ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT😊_Har ila yau Ruwa tana maganin daud'a MJ me dogon zamani 😊 toh ashe daren jiya matar so da Ina da buri ne suka farfaɗo da kimar su A'a MJ ma fa yayi an dama da MJ 🌹🍃 Ya Allah kaine kasan sirrin zukatar bayinka Ubangiji na gode maka da👏🏼_
1️⃣1️⃣
A razane na juya ganin yadda ya cikine wuyar Samim, yana muzurai, ran shi ya kai kololowar ɓaci, dan yaki sake wuyar Samim, Mama sai magana suke mishi ita da Aswad amma yaki sake shi sai da naje na rike hannunsa na kalle shi, cikin rauni murya nace.
"Ga baki daya jama'a kallon ka suke! Indai nice bazan kuma ba kayi hakuri."Ture shi yayi sannan ya fincikoni muka nufi Office d'in shugaban makarantar, ya zauna a kujeran Ni kuma ina tsaye sai huci yake, mik'ewa shugaban makarantar yayi ya bashi ruwan kwalba ya amsa sai da ya shanye! Sannan ya sauke a jiyar zuciya yafi minti biyar yana sauke numfashi kafin ya buɗe baki yace.
"Akwai wani yaro"Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa.
"Koda zai zo gurinta karku barshi ya ganta sunan shi Samim Mai Nasara"
Mikawa shugaban makarantar hannu yayi suka yi musabaha, sannan ya tashi yazo inda nake kai na a sunkuye yace.
"Kina kuka dan na mare shi ko? Toh idan ya kuma rike rigarki b'atar da shi zan saka a min sai Kiyi kuka da tushe, sakarya tunda nike ko tsawa ban tab'a yiwa kowa ba, amma kin sani abin kunya a gaban mutane! Duk kin sani darajata da kimata ya zube a kasa. Na kuma ganinki da shi sai na gotar mishi da haɓa."Har muka fito nuna min hanyar ɗakin mu yayi sannan yaje ya samu Mama sun tafi, sai Aswad ne yake jiran shi. Yana zuwa ya samu duk abinda aka kawo min har da na Samim duka ya kaiwa motar tare da jan tsuka yace.
"Har da Shirgin wancan mahaukacin aka kai mata,"Kallon renin hankali Aswad yayi mishi sannan ya mike tare da shigewa mota.
Shima shiga yayi yana cika yana batsewa, har suka fita daga makarantar sai da suka nufi har Zaria, ya kalli Aswad da ya tsuke fuska kamar bashi ba, sai jikin shi yayi mugun sanyi ya sauke numfashi sannan yace.
"Abokina! Ban san abin yaja ni aikata hakan ba, ba zan kuma ba""Toh naji Romeo! Ka bani hakuri kawai sai na fada maka abinda yasa kake aikata haka."
"Wallahi bazan baka hakuri ba, dan mutum uku nake bawa hakuri! Umma Fulani! Abbana! Sai Umma Rumana! Ita kam ma nafi bata hakuri idan naga tana cikin kunci! Umma Fulani kuwa ita bani da wata dogon damuwa da ita, haka ba a haifi wanda zan bawa hakuri ba walo mace walo namiji har da kai kenan!"
(Hakikanin soyayyar gaskiya kenan!)
Murmushin takaici Aswad yayi sannan yace.
"Na jinjina maka Yarima Jamal! Allah ya huci zuciyarka ba sai ka bani hakuri ba rike kayanka sai dai ni zan baka hakuri tuba nake ranka shi dad'e"Kauda kai yayi yana kallon tagar motar. Bai zaton abinda zai fito bakin Aswad ba sai ji yayi yace.
"Kana son Jannart Jamal!"A sukwane ya juya yana kallon Aswad yana girgiza mishi kai.
"Da gaske kana sonta?! Son ne yaja kake jin haushin Samim"Dariya Jamal ya sake sosai har yana tafa hannu yace.
"Ka zare! Ni" ya nuna kan shi sannan ya cigaba da cewa.
"Kayi kuskure! Ban tab'a jin Sonta ba! Kuma bana jin kaunarta taimakon ta nayi sai ya zama soyayya!"
BINABASA MO ANG
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...