7️⃣5️⃣

2K 399 28
                                    

https://my.w.tt/56WTRCeYl9
KWARKWARAH

      {ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

           _Don Allah zaka min Uzuri domin mun shiga karnin da maguzawa suka buga mulkin su, kafin Zuwan Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo! Dan haka kar aji na yanko wata arniyar Ashariya 🙄😱🙆🏻‍♀️bA fara cewa She started domin labarin yazo da haka Please mu ba yara bane! Balle ace za ayi tunanin rashin da'a please 👏🤝_
7️⃣5️⃣

Karni na goma..

Sarakuna biyu sun gwabza yakin da ya kusan tashin larduka guda biyu.  Lardin Kano da Lardin Daura. Wannan fadar ta sanya daura yin nasara akan kano, sakamakon goyan bayan da Sarkin Kazaure ya badawa Daura.

           Wannan abin ya tab'a kimar masarautar kano, inda suka ji faduwar gaba akan tunkarar wata lardin da yaki.

    Dan haka sarakunan Sokoto da Zazzau, suka shirya wata yar karamar tattaunawa, akan bai dace ana yakan juna ba.

      Sarkin Zazzau mai suna, ilo shi ya mike cikin jinjina al'amarin kasancewar ranshi a b'ace yake, kallon Sarkin Sokoto Tanko yayi cikin jin haushi tace.
"Tsabar tashin hankali da rashin hankali irinta mato da Bala, yan malafar uba, wai yakar juna suke yoh ban da karewa lalacewar duniya har takai su yaki juna sabida rashin mafada.

      Toh na rantse muku da mutsutsu gobe shiru, bazan iya ganin wannan babakeren jar uban ba, kai yau naga tanbad'a da lalacewa. Toh mato hito fili nan katsaya inyaso sai ku kar juna hankalin ku ya kwantar."

            Cikin b'acin rai sarki Tanko yace.
"Rabu da yan bujen Uba, banda sarkarranci, yo Ina kasar daura ina ƙasar kano, ai tsutsan nama ai tama nama, Mai hali , mai sabo. Dan haka kar na kuma jin wani dan gwafar Uban ya kuma jan tinga haura bisa dawakai ya yaki dan uwan shi, kuma shima Sarkin Kazaure zan tura mishi da sakon takara( bi ma'ana kashedi ko gargad'i)

         Kar na kuma jin bakin dan malafar geton uwa a cikin sha'anin sarakuna matukar bazai zama abokin sulhu ba.

    Mato kai da Salau, ku kiyayye mu, domin muka kuma jin wani da batun yaki, toh ba makawa mune zamu yake shi, kuma mu rushe daular shi mu kafa namu magajin Izzar muga ya zaku yi."

  Sai aka kawo takarda aka ajiye tare da yin amfani dashi gurin kafa sharad'in baza a yaki juna ba, wannan dalilin da kuma hatimin masarautun an sanya shine domin ya zama hujja da duk wanda zai kuma d'ago yaki.

      ..... Bayan shekaru biyar, da faruwan wannan al'amarin sarki mato na kasar daura, yana fama da jinyar rashin haihuwar da namiji, dan haka wani zuwan shi Kazaure, wani babban al'amari ya faru a hanyar dawowar shi, da matar shi Deluwa.

   Wannan abinda ya faru ya sanya Sarkin bakin ciki na fitar hankali, inda yayi ta bin yan fashin da suka tare su yayi ta sare su yana girbe su kamar dawa,

   Har ya shiga garin Kano, bai fasa sarar su ba, har suka isa dala. Inda gumkin tsububura take, bai fasa kashe su ba.

   Yana gamawa dasu ya takarkare ya kwatsamu ihu, a cikin garin sai da wasu daga cikin mutanen garin masu rauni suka shige gidajen su suka boya.

    Daga nan ya juya abinshi, yaje ya tadda deluwa tana kuka tare da boye kanta, sakamakon fyaden da shugaban yan fashin yayi mata, duk da sun kashe baki daya fadawan sarki Mato, sai bayin shi mata aka bari da Jakadiya, cikin bakin ciki da b'acin rai suka isa gida.

         Tunda suka isa gidan, Deluwa ta shige d'akin ta baci ba sha, har hakan yaso kasara lafiyarta.

          .... Tsakanin Jakadiya da sarki tare da wasu bayi suka san wannan al'amarin, sanin cewa bayi nada tsegumi, yasa sarki bada Umarnin a gine su a ganuwar Masarautar, babu tausayi bare imani aka gine su.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now