2️⃣9️⃣

2.7K 351 41
                                    

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹

   𝘍𝘢𝘵𝘢𝘯 𝘢𝘭𝘬𝘩𝘢𝘪𝘳𝘪 𝘺𝘢 𝘪𝘴𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘪 𝘮𝘢'𝘢𝘣𝘰𝘤𝘪𝘺𝘢𝘳 𝘬𝘢𝘪𝘧𝘪𝘯 𝘣𝘢𝘴𝘪𝘳𝘢! 𝘕𝘢𝘨𝘰𝘥𝘦 𝘥𝘢 𝘴𝘩𝘢𝘳𝘩𝘪𝘯𝘬𝘪 𝘯𝘢𝘨𝘰𝘥𝘦 𝘴𝘰𝘴𝘢𝘪 𝘚𝘪𝘴𝘵𝘦𝘳 𝘉𝘪𝘭𝘬𝘪𝘴𝘶 𝘵𝘢 𝘨𝘳𝘰𝘶𝘳 𝘥𝘪𝘯 𝘒𝘸𝘢𝘪 𝘢 𝘤𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘒'𝘢𝘺𝘢 𝘯𝘢𝘨𝘰𝘥𝘦.....♥️

𖣔︎𖣔︎𖣔︎𖣔︎𖣔︎𖣔︎
       𝘑𝘪𝘯𝘫𝘪𝘯𝘢  𝘢 𝘨𝘢𝘳𝘦 𝘬𝘪 𝘔𝘦𝘦𝘳𝘢𝘩! 𝘕𝘢𝘨𝘰𝘥𝘦 𝘬𝘸𝘢𝘳𝘢𝘪 𝘥𝘢 𝘨𝘢𝘴𝘬𝘦! 𝘉𝘢𝘯 𝘴𝘢𝘯 𝘮𝘦 𝘻𝘢𝘯𝘤𝘦 𝘣𝘢, 𝘢 𝘥𝘰𝘨𝘰𝘯 𝘤𝘰𝘮𝘮𝘦𝘯𝘵𝘴 𝘥𝘪𝘯 𝘯𝘢𝘯 𝘣𝘢 𝘴𝘢𝘪 𝘨𝘰𝘥𝘪𝘺𝘢!😘🤩


2️⃣9️⃣

Ba shi da wata amsa da zai kare kan shi! Tunda shima hasashen yake kaman ya tab'a rayuwa da wata amma ba wai ya tabbatar bane.
     *_Eh mana ka tab'a rayuwa da wata! Kayi soyayya da wata! Kun raya da dararraki masu darajar kun shimfida soyayya mai ma'ana_*

Dafe goshinsa yayi cikin rashin nutsuwa. Yana sauke wata irin ajiyar zuciya idan bai manta ba.
Akwai wasu kalmomin da yake.
Rutsa idanun yayi dan kan shi ya fara sara mishi a hankali kalmomi.
*_Amfanin rai a rayu! Amfanin hutu aji dad'i! Amfanin murmushinki  jin daɗin raina!  zan  iya ba da rayuwata akanki! Hakazalika zan iya raba wani da tasa, akan farin cikin soyayyarki, akan nutsuwar da take tarayya da ganinki! A gare Ni kece ma'anar sa'ada! Ga zuciyata kece ma'anar Salama_*

    Kafin yayi wani yunkuri ya fadi rike da kan shi, da yake barazanar fashewa. Idanun shi sun yi jajjur kamar gauta, ya manta wacce yayiwa wannan kalaman sam ya manta da wacece! Amma Tabbas zuciyarshi bata manta kalmar da suka yi musaya ba daga bakunan su.
        Kwanciyarshi yayi a kasa yana jin wani irin zafi a zuciyar shi.
        .....
Tun da tafita zuwa d'akinta. Take kuka me cin rai. Me yasa?! Bai manta da Fannah ba?! Ko dama labarin da ake badawa na tushen su Fannah gaskiya ce? Suna da alaka da mayun gado tunda Asalinsu ba yan wannan yankin bane zuwa suka yi daga wani guri na daban! Indai haka ne tsugune bata kare mata ba. Dan a yanzun take buƙatar mijinta! Kuma yana gudun ta!

      Hannunta biyu ta daura akanta. Tasan tana zuwa gurin Innah ba zata saurareta ba. Tunda  ta cika mata burinta, abu daya ta gaza cikawa Innah nata burin shine haihuwar D'a namiji wanda zai Gaji Kazeem!

             ---
Bayan kwana biyu...

    Duk saurin da nake na yau kar na makara yaci tura, dan na shiga na same su zaune da Umma tana kallon shi, cikin tausayawa. Sosai kamanin su ya fito sak, dan dai ita ta manyanta ne! Shi kuma matashi.

       Ina shiga tana mik'ewa ta kalle ni, sannan tayi murmushi tare da dafa kafad'ana tace..
"Kiyi hakuri"
Murmushi nayi mata tare da gyad'a mata kai. Fita tayi na ajiye tiran a gaban shi. Na kurawa kyakyawar fuskar shi ido, wanda yake kara jefani cikin wata alkarya na daban akan son shi.

"Zaki daina kallona kiyi abinda ya kawo ki ko Ya-ya! A haka ake kula da mara lafiya? Baki da wani aiki sai na kisaka ni a gaba kina kallona dan bani ganinki sai aka ce miki bana fahimtar kome, idan bazaki yi aikinki ba zaki iya haɗa kayanki."

        Shiru nayi tare da zuba mishi kayan shayi a kofin da nazo dashi. Dake jikina na rawa ban san na zuba mishi siga da yawa ba, ban juya ba na mika mishi kofin, amsa yayi yana jan tsaki.
    Sannan na dauki wani karamin ture na zuba mishi farfesun bindin Saniyar da aka yi mishi.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora