ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹_Gaisuwa da fatan Alkhairi gare ku masoya 🤩😍_
6️⃣8️⃣
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,"
Abinda Jaamal ya iya fada kenan, cikin tashin hankali aka shiga niman na. Babu Ni babu alamata.Take hankularbsu ya kuma rabuwa Ina Jannart? Wannan al'amarin da. Mai yayi kamar.
---
Tun ina ihu har na daina, a hankali idanuna suka fara rufewae, sabida karfin iskar dake dukar fuskana, ji nayi mun sauka a kasa.
"Ranki shi dad'e, bude ido idanunki."A hankali na bude cike da tsoron abinda zan gani, sai ganin wasu irin mutane nayi bakake Gajajjeru masu Dai-daiton kai. Kansa baya nayi cikin tsoro.
"Ranki shi dad'e, ai nan masarautar ki ce." Inji wani dan kankanin mutum mai yawan farin gashi, rike yake da wata sandan da takere shi tsayi.
"Ku suwaye?!"
Murmushi wani tsoho yayi cikin nutsuwa yace.
"Mu kabilar nok ce, wanda kuka kasance jinsin wadanin, sannan muna boye ne, sabida zalinci da aka muku, keda Mahaifinki Sarkin bokaye.Kasancewar shi din shugaban mu ne shi, amma mu ba jinsin D'an Adam bane, mu aljanu ne.
Dan haka bazamu cutar dake ba, mun kawo ki nan ne domin ki tuna baya da abinda ya faru, sannan ki samawa wancan na rufen adalci.
Bazai tab'a fadar gaskiya ba, kuma bazai tab'a kisan kai ba, akwai abinda mu dake bamu sani ba.
Shi din yaron kirki ne, Hasss tawo ga uwargijiyarka nan."
Wani hangarman doki ne ya tawo da gudu, tare da mik'ewa sama da kafaffunshi, ja baya nai. Zuba min ido suka yi sannan suka juya baya zuwa kogon da aka sanya mishi wani irin kofa tare da wata irin kwad'o.
Buda min hanya suka yi, gani nake kamar mun tab'a bin hanyar, da wani. Ina bin duwatsun da aka musu, ado kamar matakala, har muka na isa bakin kofar, bude kanshi kofar yayi. A hankali na cusa kina , abinda kunne na yaji min ya sani mamaki domin murya tace sak da ta Kawu."Fairo! Zai zo tashi mu gudu!"
Na fada a raunane.
"A'a! Zuryana, jeki kawai ki barni a nan sun kama kurwata bazan iya kome ba, tunda yana hannun su.""Ka tashi zaka iya tashi Fairo!"
"Bazan iya ba, kije maza ki bar nan karsu cin miki, dab suke da isowa.""Bazan iya tafiya ba, sai dai mu tafi tare. Ai munyi alkawarin zamu rayu tare kuma zamu mutum tare, me yasa kake ganin zaka iya raba mana tsakani, tashi zaka iya."
Dakyar ya mike, tare da rike ni har zamu fita su kuma sun iso.
Hannu mu rike da juna, muka zuba mishi ido, cikin kuka nace.
"Zulum! Ka barmu haka, kayi rayuwarka ka barmu a duniyar mu, karka lalata mana zaman mu!"
أنت تقرأ
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
أدب تاريخيA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...