6️⃣9️⃣

2.5K 493 73
                                    

KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}


   HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.


Baki daya  labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

         _Am little Sorry 🤦🤭 na gaya muku koda page goma zan baku daily dole sai munyi hakuri dani 🙈😉_

6️⃣9️⃣
Sosai ake shiga da fita akan Jamal, amma yaki magana, karshe haka suka je kotu nan ma yaki cewa kome, har ran Alkali ya b'aci sosai, yayi mishi magana akan banda kimar mahaifin shi da yau sai ya yanke mishi zaman gidan wakafi dan ya koyi magana, mara mutunci kin magana yayi, haka suka tashi daga zaman yau.

                     Karshe abin ya zama wani iri. Ana cikin wannan halin aka wayi gari Shamaki ya mutu, kamar yadda aka kashe Aryaan, haka shima aka mishi, take aka sami alkali da batun, shi da kanshi yasa aka sako Jaamal mutuwar Shamaki ta girgiza kowa.

     Dan haka, aka shiga tunanin waye za a bawa mulkin, nan kuwa aka fara tunanin Jaamal, kwana uku da rasuwar Abdoul ya iso daura.

          Ranar da akayi addu'o'in uku, ana idarwa ya mike sannan yace.
"Alhamdulillah! Tunda anyi adfy uku, yau sai ku bani mulkina."

       Kallon shi Waziri yayi sannan yace.
"Kayi hakuri! Mulkin zamu maidawa Jalal ne, sabida Jaamal ne zai fi cancanta ya zama Sarkin "

        "Hhh! Lallai zaku isa garin da babu dan jagora, dan haka yau nace a bani gurin da mahaifina ya tashi."

              Cikin matukar mamaki, suka kalle shi, sannan suka ce.
"Kayi hakuri! Bazamu baka ba, bayan kowa yasan halin ka! Mahaifin ka...."
    Shake wuyar Wazirie yayi kamar zai kashe shi.
"Kai ji mana, ba dai mulki bane! Sauke shi an baka abinka Allah baya taya ka riko!"

            Inji Jaamal dan ya lura kashe mishi suruki zai yi, sauke shi yayi yana cewa.
"Maza ayi kome! Kafin mumman lokaci ya shigo."
    Kafa mishi ido Jaamal yayi kawai yana jin kamar ya tab'a jin irin wa wannan kalaman.

          Barin gurin yayi, a hankali ya koma shashin Nanah ya zube a jikinta, sabida gajiya, shafa kanshi tayi sannan tace.
"Jannart bata da lafiya! Kuma tana b'oyewa.

         Ko zaka je ka dubata ne? Wallahi tausayi take bani!"

           Lumshe idanunshi yayi, sannan a hankali ya furta "Ziryana!"

            "Abinci zaki bani naci wanda kika dafa da hannunki!"
       Mik'ewa tayi, sannan ta kawo mishi abincin a hankali yake ci, tana mishi hirar, kallonta yayi sannan yace.
"Zamu tafi karatu kasar India! Sabida damanmakin da ake samu ina ga gwara mu tafi da ita.

      Sannan sai wani dan abinda ya faru, gurin aikina ana dakatar dani, sabida wasu dalilai nasu, amma Alhamdulillah, tunda shugaban kasa yasa min hannu na tafi karatun.

            Dan haka ki shirya wata sati, zamu bar garin nan."

       "Amma har da Jannart ko?!"
"Eh sabida ita na zabi haka!"
Zuba mishi ido tayi tana mai-maita kalmar..
"Sabida ita ka zabi haka?!"
Gyada mata kai yayi sannan yace.
"Tana cikin damuwa! Shi yasa nake son Tayi nesa da gida."

       Dukda taso taki amincewa yadda yayi mata bayani a gwarance sai ta fahimci maganar shi, da yamma suka shigo duba ni.

     Ina ganin su tare naji raina kamar ya kama da wuta, amma haka na kumshe idanuna, kamar ina barci suna gama zaman su, suka fita.
   Saukar abu naji daga hancina, shafawa nayi naga jinie, murmushi nayi, cikin sanyin jiki na shige ban daki na wanke hancina. Kamar nace na duba madubi, wani irin tsoro ne ya kamani.
                      Mace na kuka jini na zuba ta hancinta da idanunta, har kunnen ta.
Zuɓewa nayi a gurin, ina fidda wani irin nishi, sabida jinin da yake zuba daga kasata.
A hankali idanuna yake rufewa,tana cewa..
"Lokacin ya iso! Karni zuwa karni! Daruruwan shekaru sun dawo!

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz