ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹3️⃣4️⃣
"Karka yi tunanin zan saurari koda Raihanah ce, bazan saurari kowa ba kai koda Fulani ce bazan saurare su ba, na baka dama nan da sati Uku kayi shawara da zuciyarka, abinda ka yanke dashi zan yi amfani dashi, Jamal wannan shine damar da na baka!!! Kaje kayi nazari akan Jannart! Na yaba da nagartattun halayyar ta, Jamal samun mace irinta zai yi wuya, ta sadaukarwa da farin ciki saboda kai, hmm Jamal kenan kaje kayi shawara da zuciyarka."
A iya fahimtar shi ran mai martaba ya kai kololowar ɓaci, amma dake yana son shi yaki nuna mishi, cewa bai damu ba.
Haka Jamal yayi mishi sallama ya fita.
_Kana dab da rasa damarka!_
Haka Umma tace mishi, Yau Jannart ta gaya mishi, kuma ga Mai martaba ya gaya mishi. Kai hatta Aswad ya gaya mishi kar yayi wasa da damar shi.Shi wata dama ce haka yake wasa da ita a iya sanin shi babu wata damar da yake wasa da ita, tunda Allah ya gani bai san komae ba, ita kanta JANNART baya jin komai akanta!
A hankali yake takawa har ya isa shashin bayi ya shiga, kai tsaye ya nufi dakin Umma, tun da ya shiga yayi shiru, kan shi a sunkuye.
Kallon shi tayi cikin damuwa sannan tace.
"Yarima Jamal?! Kana da matsala ne?!""Hmm" yace mata,
"Toh meke damunka?!"
Ta tambaye shi,
Gyara zama yayi sosai, kafin ya fara da cewa.
"Umma ni bani son Jannart!"
A hankali ya warware mata matsalar da yake ciki.Murmushi tayi sannan tace.
"Toh indai haka ne, ya kamata ta fidda miji tayi aure, dan babu amfanin ajiye baligar budurwa a gabanka!"Da wani irin sauri ya kalli Umma? Murmushi tayi sannan tace.
"Baka son ta auri wani? Kuma kai baka sonta? Anya kayi mata adalci? Kai fa Shugaba ne nan gaba. Tunda ba kayi ka bawa wasu guri su yi, amma kaje kayi shawara da zuciyarka!?"Shiru yayi cikin tashin hankali.
_Allah ka gani bazan amshi abinda bani so ba_
Ya fadi haka a zuciyar shi, mik'ewa yayi tare da mata sallama ya bar dakin.---
Fadar Shehun Borno...Kurawa Bulama idanu Kazeem yayi, cikin damuwa sauke tagumi yayi tare da ajiye idanun shi akan fuskar Bana, lumshe idanunshi yayi sannan yace.
"Kowace rayuwa akwai jarabta! Ni tawa jarabta, na manta abinda suka gaba ne! Iya tunani na rasa fahimtar meye na manta, amma tabbas akwai abinda na rasa me daraja! Shin kuda kuke y'an uwana bazaki tuna min meye na rasa ba."Shiru fadar yayi cikin jin haushi abinda ya sami dan uwan su, su kansu basu san ta yadda zasu mishi bayani ba, tunda an wani gari ne aka gan shi ya fadi a ban daki. Tun daga nan bai kuma fahimtar meke faru ba, kuma ba zai iya tuna komai na abinda ya shafi rayuwarshi ta baya akan gidan shi ba.
A yau yana zaune ne a matsayin Shugaban al'ummar Borno, amma a zahirance, dashi da babu duk d'aya ne! Tunda ko yau ya bar duniya bashi da Magaji.
![](https://img.wattpad.com/cover/219263309-288-k330621.jpg)
ESTÁS LEYENDO
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Ficción históricaA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...