2️⃣6️⃣

3K 352 29
                                    

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹

2️⃣6️⃣
     
    A cikin wata mota kiran kunkuru suka tawo, sabida lokacin babu mota me daraja irin ta. yana zaune a baya ana jan shi har suka shigo cikin asibitin.

           Dogarin dake tuka shine ya fito da gudu yaje ya buɗe mishi mota, kallon dogarin yayi cikin rashin mutunci yasa ka, kafa ya shure dogarin. Sannan ya fito dan haka kawai yake ganin wasu irin wucewar abubuwa a idanun shi.

      Fitowa yayi yana kallon ko ina, kamshin wani irin turare ya shaka. Wanda ya haifar mishi da kasala, jingina yayi da motar dogarin yana fad'in.
"Sannu, ranka shi dad'e! Takawarka lafiya toron Giwa! Lafiya dai gyara kin kitsi"

      Idanun shi a lumshe, aka yadinga ganin wasu irin abubuwan suna yawo kanshi, ganin Yan mata suna kewaye dashi. Daga su sai warki da ganyen da suka rufe kirjin shi.

     Wata fuska yake don shaidawa amma ya kasa fahimtar fuskar, gashi nan dai yana hangota kusan duk jikinta tsirara.

      "Yarima Abdul!"
     Da sauri ya buɗe idanun shi wanda suka yi mugun ja. Ya sauke akan Aswad wanda muke tare dashi. Janye kallon shi yayi daga Aswad ya zuba min ido, ji yayi zuciyarshi Kamar zata fado kirjin shi. Kallona yake kamar zai cinye ni.

     Haushi ya bani na wuce zuwa cikin asibitin, tare da Aswad suka shigo. Ina shiga naga fuskar Mama ta sauya, da alamun tayi faɗa.

      Komawa gefe nayi ina kallon kasar ɗakin, ina jin wata irin kunya da tsakuri, koda suka shigo. Gaida Mai martaba yayi cikin dan kunyar da ya aro.

     Sannan ya d'aga murya yana fad'in.
"Yarima Jamal! Ya jikinka? Naji ance Yayarka ta kalubalenci Gasar."

      Gyara zama yayi fuskar shi dauke da murmushi yace.
"Fata na gari ne, a gurin yake cika"

   Tab'e baki yayi cikin jin kai yana kallon kome na dakin sannan yace.
"Wai bishiya ce zatawa, kunkuru gorin kafa, kuji abin dari."

    Haushi ya bani ban san lokacin da naja tsaki ba.
"Mtseew!"
   Har cikin kunnen shi yaji tsakin, ji yaƙe kamar ya tab'a jin tsakin da jumawa sai bazai iya tuno adadin lokutan da yaji tsakin ba, amma Tabbas ya tab'a jin irin muryan. A fusace ya juya kaina na kuwa kafe shi da ido, yana son tuni wani abu amma da zaran ya kalli cikin idanuna sai yaga kamar ya san ni.

    
    "Ai kece mahaukaciyar da kika shiga filin da wancan ya fadi ko." Ya tambaye Ni cikin wata irin murmushi.

  Murguda mishi baki nayi tare da kauda kai nace.
"Mahaukacin suna dayawa!"
      Dab da fuskana yazo kamar wanda zai hade da fuskar mu, nayi maza na kauda kai na, ina b'ata rai.
"Dalla malam matsa min a gaba banda rashin hankalin irin na wasu mutanen kamar dabbobi suke"

        Dafe goshinsa yayi cikin mamaki, komai zai fito a bakin ta yasan shi da jimawa, babbar damuwar shi wani irin yanayi da yake fisgar shi akan ta, bai tab'a haduwa da macen da tayi mishi tsaurin ido kamar ya ba, sannan yadda yake ji halittar jikinsa na d'a namiji, yana harbawa shine yafi d'aga mishi hankali.

   Kamshin da yake fita daga jikinta yana sabunta mishi duniyar shi.

      Ba tare da yayi musu sallama ba ya ficce cikin tashin hankali, kan shi na sarawa.

      Koda ya shiga cikin motar ji yayi gaba d'aya nutsuwar shi ta d'a namiji.

        ......
   Cikin masifa da babu irin shi yace.
"Wato ke! Ban isa dake ba. Babu wanda ya isa ya gindaya miki sharad'i ki bi. Dan kin ga bani gani?"

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن