5️⃣2️⃣

2.7K 579 68
                                    

https://youtu.be/BF0xPPv4v-M

_BAHWA HAUSA NOVEL sunan Channel din_
Subscreb, like ,share and also comment , subscribe is free..

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._


https://my.w.tt/4hpOgA0V57

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍

5️⃣2️⃣
Tsaki naja a hankali, ina goge kwalla da take zubo min, na kuma hararar inda take tsaye kamar an dasa gunki, shiga motar nayi ina me kuma gargad'in ta sa ido.

Sake baki tayi tana kallona har muka bar gurin.

....
Har na isa inda nake koyan girkin raina bai huce ba, ba haka dai nayi na gama, karfe biyu na dawo gida na samu anyi baki. Baki a gidan, tunda na shiga naga wani hadaddiyar mota,

Mai tambarin hukumar custom, ina shiga da sallama naji gidan ya kaure da wani kamshin turaren ya daki hancina.

D'ago kai yayi tare da suke idanun shi a kaina, idanun mu cikin juna.

Kauda kai nayi cikin jin kunya, yadda ya tsare ni da ido.
"Ina wuni Abba?!"

Murmushi baban Aliyah yayi sannan yace min.
"Lafiya lau? Janny, ya karatun?"

Karamar murmushi nayi sannan nace.
"Alhamdulillah!"
A sace na gaida bakon bai kalli inda nake ba ya amsa, yana wasa da hannun Khalid.

Cikin rigima Muhsina ta iso gurina, Ni kuma ina ƙoƙarin cire takalmina.
"Yaya Janny! Kicewa Khalid ya bani abuna."

Dan kallon Khalid nayi idanun na ya sauka akan mutumin shima yana kallona, mikewa nayi na bar falon, jikina na rawa. Dan ina jin kallon shi har cikin kaina.

Ina barin gurin ya kalli Abban Aliyah yace.
"Mr Aryan! Itace wacce Muhsina take cewa sai ta faɗa mata ta zane ku."

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya kalli Abba yace.
"Yarinyar tayi min, da fatan baku mata miji ba"

Cikin wani irin jin dadi, Abban Aliyah yace Mishi.
"Alhamdulillah! Lallai Addu'ar Umma Allah ya amsa. Kana son Jannart!"

Lumshe idanunshi yayi sannan ya sauke akan hanyar da nabi.
"Jannah! Sunan ya dace da mai sunan. Tayi min amma zanje Sokoto na gayawa Sultan."

Ya fada a hankali, dan muryan shi kamar bazai iya magana ba, sabida sanyin murya.

Mr Aryan Sultan shine da na fari a gurin Muhammad Kabir na uku, sarkin Sokoto. Tun bayan rasuwar matar shi Fhadelah yaki aure kusan shekaru goma sha biyu kenan.

Abinka da gidan sarauta cewa akayi fatalwar matar shi ce take hana shi aure.

An nima Mishi mata daga gidajen sarautu har gidan manyan malamai da attajirai.

Amma fir yaki su, yau ganin Jannart, dan haka wani irin farin ciki ne ya kama Abban Aliyah, ya kasa hakuri ya kira Mama ya gaya mata.

Kirjinta ne yayi mugun bugawa, tayi murna amma idan ta tuna da alo tsiya alo danja, yasa jikinta yayi sanyi.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now