KWARKWARAH
{ITAMA MATAR SARKI CE}
HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.
Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹Ga masu bukatar anko na biki ko suna, hada kayan leffe, sayan ɗai-ɗai ko sari! Zasu iya tuntube wannan manhajar whatsp! Lace! Material! Veils
wa.me/2349071442935
Follow our Instagram page
www.instagram.com/la_fashion_trendsGa WhatsApp group na masu sari👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/Ew5omSsWIuF6I8oeJj1mbc8️⃣6️⃣ Kuyi hakuri nima na zaku na gama wannan labarin na huta! Zuciyoyin masoya su huta 😍🌹🤭
......
Duk yadda naso na bawa Sarah hakuri na mata bayani taki fahimta, sai ma kara botsarewa take........gashi k'asa-k'asa kishiyoyinta suna goranta mata, abinda yayi matukar d'aga mata hankali kenan tayi ta min wulakancin son ranta.
Jamal ya sameta dan ya fahimtar da ita taki sauraron shi, a nake ganin rayuwa, kome nice duk abinda take bukata na hana bayi su mata nike mata.
Ina fama da lalura ta fara rashin lafiya, kafin kace kwabo Sarah ta fita hayacinta abinda ya fara min shine wai Nice na kama kurwanta.
Anan saura sati biyu bikin sarautar Kawu. Haka nayi ta jigila da ita, har lokacin bikin aka gama bata leka ko waje ba, gashi tana kwance bai hanata kafta min rashin mutunci ba.
Haka zan lumshe idanuna, na yi kamar ban gani ba. Tana abinda taso. Amma naga kamar aron lokaci ne Allah ya bata. Bayan nadin sarauta da kwana biyu Aryan yazo.
Ban san me ya faru ba, amma Kawu yazo a fusace ya rike hannuna muka nufi inda Aaryan yake, zamu shiga na dakatar dashi, dan tun daga bakin kofar naji kamshin turaren shi, a hankali na shiga.
Na zauna ina kallon yadda falon yake,
"Jannart! Ciwo kike? Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Ya Allah Nagode maka, Jannart gaya min me ya faru dake."
. Murmushi nayi ina wasa da zoben hannuna, sannan nace mishi.
"Bani da lafiya ne! Amma da sauki. Bansan abinda ya kawo ba, amma yana na saba da halin da nake ciki!Aaryan na san kaji labarin Kome ba sai na mai-maita maka ba!"
"Naji! Sai dai KWARKWARANCI bai dace dake ba! Kema Y'a ce a wata masarautar! Naje na bincika na kuma sami labarin inda kike fito me yasa bazaki koma cikin danginki da Zuri'arki ba?!"
Gyara zama nayi sannan na kalle shi, nace.
"A gurin su ni bakuwa ce! A gurin shi kuma nice farin cikin shi, idan naje bazasu barni na dawo ba, zasu rike ni. Shi kuma zai kasa tsayuwa domin al'ummar shi. Hankalin shi bazai tsaya a guri ɗaya ba, matukar bana tare dashi kome zai faru.""Taya zaki fadi haka! Da zuri'arki da kome kina kaskance a nan!"
"A'ah! Kaskanci bane, kaddara ce. Ita ta kawo Ni nan! Kuma idan lokacin yayi zai dauke ni d'aga man. Don Allah ka tafi bana son ganinka!"Daga haka na bar falon, ban san me yasa nake jin bana son alakata tayi nisa da duk wanda zai min magana akan Asalima ba, na kori Ziryana yau kuma na kori Aaryan. Kawai nasan sabida.
Jamal da Sarah nake wannan abin Musamman ita da taki fahimtar zuciyata.
----
Ina tsaye gaban abincin da nake yi, naji an sanya hannu a saman cikina, komawa nayi da bayana na jingina a kirjinshi.
CZYTASZ
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
HistoryczneA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...