5️⃣1️⃣

2.6K 472 61
                                    

https://youtu.be/BF0xPPv4v-M

    _BAHWA HAUSA NOVEL sunan Channel din_
Subscreb, like ,share and also comment , subscribe is free..

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

https://my.w.tt/KhRU5Ga647
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLA

_For You Mariamah Mai-shanu🌷💐🌹_
5️⃣1️⃣
         "Koda yake, bana son damuwa kuma ban cika son ana min shigar sauri. Dukkan mun nan y'ay'an sarakuna ne, ke kuma Ummar Mijinmu ne, ina ganin babu wani burgewa muzo mu zauna a gabanki kamar wasu bayi.

       Na taso gidan da ake da yawan ya'ya banga ana irin wannan tsarin ba du...."

"Kee!"
Ya daka mata tsawa, kamar zai fasa mata dodon kunne, d'aga mishi hannu Fulani tayi, kallon shi tayi sannan tace.
"Duk da banbancin al'adun masarautar ƙasar Hausa, amma akwai tsage gaskiya daga inda aka ƙalla zaka fahimci, tsarin kenan."

   "A'a Fulani! Ba tsarin bane, Dai-daiton ra'ayine, dukkan mu nan baza mu tab'a zama sarki ba ba, sai dai mu kasance matan sarki, amma yana da kyau abawa kowacce mace damar kimanta kanta.

     Ke uwa ce! Me daraja baki yi laifi ba dan kin tara mu, amma yana da kyau a sanar mana, tun da jimawa, ba wai sai lokacin ya kore ba.

             Kayi hakuri kawu, iya Gaskiya ce da aka rene ni dashi."

Tana kaiwa nan ta koma gefe ta zauna, shiru dakin cin abincin yayi. Kafin aka fara shigowa da abincin ana zuba musu.

   Koda aka zo gabanta rike hannun baiwar tayi sannan tace.
"Karki damu, ba sai kin zuba min ba, tunda kin zubawa Fulani, zan ci nata."

   Da wani irin kallo Fulani Hasiyah ta bita, wannan kallon kawai sai da ya sanya kowa ya kalli Fulani, murmushin yake tayi sannan tacewa Sarah.

" Ya haka? ga abincin ku zaki ce nawa zaki ci?!"

Wani Munafikin murmushi Sarah tayi sannan ta kalli, Fulani wacce itama take cikin shakku tace.
"Ummana! Ai kinsan ban tashi da uwa ba, dan haka idan zanci abinci da wani nake ci. Kuma idan ban ci da wani ba, akwai matsala.".

   Duk yadda Fulani taso kaucewa shaidancin, hakan aka zuba musu abincin suka ci tare.

     A ran Fulani Hasiyah kuwa, niman hanyar da zata ji da Sarah take, yadda zata mata kisan munmuke, suna gama cin abincin Fulani ta kalle ta sa murmushi akan fusakarta,

         "Ke yarinya ce! Da alamun an gaya miki kadan daga cikin halayyata da mutane basu sani ba, shi yasa kike abubuwa son ranki."

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant