ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹AminuIsah1 Nagode bani sarautar Sarauniyar Marubuta! Fatan Alkhairi me tarin Yawa 🤩😍😘
2️⃣8️⃣
"Kul ka cutar musu da Y'a daga zuwa hutu, sai ka zalunce ta!"
Sunkuye da kai tayi, cikin jin haushi Ummi tace.
"Magajiya! Sharri tayi Mishi da!"
Caraf Labiba ta karb'i zance da cewa.
"Meye ribata da zan Mishi sharri? Ni kawai a mai dani gidan mu.""Ya isa muje d'akina!" Magajiya tace mata, ba musu tabi bayan ta.
Tunda ta shiga dakin take kuka.
"Kiyi hakuri!"
Shine abinda Magajiya tace mata, sannan ta barta anan zaune........
Kafin kace me abinka da gidan sarautar har maganar ta yadu, kuma aka rasa a bakin waye maganar take lilo, domin wannan itace dabi'ar masarautar, koda tusa aka yi matukar wanda yayi ta yana da wata nasaba da mulkin gidan toh ba makawa sai kaji tana yawo......
Washi gari da safe.
Haka na rako Mama inda Motar da zai kaita Kaduna yake na tsaya, ina share kwalla."Kin san yau zaki fara kula da lafiyar shi! Kuma kin fi kowa sanin halin shi! Don Allah ban da abinda zai janyo hankalin mutane kanki. Kin dai ji abinda yake faruwa a gidan nan don Allah ki kula ban da shige da fice, kuma ki zauna a Shashin Umma Fulani. Ban da yawo dan kar matsalarki ya tashi a rasa wanda kula da wani."
Gyad'a mata kai nayi cikin gamsuwa da bayaninta. Sannan ta cigaba da cewa.
"Ciwon idanun shi bazai wuce wata biyu zuwa uku ba, kafadar shi da haƙarƙarin shi ce zata iya daukar lokaci! Nan dai da wata shida, idan kuma Allah ya taimaka bazai jima ba."
Gyad'a mata kai nayi dan ban san me zance mata ba. Sallama muka yi sannan motar ta bar Masarautar.A hankali nake takawa, ina tunanin yadda zaman mu zai ƙarƙe, dan yadda na fahimci Kawun nawa ya koma dan rigima ne.
"Damar kece ta sauya kaddarar ki da ta wasu! Lokacin ki ne na nunawa Ahalin Zulum kin dawo! Ranki shi dad'e! Karni uku zuwa hud'u kika dawo! A shirye muke mu bada rayuwar mu dan sabunta masarautar da aka Zalince ki."Kallon ta nayi ina nunata da D'an yatsa bakina na rawa, mik'a min wata sarkar wuri tayi. Wanda yake sarke da wasu karafunan azurfa.
"Wai ke meye matsalarki da Rayuwa?! Meye kike bukata dani?! Meye na tsare miki ne?! Me yasa kike kambama al'amarin canfe, wanda babu shi cikin addinin Musulunci."Cizon lebenta tayi sannan ta gyara tsayuwar tace.
"Wanda za a kashe don an karairaya shi ba kome.! Kafin Zuwan ki nasan wacece ke! Yaushe zaki zo, shine ban sani ba. Amma koda zaki kashe ni abinda na sani shine kina da nasaba da jinin wannan masarautar!Ƙarfe duka ƙarfe ne, amma a cikin ƙarafa akwai zinari da azurfa."Yadda take kallona ya kashe min jiki, k'in karb'an abin wuyar nayi na juya abuna ina cewa.
"Ban da ina jin kunyar ki Tabbas da na baki mamaki mata duk kin hana Ni sakat""Ranki shi dad'e ki amshi wannan sarkar wata rana zai miki amfani."
Juyawa nayi a fusace kamar zan rufeta da duka, sai zuɓewa tayi akan gwiwarta. Abinda Ya kuma kashe min jiki kenan.
"Wai me kike bukata dani?!""Ki amshi wannan sarkan. Shi d'aya ya rage zan baki domin tuna wasu shudadd'en alamari dake tattare dake. Ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare"
Saka hannu nayi na amshi abin, wanda yayi dai dai. Da isowar Aswad cikin sauri na boye abin ina kallon yadda ya kafa min ido. Murmushi nayi sannan nace.
"Ina kwana?!"
![](https://img.wattpad.com/cover/219263309-288-k330621.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Ficção HistóricaA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...