ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹2️⃣0️⃣
"Ya Allah! Nayi tawassali da sunayenka tsarkaka, Ya Allah ka kawo mishi dauki, Ubangiji bamu da tsimi bamu da dabara, Ya Allah kaine gatan mara gata, Ubangiji ka kawo mashi dauki, Ya Allah! Indai Jamal jini ne a jikin shi ya Allah ka tsiratar da rayuwarshi "
---
Ruwan addu'o'in Mama ta shafa min, ajiyar zuciya na sauke tare da fashewa da kuka nace.
"Mama! Kawu"
Shafa kaina tayi cikin damuwa tace.
"Don Allah! Ki daina Irin wannan abubuwan, tashi muje kiyi wanka."Dakyar na tashi sannan na nufi dakin mu nayi. Ina barin cikin su duk suka juya kan Raihanah da tambaya,
"Raihanah!!! Ina kika sami yar bori? Lokaci d'aya ta koma aljana?!"
Yadda Yayunta suka zuba mata idanu yasata jin wani irin fargaba, nan tayi musu bayanin da tayiwa Umma, kuma suka gamsu.
Koda na fito daga wanka na sami kayan mu nida Aliyah, sakawa nayi gudun kar mamah ta shigo, na zauna shafa stalle mai me gurguwa wanda aka hada da man zaitun da habbatu saudah. Ina gama shafawa zuciyata sai bugawa take sosai kamar zata bar gangan jikina.
Haka na shirya na fito. Kallona Yaya Rukayyah tayi sannan ta kauda kanta, cikin Izgilanci tace.
"Raihanah! Ita wannan Yarinyar bata da kyau sosai, kawai dai tana da tsarin jiki me kyau, da zance ko za'a bawa, Sadeeq ne."A tsorace na kalleta zuciyata tana lugude.
Ina kallon Mama ta tsuke fuska sannan tace.
" Akwai kyakyawa a gari har makotar ƙasar nan zaku iya Niman su, ita din mallakin wani ne. Idan na ga wani da sunan yazo zan sab'a mishi har wanda ya turo shi."Tana gama fad'ar haka ta nuna min hanyar fita, da sauri na wuce gaba muka fita, jikina babu kwari muka nufi inda mata ke zama.
Tunda na zauna a hankali na dafe goshina, ina jin hayaniyar jama'a. Ji nake Kamar kaina zai buɗe. Har aka fara wasan, bani jin daɗin zaman gurin.
Kifa kaina nayi ina jin wani irin a jikina, ga kuma ciwo da kaina yake. A hankali hawaye ke zuba a idanuna, sosai ƙoƙarin danne kuka na nake, Ni kaina ban san dalilin kukan ba, amma nasan yana da nasaba da ganin wannan matar, tashi nayi da sauri na bar gurin, da ido Mama ta rakani. Ina fita ban zame ko ina ba sai can inda Bayi ke zaune ina shiga zauren da zai kai Ni gurin su, kawai sai na d'imauce. Ganin zauren nayi ya koma min kamar wani shahararren pada wanda aka yi shi tsawon lokuta me tsayo, cikin padar kuwa cike yake da kayukan kwarangwal, sai kuma jini da yake gudana, mata da maza ne a duke daga su sai d'an fatar b'auna ko kura, gefe can wani yagwalgwalen tsoho ne a duke yake tafiya, matar nan tana zaune gaban wani mutum, yana gyara mata gashinta, kura musu ido nayi cikin mamaki, dan kamar zahiri kamar mafarki, juyowa tayi ta kalle ni, sannan ta juya abinta suka ci-gaba da abinda suke, ina son nayi magana na kasa, sabida harshena yayi matuƙar nauyi sannan kuma na kasa motsawa, domin ji nake kafaffuna kaman an daure min su, a hankali naga babu kowa a cikin fadar sai matar da mutumin ya dauketa, suka shiga wani guri kaman mayafi aka ja musu, shigowar wasu mutane da gudu tare da wasu muggan makamai, suka shiga sararran mutumin, wanda suka fidda shi, sai lokacin na lura rabin shi daga cikin shi zuwa sama mutum ne, rabin shi zuwa kasa ta dawakai ne! Cikin wahala yacewa wani mutum wanda kan shi yake sanye da kan damisa.
VOUS LISEZ
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Fiction HistoriqueA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...