8️⃣3️⃣

1.9K 474 64
                                    

KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

    Ga masu bukatar anko na biki ko suna, hada kayan leffe, sayan ɗai-ɗai ko sari! Zasu iya tuntube wannan manhajar whatsp! Lace! Material! Veils

wa.me/2349071442935
Follow our Instagram page
www.instagram.com/la_fashion_trends

Ga WhatsApp group na masu sari👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/Ew5omSsWIuF6I8oeJj1mbc

8️⃣3️⃣
DAURA...
"Ka rufuwa kanka asiri! Dauko Yarinyar nan dai-dai yake da ajalinka! Dan haka ba gargad'in ka muke ba, shawara muke baka.

            Duk da kai ma ba kada sauki, amma ka bar yarinyar nan."

     "Kaga ajiye shawarar ka! Mulkina nake so! Kuma itace nake bukata ta dawwama, idan ta kama na kashe kowa toh ba makawa zan aikata hakan, idan kuma ta kama na kyale su zan kyale su.

         Ban san Hujjar ka na hanani kashe Aaryan ba, na barshi amma kullum zuciyata cikin barazanar cewa zai sha nake.

              Ba damuwa! Amma tilas a dauko min jinin Ziryana! Ko kuma"

.... "Ina me baka hakuri! Tabbas rayuwar ka tana cikin matsala, matuƙar ka dauko yarinyar tabbas zaka mutu! Dan haka idan kana ganin karya ne, zaka iya tafiya. Kai ɗaya ne a tare da kai, ita kuma uku ne, tare da mijinta.

      Kuma karshen mulkin zalunci da kake musu kenan,idan ka hakura babu me kwace maka mulkin ka."

       Kallon Bokan yayi sannan, ya juya cikin fushi ya bar dajin.

     ...... Bayan wasu awanni ya iso masarautar daura, abinda ya fara shine sanyawa a Nima mishi karti majiya karfi, ya kuma basu damar su tafi lagos, su sami daya babban yaron shi, ya nuna musu inda Jannart take su daukota.
Cikin kwana uku maza.

            ----
Lagos

Sosai likitan ya mai da hankali, gurin aikin kula dani, cikin kwanaki shida, Alhamdulillah na ji sauki sai shirya shiryen tafiya can cairo.

    A zaune nake, ina kallon Mama da Kawu, sai musu suke. Abinda ya bani dariya sai dariya nake ina bin bayan Mamah ta hanyar cewa.
"Gaskiya ne! Babu ruwana a cikin wannan shirin Kawu, Ina bayanki Mamah"

     Tasowa yayi ya tawo kaina, rungume ni yayi,. Sannan ya sauko da fuskar shi dai dai goshina ya sumbace ni yana cewa.
"Kinji bakin nan naki, Firdausih!"
   D'ago kaina nayi cikin murmushi ina kallon shi.
"Nagode sosai! gashi nan kina dauke da d'an mu, ko yar mu. Nagode sosai."

     Kunyar Mamah ya hanani magana sai boye fuskana nayi, cikin jikin shi tare da murmushi.

A bazata na d'ago kaina, ina girgiza mishi sakamakon gaya min da yayi wai za a cire min cikina.
"A'ah don Allah kar ku cire min shi, ka barni na haifi abuna, kaji Kawu, don Allah kar a rabani."

          Zama yayi dai-dai shigowar Sarah ya rike hannuna, yace.
"Babu me rabaki da cikin jikin mu, Insha Allah, bari na kai Raihanah gida na dawo tunda ga Sarah."

  Murmushi nayi sannan nace mishi.
"Duk wanda kace Sarkin dake mulkin birnin zuciyata"

        Jan kumatuna yayi sannan ya dube Raihanah da Sarah yace.
"Sarah bari naje na dawo, ga Jannynki nan."

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now