ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹Fatan Alkhairi! My @Aishadurling😍😘 Uwar dakin JANNART
2️⃣7️⃣
Girgiza kai nayi cikin nuna ba haka ba, nace.
"Ayya hakuri za'a yi dashi, domin kome aka mishi baza a tab'a burge shi ba. Asalima gani zai yi ai da yake da lafiyar shi babu wanda bai more shi ba. Sai yanzun da aka ga ya zama mara amfani shine za a juya mishi baya."
Kura min ido tayi na cigaba da mata bayanin yadda za a zauna lafiya dashi. Kuma na fahimci ta gamsu da baya."Toh idan aka ce ke ki zauna dashi zaki iya duk abinda kika lissafo min? Idan kece zaki zauna domin jinyar shi?!"
Zaro ido nayi waje! Ina girgiza mata kai sannan nace mata.
"A'ah Ni kam bazan iya ba! Dan bani da kwarin gwiwar kula dashi kina ga yadda kuma baku sha dashi ba sai nice zan iya kasassaɓar zama dashi ba."
"Zaki iya mana! Kuma idan kika yi hakuri burin dake ranki ne zai cika."
Girgiza kai nayi cikin damuwa na nuna bazan iya ba, kawai zan bi mama mu koma gida.
Tashi tayi ta isa bakin kofa, ta rike kofar tana kallona, sannan ta lashe bakinta kafin tace.
"Zaki iya!"Sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa, kwalla na ciko min ido.
D'agowa nayi da niyyar na mata magana, sai girgiza kai tayi sannan tace.
"Zaki iya fa! Kawai kina tsoron Jamal ne amma zaki iya shi jinya dole ka cire shakkar mutum da kuma, koma dai yayi ne kiyi hakuri amma tabbas kece zaki zauna dashi."Tana gama fad'ar haka tayi ficewar ta.
Dafe goshina nayi cikin damuwa, domin kuwa na yankowa kaina damuwa, dan nasan Kawuna ba sauki ne dashi ba.
---
Kallon shi Shamaki yayi a ranshi kuwa dariya yake, amma a fili fuskar tankar babu komai a zuciyar shi.
"Ina son ka shirya zuwa Yola! Kaje kaga yar Sarkin Haris"Idanun shi a lumshe kamar bada shi ake ba, yace.
"Ni bana son auren kowacce mace."Cikin fusata da jin haushi yace mishi.
"Sai wacce?!"Buɗe idanu yayi kafin uban, sai da shamaki yaja da baya. Jan da idanun shi yayi har wani wani irin haske.
"Kai lafiyarka?! Dubi yadda idanunka suka yi ja! Anyi maka wani abu ne?!"Tashi yayi zaune, yana jin haushin da yake ji kamar ya saka a kashe uban, amma ya rasa gane ta inda zai yi haka.
"Kawai ka kyale ni! Aure kuma ka nimawa kanka."Yana gama fad'ar haka ya ficce daga gidan, fita yayi daga cikin masarautar baki d'aya, da kafa yake tafiya shi kanshi bai san inda yake takawa ba, kawai tafiya yake.
Sai da yayi nisa da masarautar ya bi ta bayan masarautar inda babu yawaitar jama'a yaje ya zauna, shi d'aya ya zauna ya kurawa gurin ido. Sam baya cikin nutsuwar shi, abu d'aya yake bukata itace Mace macen ma Jannart.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...