KYAUTA TA BIYU

930 99 5
                                    

*https://my.w.tt/z5Z3LK0029*

MAGAJIN IZZAH!!!

{CIGABA KWARKWARAH}
(Fita ta biyu)

HAZAKA WRITER'S ASSO

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

_Fatan Alkhairi Maryam Kolo da Maman Ummite tare da Matar kakana! Hajja Rukky😍🌹_

BIYU
Da gudu nabi bayan shi tare da rike rigar shi cikin kuka da tashin hankali nace.
"Don Allah ka rufa min asiri! Bani da kowa anan! Jay! Idan Yayarka kace a wannan halin zaka tafi ka barta"

Juyawa yayi cikin zafin nama, ya ture ni sai da na zube a kasa, na sake mik'ewa zan tashi har ya shiga motar shi ya bata wata irin wuta.

"Jayyyy!" Na kwala mishi kira! Tare da sake kukan da yafi nada karfi, ina da nasanin abinda na aikata a cikin shekaru uku da suka wuce, zuwa huɗu.

........
Aanih Fatimah Aryaan! Cikakken sunana kenan!

Shekaru ashirin da biyu baya..
(Kad'an daga cikin Kwarkwarah)
---
Cikin tashin hankali! Suka nufi asibiti da ni, ranar da aka sace Yarima Jalal, abinda aka fara shine kara min jini, abin mamaki jinin kowa yaki Dai-daito da jinina, sai da Aka dibe na Sarki Jaamal, aka gwada take jinin yayi daidai da nawa, hankali Baabina ya tashi, tare da Ummi, sai kaiwa da komowa suke.

Sai da na kwana na wuni, sannan na farka, ina tashi a firgice, na fara ihu, tare da niman inda zan b'oya. Sai da U mmih ta rungume ni, amma a haka na ture ta sabida karfin da yake shiga na, ihu nake tare da kiran sunan Jay! Tunda Baabi yaga matsalar haka take, sai yayi maza aka mai dani Sokoto.

Inda aka kaini shashin kakata, Umman Baabi. Tunda aka kira malamin masarautar, yana zuwa yayi min addu'a, sannan yace.
"Zaku yi hakuri zuwa gobe! Insha Allah zamu duba Alamarin."

Haka suka amince, dake na samu barci, har washi gari da malamin yazo shiru yayi sannan yace.
"Tabbas rayuwar mu da mutuwa duk na Allah ne! Sannan babu wanda ya tab'a zanawa kanshi ƙaddara! Sai dai ƙaddarar yarinyar nan ta shiga na shi.

Haka ya sanya masu faffutikar ganin cewa sun dauki fansa! Sun yi tarayya akan ta! Dukda ban san meye ba! Akwai matsala. Sai dai zamu iya magance abin da Allah ya nuna mana!"

Daga haka bai kuma magana ba, ya mika musu addu'o'in da zasu na bani, ina sha.

A hankali na soma samun sauki tare da samun kulawa daga Matan Babana! Ummi da Ammih.

.....
Bayan na warke na cigaba da zuwa makanta, kamar yadda na saba.

--- A masarautar Daura.

Gimbiya Sarah! Sai da tayi dogon jinya dan ya hadu mata da kewar D'anta da kuma ciwon zuciyar da yake barazanar kamata! Hakan yasa ta daina shiga cikin duk wani abinda yake faruwa a cikin gidan, dukda Abba Jaamal yayi kokarin fahimtar da ita! Hakan kaddara ce, dan haka su godewa Allah tunda ya basu wasu yaran.

Cikin zubda kwalla tace mishi.
"Don Allah! Kawu karka sani jin wani abu a raina domin, kuwa bana raba daya biyun, Akwai Sannun wasu manyan mutane na cikin masarautar nan!

Wanda dama basu kaunar mu! Taya zanyi hakuri bayan nasan akwai mutanen da ban san su ba, a bayan Inuwar mu!

Kawu bazan tab'a samun nutsuwa ba, sai naga yarona!"

Cikin damuwa ya zuba mata ido, tare da tausayinta, sannan yace.
" Zato zunubi ne! Kuma babu kyau don Allah ki cire tunanin wani zai iya cutar da shi."

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now