ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT😊ɓɑ ɳɑ Բiyɛ ki ɓɑ ɑɳ cɦɛ ɗɑ kɑʀuwɑ "ɦɑwѳ gɑɗѳ"
ѳuɱ ɱuwɑɗɗɑɦ🌹
1⃣5⃣
*_Assalamun Alaikum_*_Da fatan d'akina zai isa gareka cikin amincin Allah! Da farko abinda zan fara cewa shine Allah ya jibanci al'amuranka! Yayi maka albarka cikin rayuwarka baki daya, yasa ka gama da duniya lafiya! Alhamdulillah ko yau na mutu bani da tararradin abinda na bari zai tsaya domin kwatowa dinbin Al'ummar shi hakokin su! Naji dad'in yadda ka gigita duniyar Shamaki domin naga madarar tsoro a cikin idanun shi! Sannan wani abin alfahari a yau goyan bayan da kasamu daga wasu masu rawanin da suke cikin Padar! Jamal Allah yayi maka albarka! Sai dai ina jin tsoron takaddiranci Shamaki! Idan da hali rijiya ta ba da ruwa guga ya hana! Da wannan nake maka fatan Alkhairi_
Daga
Mahaifinka
Jalaludeen AminullahMurmushi yayi sannan yace.
"Abbana kenan! Ai wukar yanka Giwa ba girma gareta ba, sai kaifi! Akan Shamaki kake shirin hanani zuwa gida! Shikenan naji Abbana, sai dai me kaya ya k'iyayye mai zamani"Haka yayita juyar maganar har lokacin sallah yayi.
*
Tsakurar abincin nake wanda Samim ya kawo mana daga gidan Yayar shi da take aure, a unguwar sunusi, dan can ta tura su Aliyah da Halifa, ajiye abincin nayi nace.
"Mama na koshi?"Kallona tayi na wani lokaci sannan ta tab'e baƙi, kafin tace.
"Ina kyautata zaton Jamal zai tawo anjima, kuma idan yaga baki cikin abinci akwai matsala!"Kallon abincin nayi sannan na shafa cikina wanda yake had'e da baya, kwalkwal nayi da idanuna nace.
"Allah cikina fashewa zai idan naci abincin nan dukka"Bata kuma kula Ni ba, har likita ya iso, ya gama dubani sannan ya bamu sallama.
Muna cikin shirya kayan mu ne, Samim yazo tunda yace min.
"Ya jikinki?!"
Nace da sauki ban kuma kula shi ba har muka tafi inda motar da yazo da ita, muna shiga tace mishi.
"Jiya nake lissafin dawowar Yayanka"Murmushi yayi sannan yace..
"Insha Allah! Yana dawowa Sai karin matsayi! Daga nan sai a maidaku Lagos dan nafi tunanin haka""Babu inda zani! Ina da yara da suke karatu bazan so a kasa musu hankali ba,"
"Har da Sarauniya ta?!" Ya tambayeta yana satar kallona ta madubi ina kwance bisa kafadar ta,
A hankali suke zantawa har muka iso gida, ina fita daga motar na kwashi kwandon da aka kawo mana abincin, na shige cikin gidan ina jin kaifin kallon shi a jikina, da sauri na shige cikin gidan.
Dakin mu na wuce na zauna dan saurin da nayi na gaji, kwanciya nayi tare da lumshe idanuna, ina kara girma jinin dake zagaye a jikina, Jinin Yarima Jamal. Murmushi nayi tare da gyara kwanciyata.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...