6️⃣6️⃣

2.4K 476 79
                                    

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹

    _Barka da Sallah! Da fatan anyi sallah lafiya! Allah ya maimaita mana! Ya kuma nuna mana na bad'in ba d'ad'a! Akwai masu mai da labarin Baya!  Ku dan nutsu sosai! Shi yasa nace ku rike code din! Sabida ina rud'ewa idan kuka tambaye Ni! Wacece kaza wacece kaza, ku duba labarin daga farko zaku fahimci kome!_

6️⃣6️⃣

   Borno...
_Duk rayuwar da zaka gina! Yana bukatar so da kauna! Sannan yana bukatar k'iyayya da bakin ciki! Sannan dole jigon shi ya zame hassada da kyashi..... Ya shugabana. Zan kasance maka tankar raƙumi da akala! Ya shugabana ni baiwa ce amma nasan a cikin bayin Ni mai daraja ce kamar yadda ka zab'e Ni Kwarkwarah a cikin sauran bayinka, Umarni ka ya isa biyan buƙatar ka koda kuwa haka yana nufin musayar rayuwa da mutuwa ce._

Matuƙa firgice ya farka yana haki yau ma bai ga fuskar ta ba, kuma yana tsaka da nutsuwa da ita take gaya Mishi wannan kalaman.
Wacece ita? Meye ma'anar haka, duk sai yake jin ya damu da ya san meke faruwa dashi.
Dan haka sauka yayi daga gadon.

Ya dauki littafin tarihin masarautar yana dubawa.

            *Shafin Sarauniya ziryana*
      Mace mai kyau da kyalkyali!
Macen da aka sadaukar da ita domin kasancewar ta....
A cikin karni na sha uku aka binne shi, duk da yayi yaki dan wanke kanshi amma hakar shi bata cimma nasara ba.

                      Kuskuren da zai sanya a kuma mai-maita kanshi, shine na kin sauraran Fairo akaro na biyu, haka zai bawa tarihin daman mai-maita kanshi, zai kuma bada damar sake fahimtar aininin gaskiyar labarin.

     Soyayyar mutum da Aljanan ba sabon abu bane, amma kyautar rayuwa da mutuwa itace sadaukarwa soyayya!

    In dai har zai iya sadaukar da Rayuwar shi toh Tabbas dole Ziryana ta bada nata domin ceto na wanda take kauna..

      Tsaki yayi cikin gajiya da karanta wannan labarin, me kama da taatsuniya.

   Ajiye Littafin yayi tare da kwanciyar shi.

             ---
Washi gari...
Bai fita fada ba, Qoiseh ta shigo mishi cikin shigar Alfarma,ta zauna a gaban shi.

             Kallonta yayi cikin nutsuwa, dan ya fahimci akwai damuwa a tare da ita.

        "Hmm!"
Gyara zama tayi sosai, kafin ta fara mishi bayanin kamar yadda zai fahimce ta.

    Allah sarki da sauri ya mike zuwa shashin Innar daga nesa ya hango ta kwance.

              Yanayin ta, yaso firgita shi, amma bai damu ba. Zama yayi yana kallonta, cikin wani irin SO da Kaunar gudar Yar shi daya Tal a duniya.

      "Rahil! Sannu, duk tsawon shekaru ban san kina nan ba, sabida lalurar da ta same ni! Insha Allah koda zan rasa kome sai na jinya ce ki"

     Lumshe idanu tayi ta bude akan shi. Sannan ta kuma rufewa a hankali.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Onde histórias criam vida. Descubra agora