7️⃣4️⃣

2.3K 465 65
                                    

https://my.w.tt/ehkdbYWni9

KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

*_Barka da ranar HAUSA! Hmm Damina bana ba irinta Bara bace, kwad'o ya faɗa ruwan zafi! Masoyin kwad'o bana kifi bane! Tsohon doki yafi sabon takalmin! Akwayi tayi wayo, da yankakken kunnen! Ba gwada ba, dadin Sarki a jaki! Mhm inji matar barawo! Mununnan kare sai cizo ba haushi!🤭😜🤣😲🙄🤔 Me hankali ke gane dingishin kwad'o_*

7️⃣4️⃣
1377...
Yau ta kasance Laraba, dan haka ga mabiya gumkin tsella, yau suke Shagali cire amfanin gona, murna sosai ake inda mutane suke kawowa gumkin tsella, ana zuba mishi.

Bayan an gama, sai sarkin Bokaye ya shiga dakin ibada ya zauna. Aljani duduma ya bayyana a gaban shi yace.
"Wannan shekarar tazo da zubda jini, sannan kuma sadaukarwa zata iya hawa kan ko wani abu.

Bayan nan tsinuwar mu ya tabbata akan Zulum da zuriyar mato gargara, da duk wanda yake raba kafa ga abin bauta.

Dan haka ka kiyayye mutanen da suke kusa da kai! Domin kuwa a cikin su kwai Bara gurbi, sannan a cikin bazara za ayi bikin Yarima Fairo da Gimbiya Zuryana.

Wannan itace sakona a gareka, da fatan zaka rike ka bawa Zirya hakurin rashin da zata yi na abokinta, sannan ta kiyayye fita daga gida..

Su kuma mutanen, ka gaya musu abin bauta ya amshi sadaukarwa su, dan haka suje su aikawa matayen su, zuri"a zata cika duniya.

Sannan kowa yake da bukata yaji a ranshi an biya mishi, da wannan nake maka sallama dan kumdum uba."

Kaskantar da kanshi yayi, sannan yace.
"Godiya nake dan malafar Ubanka"

Da haka Aljani dumduma yabar dakin bautare, yana fita Sarkin bokaye yana fita.

Yayi shela, ga abinda abin bauta ya faɗa, sannan ya isa fadar sarki Mato, ya gabatar da abinda tsella ya faɗa.

Nan hankalin mutane ya tashi, tare da mik'ewa suna barin fada ya kuma kallon Sarki mato yace min shi.

"Tabbas! Zulum yana fusata abin bauta! Gashi har ta kai da an tsine mishi ba shi kad'ai ba hatta ga wasu nashi, na roke ka dakatar da shi.

Yin haka tankar tallata kanmu ne ga sauran larduka, nunawa ne abin bautar mu ya kasa, me yake nima a gurin tsunbubura, bayan ga na mu Ubangijin ya bamu.

Ka duba Alamarin mai martaba, wannan tamkar tozarta abin bautar ne, nagode Abin bauta ya albarkaci rayuwarka."

Sannan ya bar fadar,
Zulum! Shahararren mayakine wanda ba a taba irin shi ba a cikin masarautar daura da nahiyar baki daya.

Shi kadan shi ana mishi kirari da sa maza gudu, Zulum karfafa ne, dogo mai matsakaici kiba, sannan yana da halittar zaratan maza, idan yana tafiya sai kaji sautin takun shi.

Idan kuma yayi maganar to tankar an buga katon gangane,

Bayi da abinda yake so sama da mulki, sai kuma jaraban son mata, idan yaga mace, gabaki daya nutsuwar shi gudu take, sai ya bangajeta ya haɗa shimfid'a da ita yake jin nutsuwa,

Sai dai kyakyawan ne, mai kuma kan yanayi, amma ya kasance kamar kan dan maciji. Shi yasa yake yawan rufe fuskar shi da kyale, dan halittar kwayar idanun shi tankar an sanya mishi kwali.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora