ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹2️⃣5️⃣
.......
"Takawa! Ina ga ba wani abin d'aga hankali bane? Idan kayi dubi da Jamal din yana kwance koda ya tashi ba wani abu ya rasa ba sai idanu, dan haka ka bar d'aga hankalin ka, zai ji sauki"Cike da mamaki yake kallon Fulani Furerah, wacce take bayani kamar wata na Allah.
Murmushi yayi me ciwo dan yasan iya cutarwa Shamaki ya cuce shi sai dai ba komai Allah yana tare da shi, kamar yadda ya sashi cikin damuwa haka shima Allah zai jarabce shi da damuwar da tafi tashi.Shigowar Fulani Hasiyah ya sashi sauke ajiyar zuciya, bayanta Jakadiya ce rike da kwandon abinci, sai Yaya Rukayyah tare da Raihanah, da Yaya Shatu, wacce labarin faruwan abu ya isa har Zaria, sai kuma Khadijah.
Zama suka yi akan babban dardumar da aka shimfida a d'akin, gaishe da Mai Martaba suka yi tare da tambayar shi ya jikin kanin su, murmushi kawai yake musu, tare da nuna mishi Jamal ɗin.
Cike da tausayin Jamal din suke tattaunawa kasa kasa, yana jin su da yadda kowa ke kawo shawara, amma duk cikin su shawaran Raihanah ce yayi na'am da shi inda tace inda hali a fitar dashi koda kano ne balle ma sa a iya fitar dashi ƙasar waje.
Caaa suka mata kamar zasu cinyeta d'anye, yadda suka mata yasata fashewa da kuka, dan sun hayayyako mata, har Yaya Rukayyah tana cewa.
"Dan kin auri Me kuɗi sai aka ce miki kowa ma haka ne! Idan aka tattara kudin sabida jinyar shi dan son kai."Cikin kuka tace.
"Yaya Rukayyah Ni kam ban san laifin da muka miki ba. Ni da Jamal kina tadda fadar ki zaki ce ina son kai ko ina nuna nafi kowa son shi, dukkan mu ciki d'aya muka fito amma kulli yaumin sai kin nuna mana tsana, toh ko me ya kawo maganar miji da arziki oho, naga Kema mijinki me kuɗi har yafi Hamis. Amma kullum idanun ki yana kan shi.Wallahi Fulani keda Abba ku ja mata kunne dan gaba idan ta gaya min magana mara dad'i zan mata rashin kunya, tunda na fahimci rashin kunyar take buƙatar a mata."
Kurawa Yaya Rukayyah idanu yayi, cikin alamun b'acin rai ya nunawa Yaya Rukayyah hanyar fita da idanun shi.
"Toh Abba ba halin ayi ma Raihanah da Jamal Fad'a sai a nuna maka wariyar launin fata, sabida su fararre ne masu zubin Buzayen." Inji Yaya Rukayyah,
Mai da idanun shi yayi kan Raihanah, yana kallon har cikin ƙwayar idanunta, da fuskar ta daga nan har yatsun kafarta.
Juyawa yayi kan Jamal, yana nazarin maganar ta.
*_Masu zubin buzayen! Rumanah!!?*
Abinda zuciyarshi ya ambata kenan, sunan Rumanah.Zubawa Jakadiya idanu yayi, ita kuma ta takura gefe guda. Tana satar Fulani wacce itama take dafe da goshinta, sabida bakin cikin katab'aran da Rukayyah tayi musu, sai da ta haneta da saka Raihanah da Jamal a gaba, amma dake bata jin magana sai da yi abinda zai b'ata mata rai yanzun wata amsa zata bawa.
Mai martaba kauda kai yayi amma yasan ruwa bata tsami banza, da walakin goro a miya.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...