8️⃣2️⃣

1.7K 498 70
                                    

https://my.w.tt/FmKWqgEws9
KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

    Ga masu bukatar anko na biki ko suna, hada kayan leffe, sayan ɗai-ɗai ko sari! Zasu iya tuntube wannan manhajar whatsp! Lace! Material! Veils

wa.me/2349071442935
Follow our Instagram page
www.instagram.com/la_fashion_trends

Ga WhatsApp group na masu sari👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/Ew5omSsWIuF6I8oeJj1mbc

8️⃣2️⃣
Fitinar Sarah tayi yawa, shi yasa yanzun nafi bukatar na fita a gidan, sabida habaici da tashin hankali.

Sai tafi yawo, dukda ba wani waje bane, inda na koyi girki ne. Bai sani ba, ranar ya kwaso uzurin shi ya samu bana gida. Abin ya bashi mamaki.

Kawai ta zauna ta shimfid'a mishi karya, dan haka ina dawowa na hango motar shi, a cikin damuwa na shigo gidan.

   Tun daga kallon da yake min, ya sani jin tsoron abinda zai gaya min.
"Amma kinsan baki da ikon tafiya inda kika gadama ko? Ban san me kike dauki Sarah ba, da baki son zama da ita, bayan ita tanan matukar zaune dake domin Allah.

      Yanzun da na dawo duk tambaayr da nayi mata Dakyar ta gaya min, sabida kaunar da take miki amma ke tsabar kishi da bakin hali kin kasa fahimtar kome akanta, daga yau kar na kuma ganin kafarki a waje."

Daga haka ya juya ya koma dakin shi, nasan idan na shiga dakin shi bazai tab'a kula ni ba, shi yasa na wuce d'akina, ina kallon yadda take murmushin mugunta.

.... Har zan shiga daki na juya na kalleta sannan na gyara tsayuwana nace mata.
"Da alamu duniyar tana miki faɗa! Tana miki yadda kike so! Ni kuma takurani take sosai, Sarah zan baki mamaki, zan baki kyauta Mafi girma da daraja!

      Zan bar miki kome! Zan tafi inda zan kwanta cikin kwanciyar hankali, zan bar miki kome dan kiyi yadda so!

         Sarah nayi miki laifi, amma Insha Allah na miki alqawarin zan sanya ki kuka da dariya a duk lokacin da kika tuna Janny.

              Banji haushin ki! Sai ma Uzurin da na miki, na miki uzuri. Shima Kawun na mishi Uzuri.

           Laifin da nayi miki kuma ki yafe min, kiyi hakuri tafiyar ce take da nisa amma nayi imani da  saura kiris."
. Daga haka na juya na barta a tsaye. Ba ita ba hatta shi sai da jikin shi yayi sanyi, kallonta yayi cikin nutsuwa yace mata.

"Kina muzanta mata ne? Ko kina cusguna mata ne? Bana son tana ambaton mutuwar nan, idan kina mata abu ki daina, dan wani abu ya sameta zan baki mamaki."

       *Toh Ni meye nayi mata? Dan baka sona! Ita bafa matsayinmu daya ba, amma yadda kake nuna min kamar tafi ni daraja nan kuwa*

Daka mata tsawa yayi cikin zafin rai yace.
"Ina magana kinyi min shiru," sai lokacin ta dawo hankalin ta, tayi kasa da kanta tace.
"Kayi hakuri! Amma wallahi babu kome kawai ta fadi haka ne dan ta sanya maka zargina, kaga abinda Yasaka mata suke gudun a kawo musu wasu matan kenan.

            Bafa kishiya na dauketa ba."

     Na fashe da kuka, sannan ta wuce d'akinta ita da yaran ta, Ni kuwa numfashina ne ya keta hawa da sauka.

     Kamar bazan rayu ba, sai niman abinda zan musu alamar ina cikin tashin hankali babu har dai na fadi kasa, shima fita yayi a gidan, dakyar na iso bakin kofa.
Na shiga buga kofar.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now