9️⃣3️⃣

1.6K 355 27
                                    


KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

_Ingantaccen Zumar goran Tula! Maganin rage kiba! Maganin kara kiba! Maganin gyaran Boons! Karki ji kome tuntube mu ta wannan Number +2348030861857! Sayan  na gari mai kudi gida_

9️⃣3️⃣

     "Tambaya ta kake?"
Na bashi amsa, kai tsaye.

"Rashin kunya zaki min?!"
"Ai haba? Toh zaginka nayi ko.."
Buge min baƙi yayi, kura mishi ido nayi, kwalla ne suka cika min ido.

     Na mike zan bar dakin ya sha gabana yayi cikin b'acin rai.
"Ina magana zaki!"
"Dakata min!  Da alamu kai mutuwar Jannart bai zame maka izina ba, toh ni ya zame min, Kawu don Allah ka rabu dani kaje can kayi ta fama da rayuwarka!"

      Wuce shi nayi, zan fita kawai ji timmm! A tsorace na juya, ban san lokacin da na tsilla ihu ba, tare da dawowa kan shi ina jijjiga shi, ihuna Mamah tayi itama ta fito, a tsora ce ta fita tare da kiran Aswad, aka fita dashi.

         Tashin hankali da muka gani yau ba iyaka,  ruwa aka ya-yafa  mishi Dakyar ya bude idanun shi, aka jingine shi.

      A sanyayye yake sauke numfashi, tare da kallon Aswad da Mamah yace.
"Bani da lafiya!! Tun bayan rasuwar ta, na rasa lafiya ta. Har yau ina fama da rashin lafiya, Aswad mu wuce masauki."

    "A'ah akwai dakunan saukar baki kuje kai da Aswad dinka ku kwana, Gobe Insha Allah sai ku wuce ko!"

  Tana fadar haka tayi juyawar ta zuwa d'akin ta, kamar ya fasa ihu, dan a wannan lokacin matar shi yake bukata, amma tsabar kafiya irina shi ya kasa fahimtar haka.

      Fita suka yi na je na kai musu abinci, ina ajiyewa ya rike hannuna.
"Ko babu kome dole gobe ki bini!"
D'agowa nayi na mishi magana naga idanun shi sunyi wani irin ja, kamar gaushi kwalla ya cika idanun tare da sheki.

          Komawa nayi na zauna kusa dashi, nace.
"Ni mai laifi ce! Wacce yayi gudun hijira daga inda ka ajiye ni, Kawu! Kayi hakuri da abinda nayi wallahi ban yi dan na raba ka da farin cikin ka ba, sai dai nayi haka ne dan faffutikar ganin na same ka.

                       Idan ka duba rayuwata bani da kowa sai Abbana da kakata, ban san soyayyar kowa ba sai ta kakata, Kawu me yasa lokacin da na shiga rayuwarka baka dakatar dani ba? Me yasa ka cigaba da koya min yadda zan sonka?

        Na bika ba sau daya ba, ba sau biyu ba, na tambaye ka wacece abincin ruhinka kayi min shiru! Taya na rasa soyayyar kowa sai na ka da na samu zan yarda Kawata Aminiyata ta rabani da kai? Kawu kai ne silar raba dangantakar mu! Janny ta Rubuta min sako ka bani! Amma ka yaga kak'i bani! Me yasa? Me ya hanaka bani sakon ta? Sai dai Sahibar tawa! Da ƙwaƙwalwa take lissafi! Ba da zuciyarta ba! Ta bar wani sakon a d'akinta!

Ka ganshi har da kwanan wata da lokacin da ta rubuta, washi garin bud'ar kai! Wannan shine bayanin irin soyayyar da tayi maka, ta kuma gaya min cewa nayi hakuri tana sonka! Sai dai lokaci ya kure muku!

         Kana raye! Amma zuciyarka ya mugayen mutane ce! Zuciyarka bata baka shawara ta gari! Amma ba damuwa duk abinda Mamah tace a kaina dai-dai ce, kuma bazan tab'a barin son kaina ya rinjayi abinda zata min ba. Allah ya baka lafiya."

...ina gama gaya mishi magana na bar dakin zuwa nawa dakin, na samu Jay ya tashi, rarrashin sa nayi, sannan na shiga kimtsa kaina sannan na Kwanta na jima ina nazarin abinda na aikatawa Jannart!

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now