kai nayi, sannan na zuba mishi ido, kafin na bude baki nace.
"Kawai bana jin kome akan ka ne! Kuma da zaka taimaka min ka daina damuna zai fiye maka Alkhairi."

   "Toh an tab'a kin mutum babu dalili ne? Ki gaya min meye matsalar ki da ni?!"

     Mik'ewa nayi ina duba agogon hannuna, sanan nayi wuccewa ta na barshi a gurin tsaye. Yana mamakin yadda nake gudun shi.

       ---
Baraq Nafi'u! Ya addabi rayuwata, yadda ya kai kanshi gurin Baabi ya bani mamaki, dan haka ba iya gurin Baabi ba, sai da ya gama zage dangin mu, na cikin masarautar, da nuna musu yana kaunata.

    Su kuma suka mara mishi baya da taimakon Baabi, zama nayi a gaban Baabi, ina kuka wanda tun rasuwar Muhid ban kuma haka ba, kallona yayi sannan yace.

          "Toh Mamana meye na kuka haka indai Baraq ne, zan ce me ya hakura, kuma zan nima miki wanda ranki yake so! Amma ki duba dakyau yaron yayi kokari domin kowa a cikin zuri'ar mu, ana son shi dan haka kiyi hakuri ki amince ayi abin."

Cire kaina nayi cikin kuka nace.
"Baabi! Tsoro nake ji! Ina tsoron abinda ya faru da Muhid don Allah baabi na kayi wani abu."

    Jikin shi ne yayi masifar sanyi, tare da kura min ido, yana me jinjina maganar da nayi, amma da ya tuna. An hana shi camfin abinda zai faru, dani sai ya zuba min ido na wasu lokuta kafin yace.
"Za ayi auren ki daina sakawa a ranki wani abu zai faru saboda babu kyau canfe!"

Da haka Baabi ya kashe bakin maganan ya kuma hanani cewa kome, na cigaba da zubda kwalla, ba tare da na amince ba Baraq ya shiga niman aurena, tare da goyan bayan Baabi na, sabida lokacin, na kai shekaru ashirin da biyar, dan bayan na gama bautar ƙasa, nadan zauna na shekara daya, toh yanzun fara aikina ma yana niman shekara biyu.

      ..tun ina nunawa bana so, har ta kai na hakura, sabida Baraq akwai son sanya mutum a walwala. Haka kuma Iyayen shi, suma sunyi godiya sosai da irin karb'an da aka yiwa ɗan su.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن