ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLA_Ina son na kuma tuna muku! Cewa wannan labarin yana tafiya ne kafin shigowar musulinci kasar Hausa! Duk da lokacin da musulinci ya shigo Sarkin Daura shi ya fara amsar musulinci! Kuma idan baku manta ba, nace muku rike code din shekarun da anyi ta amfani dashi, dan haka labarin yayi tafiyar bazata tun kafin zuwan Musulunci, sannan labarin yana nuna muku yadda aka yi imani da canfe! Da yadda akayi rayuwa da kwarkwarori! Ban tab'a cin karo da a kan labarin KWARKWARAH ba, sai yadda akace haramun ne! Har malam Abubakar Muhmood Gumi yace haramun ne, amma idan muka yi dubi da Mariyatul kid'iya! ita kwarkwaran Manzon Allah ce! Kuma ta haifa mishi Ibrahim! Dan haka sai na ajiye wancan batun haramcin, sosai nayi bincike akan labarina, dan haka ku bini a hankali, duk abinda ya faru daga 1370Ds zuwa 1875Ds, akan kwarkwarah ce,duk abinda ya faru akan samuwar kwarkwarah ce a cikin daular ce! Dan haka abin ya faru shakaru 200yrs da suka gabata! Ban tab'a labarin da yabani ciwon kai kaman wannan ba, dan haka zaku min uzuri sosai, dan matukar na kafe a hanya zan iya ajiye labarin sai farfaɗo! Da wannan nake baku hakurin Bazan cigaba da HABEESHAH ba! Kwarkwarah ce kawai zan cigaba da rubutawa Nagode for Long writerup 🌷🥀🌹_
4️⃣5️⃣Wannan wacce irin ƙaddara ce mara mafari, rungume jaamal yayi cikin matsanancin kuka, sabida tsabar tausayin.
"Wani irin bashi ne da ake son sai kun baya shi, kaunarku me zafi ce mara sarki da algus"
Kwalla yake zuba mishi sharr, abun gwnini tausayin.
Haka ya d'aga shi, ya kai shi har dakin shi, yana zaune dashi har aka kira sallar farko, sai lokacin ya farka da salati,A hankali ya mike tare da kallon Aswad da yake zaune kan dan drowar gadon.
"Aswad! Ina yarinyar nan take? Kira min ita, kuma ka tabbatar Khalil ya bar garin nan, dan babu wani abinda zanyi bikin ya kare."
"Don Allah! Ka sawa zuciyarka hakuri ka rungume matanka, ka bar rayuwar Jannyh ta huta, ina dalili zaka sanya yarinyar mutane a gaba da fitina.
Wa take dashi da zai tsaya mata, dan bata da galihu ai bata cancanci kyautar haka daga gare ka ba. Don Allah ka barta tayi rayuwarta tunda Allah bai hada ku a ma'aurata ba"Duk yadda naso yayi magana haka ya hakura, tare da zubawa sarautar Allah ido.
Bayan sallar asuba, ne yaki shiga cikin gidan, ya koma dakin shi.
Ni kuwa a shashin Abba na kwana ina kuka, shi kanshi ya ganin laifin kanshi a raba masoyan asali.
Sai da aka fito Sallah Aswad yazo ya rakani cikin gidan, a nan naga irin kallon zargin da ake min, kasancewar lokacin da Kawu ya ture ni na buge gwiwata.
Nan aka kuma ririta alamarin ya zama babban abu, kafin kace kwabo labarin ya tarwatsa cikin gidan da baki, ai Jamal ya keta min alfarma, shi yasa yayita ihu a gurin bikin shi, ya tsallake matan shi.

BẠN ĐANG ĐỌC
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Tiểu thuyết Lịch sửA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...