https://my.w.tt/v3NAY1mQ49
MAGAJIN IZZAH!!!
{CIGABA KWARKWARAH}
*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*
Mallakin
Mai_DambuSadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️
Godiya sosai Maman Abba Allah yabar zumunci!🌹😍
Last free page...*_Assalaikumun! Barkan ku! Ga masu bibiyar book dina Ina me baku hakuri! Idan baki karanta Kwarkwarah ba! Karki damu kanki sai kin karanta Magajin Izzah! Domin cike yake da murdaddun alamura! Karki damu kanki akan sai kin saya. Ban san me zan ce muku ba amma ba lallai ki fahimci Yaren ba! Tafiyar daban yake da sauran_*
UKU..
Haka Baabi Yasaka Ummi a gaba da fada har karshe ya bar mata d'akin, tana kuka da dana sanin, abinda ta aikata, a cikin daren ta haɗa kayanta kala daya.Da asuba ta barni a hannun amintacciyar baiwarta, sannan suka nufi Daura.
Sun isa da wuri, dan haka sun sami ganin Sarki Jaamal. Bayan sun gaisa Sarki Jaamal yace musu.
"Amma kun fito wani guri ne? Dan naga kamar daga tafiya kuke?"Sunkuyar da kai Baabi yayi sannan yace.
"Mun zo baka hakuri ne! Akan b'atar Jay! Shine muka zo domin mai d'akinka tasan kome!"
.gyara zama yayi sannan yace.
"Dan Rahil tayiwa Jay fada ya fita, shine zaku zo bani hakuri!Rahil! Kanwar Jannart ce, kuma uwa ce mishi, koda me tayi bazan tsawatar mata ba, sabida tafi ni kaunar shi, kai jinka da Jannart tana raye zata yarda na dibo jiki kazo bata hakuri ne bata borance muku ba, wallahi ban tab'a jin kome akan b'atar shi ba.
Sai dai ina kyautata zaton cewa! Allah yayi hikimar haka ne dan wasu dalilai, da yana tare damu, bazai iya rayuwa babu kalubale na, dan haka babu komai."
Shiru duk suka yi sannan Aaryan yake gaya mishi, ai ga halin da nake ciki, shiru Sarki Jaamal yayi sannan yace.
"Karku canfeta, ku dauka jarabta ce! Domin yin haka dai dai yake da wasa da rayuwarta. Don Allah karki bari wani ya camfeta"Wannan abun da ta gaya musu, yayi matukar tasiri a zuciyar su, har suka dawo gida, sun sanya dokar kar wani ya kuma cewa akwai wani abu a tare dani.
----
A hankali rayuwa take Gara mana, har na kusan gama jami'a, a lokacin na hadu da wani soja, muka makalewa juna, a waya dan a lokacin Waya ta shiga hannun kowa, idan muna wayar nan kamar zamu cinye juna, tun ina b'oyewa har na hakura kowa ya sani.Aikuwa Adda kishiyar kakata, ta sani a gaba da Tsokana. Sai na gaya mata.
"Ke yar doguwa waye ne kuke magana dashi a wancan manta sabo.""Addah ki fita idanuna na rufe ina ruwanki da darling dina, jeki gurin dattin ki, kuyi ta lallaba juna"
Maka min mahuhuci, Innono tayi kamata, na tura mata baki cikin jin zafi nace mata."Wallahi koda Baabi ya sayo miki maganin zafi ya bani, bazan kawo miki ba tunda kika buge ni!"
Ina tura mata baki.
"Yar kwaila kawai, dube ki don Allah waye zai yi asarar kudin shi ya auri mace ba kirji.""Innono! Wallahi ki daina wannan maganar, zaki sanya ni dai na shigowa wallahi, ai haka Allah yayi ni"
"Karki kuma saka mana mijin mu" sake baki nayi tare da kallonta sannan nace.
"Yanzun don Allah sabida wancan takwarkwashen mijin ku,.kike min wannan wulakancin, na zata sabida kawai na tsokani yar uwanki! Toh wallahi sai na kuma!"Make ni ta kuma, na tura baki na karar wayata ne ya katse ni, na dauka tare da sakawa a kunne na.
Gyara kwanciya nayi, sannan na lumshe idanuna, tare da bude shi nace.
"Barka hasken rayuwata! Muhid"
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...