9️⃣2️⃣

1.7K 378 44
                                    

KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

_Ingantaccen Zumar goran Tula! Maganin rage kiba! Maganin kara kiba! Maganin gyaran Boons! Karki ji kome tuntube mu ta wannan Number +2348030861857! Sayan  na gari mai kudi gida_

9️⃣2️⃣

     " Ina zan ganta! Ya kake son nayi da rayuwata? Me yasa aka haife ni a cikin masarautar nan?"
  Cikin tashin hankali da damuwa ya juya zai koma cikin gida ya juya harshen turanci yace!
"An haife ni domin kaddara tace! Ba dan naji dad'i a rayuwata ba! Dan haka kowacce mata ta koma gidan iyayen kai kuma ka shirya ka nufi Kano! Idan bata Kano ka karasa Bauchi ka duba min ita!

       Idan kuma na rasata! Toh bazan yafewa kaina da zuciyata ba, domin ita amanata ce!"

     Daga haka ya nufi cikin gidan, rai a b'ace, kirjin shi yana wani irin bugawa, kwalawa Yahanasu kira yayi, cikin mugun b'acin rai.

"Maza ku tattara kowacce ta bar gidan nan, Kafin raina ya b'aci nayi muku abinda baku tsammata ba! Maza ku fita"

Ya daka musu tsawa, da sauri suka shiga dakin su. Suka dauko matakan su, suka nufi cikin gidan, zama yayi zuciyarshi tana zafi yana tambayar kan shi yaushe zai daina ganin bldamuwa a cikin rayuwar shi.

     Shiru yayi tare da zubawa, kofar Jannart da Sarah ido, ga baki daya ji yaƙe yana dana sanin abinda yayi a rayuwar shi, domin Sarah tayi gaskiya duk abin ya faru yana da kaso me girma! Shi yasa yanzun yake jin zai iya gyara rayuwar shi, dakin shi ya mike ya nufa.

      Zuɓewa yayi a saman gadon, yana kuma jin b'acin rai, tun yana karanta wasikar kaki har barci yayi gaba.

           Zaune take sanye da fararen kaya, fuskarta kunshe da murmushi, hannunta na dama wani katon abin hannun azurfa ne tayi kyau, rabon sallar ta har wani sheki yake. A gajiye ya isa gareta, ta mika mishi hannu ya zauna kusa da ita.

       "Kiga yadda gurin nan yayi kyau! Sai kace dausayi."

      Murmushi tayi sannan tace.
"Shi yasa ka kasa rike amanar da na baka? Kawu na! Sarah amanarka ce me yasa kake wulakantata. Sarah tana sonka! Addu'a nayi Allah ya amsa min me yasa kake son shiga tsakanin abinda Allah ya haɗa!

     Kawu karka manta ko yayya Sarah taka ce! Ba zaka iya rayuwa babu ita ba! Don Allah ka nimota ka riketa da amana! Sannan nauyin al'umma yana kanka, su kansu matan ka suna da hakki akan ka, me yasa kake ƙoƙarin raba zaman lafiyar gidanka da na Al'umma, karka manta nauyin su da yake kanka yafi karfin kwatance."

   Tana gama fad'ar haka ta bar wajen ta nufi wata hanyar da zata sadata da cikin wani kayataccen lambu.

"Jannart!" Juyawa tayi tare da sake mishi murmushi, sannan ta juya tana mishi adabo, mik'ewa yaƙe son yayi amma yaji kamar an daure shi, dole ya zauna yana gani har ta b'ace mishi, a firgice ya farka dai-dai sallamar Umma.

    Mik'ewa yayi ya fito ya ganta ta sako tumakan matan shi a gaba, sake fuska yayi tare da niman guri ya zauna, fada tayi mishi sannan ta kuma daura da nasiha, bai iya hakuri ba ya gaya mata abinda suka mishi.

"Basu da laifi! Kaine me laifi! Da ka nunawa kowacce mace zaman ka take babu yadda za ayi su cutar da ita! Ka mai da yarinyar mutane baiwa mara yanci, bayan dukkan su. Suna da yanci karka kuma aikata kuskuren da zaka dawamma kana dana sani mara amfani.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Kde žijí příběhy. Začni objevovat