ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦhttps://my.w.tt/ngUvKpKtO7
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLA4️⃣1️⃣
__________________________________
"A'ah Jannart! Wallahi Jamal ya gane kusakuran shi, kuma a shirya yake ya gyara gaba, ki bashi damar haka!"
Shiru nayi ina kallon ikon Allah! Kafin na mike, har zan bar falon sai na juyo. Tare da zuba mata ido nace.
"Amma! Kinsan babu yadda zai yi dani! Kawai."
Kad'a kai nayi na wuce abuna, ban kuma ce mata kome ba,A ranar ta samu hada kayan mu, zuwa daura dan halarta bikin shi, da safe muka nufi filin jirgin sama.
Dan Abban su Aliyah ya biya ta jirgin zamu tafi.
Tunda na shiga na zauna na zubawa tagar jirgin ido, zuciyata na soyuwa.
Nice sani bikin Kawu, wanda ya tsallake ni, hmm nifa alamarina da sauki. Domin kuwa na Kawu yafi nawa muni.
......
Tunda suka bar Lagos, Aswad ya shiga boye wata takarda, kamar wani abun arziki. Can ya buɗe ya rufe. Tare da sake murmushin mugunta.Sannan ya kalli Jamal da gefen idanun shi. Yaga shima ya sakalo kai sai ya rufe.
Haushi ya gama cika shi, juyawa yayi yana kallon Aswad yace.
"Uban me kake b'oyewa? Shugaban munafukan daura!"
Ya fada tare da tsare Aswad da ido,Murmushi Aswad yayi, sannan ya cigaba da boye takardan shi, har suka sauka, a filin tashi da saukar na katsina.
Motar masarautar ce tazo daukar su.
"Wato idan na sami Jannart a matar aurena na ca....""Ka dai kwala asara, yarinyar da abokinka yake ajiyewa dan kanshi kake tunanin cewa kana so wallahi kayi faduwar bakar tasa"
"Eh na yarda guntun goro. Yafi katon dutse! Ba dani zaka yi bita da kolle ba, dukar kabarin kishiya"
Shiru Jamal yayi dan ya fahimci maganar banza ya gaya mishi sannan ya cigaba da cewa.
"Kuma muna nan da kai za ayi bikinmu, a kaita gidana na gurje amarc"Shake wuyar Aswad yayi yana huci.
"A gidan Uban waye zaka ka gurji amarci, Aswad meye na tsare maka? Na rantse da Allah! Sai Allah ya bi min hakkina."Dariya da tausayin Jamal ya cika mishi zuciya, amma yaki ya nuna kawai ya matse sannan ya cigaba da amayar mishi da tarin kaunar da yakewa Jannart.
Tsabar bakin ciki, ji yaƙe kamar zuciyarshi zata fita a kirjinshi, kafin wani lokaci zazzaɓi me zafi ya rufe shi dan tabbas yasan ya rasa Jannart har Abada.Tunda suka shiga masarautar yaƙe tafiya a hankali, kamar zai fadi.
Shashin Abba ya nufa, tare da zuɓewa. Jikin shi yana sauke wata irin gajiyayyar murya wacce take niman tallafawa yace.
"Abba! Karka hukuntani da laifin zuciyata ta aikata.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...