ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO....__Yi sha'aninki Candy🤣 bana ce kar a kirani ba sai da kika dage kika ce MAI_DAMBU toh Alqur'an kinyi na kud'inki nagode 🤝 sosai Allah Ya bar zumunci_
#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT😊🔟
Abinci Jamalah ta fara bawa me Martaba, yana ci a hankali idanun shi na kanta tana share kwalla,koda ta kuma dib'ar abincin juyar da kai yayi yaki amsa yana kallon ta
Hawaye ne wani na bin wani, shafa kanta yayi, yana mata kallon tambaya,Dakyar ta had'iye kukan tace.
"Abba! Kawu Shamaki shine."
Kura mata ido yayi sosai, yana son jin karin bayani.
"Abba! Wai zai had'a Ni da Yaron shi Abdul Kareem"Murmushi ya kuma yi sannan ya kalli wasu takardun Jamal.
"Abba! Insha Allah yau zai dawo!"
Shafa kanta yayi sannan ya jinjina kan shi, diban Abincin tayi zata ba shi ya girgiza mata kai alamun ya isa.Ɗaukar tiren tayi ta fita daga Shashin, ajiyer zuciya ya sauke a hankali yace.
"Jamal! Ka dawo haka"Tura kekenshi yayi yar inda tarkadun shi yake, ya dauki kundin tarihin shi ya shiga rubutu a cikin sa.
++++
Da yamma likis suka iso garin Daura, kallon shi Aswad yayi sannan yace.
"Ka karbo min takardan ziyarar Yarinyar can?!"
Wani irin kallon banza Aswad yayi mishi sannan ya karya kan motar zuwa cikin gidan.Shiru yayi kamar bazai magana ba, ya kuma sake tambayar shi a karo na biyu,
"Wallahi Jamal ka fita idona na rufe! Ban karb'a ba kanin Ubana Allah karka takura Ni"D'aga kafad'arshi yayi kamar bai damu ba, har suka shiga gidan.
Fita Aswad yayi daga motar Jamal ya rike hannunsa, zuba mishi ido yayi bai ce kome ba, kuma ya sani ina zasu kwana a haka bazai magana ba, saka hannu yayi daga aljuhun rigarshi ya ciro yan kanunun takardun ya ajiye mishi sannan yasa kai ya fita.
Ajiyer zuciya ya sauke sannan shima ya fita daga motar.
A gajiya yake tafiya duk inda ya ratsa sai an zub'e an gashe shi, bai tsaya ko ina ba sai Shashin mahaifin shi, nan ya fara zuwa.
Yana shiga ya zube a gwiwar shi sannan ya daura kan shi akan cinyar Abban shi, yace.
"Abbana! Afuwa""Gashi ina son na baka sako zuwa ga Waziri ya tura a dawo da Jamalah nan arewa, sannan akwai muhimmin magana akanta da D'an Sarkin Kano dan tun wani zuwan mu hawar daba a Kaduna ya nimawa dan shi Abu Turab wato Aliyu, d'azun da rana tazo tana kuka wai Kawunku zai had'ata da Abdulkareem, ban san me yasa Shamaki yake haka ba."
Shiru yayi kamar ba zai magana ba, d'ago kan shi yayi sannan yace.
"Me kake bukata ayi!"
Tura kekenshi yayi ya juyawa Jamal baya, sannan yace.
"A bar ganin allura kankanuwa,karfe ce."
Ya bar ganin Shamaki haka hatsabibi ne,Murmushi Jamal yayi Sannan yace..
"Abbana! Sai an gwada akan san na kwarai"
"A'a! Jamal ba a daukar kare ranar farauta!""Idan takama hakan ce masalaha dole a dauke shi ',ai maganin biri karen maguzawa! Matuƙar ina numfashi! Kuma jinin Habibullah da Aminullah suke yawo a jikinka! Jininka yake yawo a jikina! Wallahi babu wanda ya isa taka min ahalina! Kai dai zuba ido kaga yadda zamu kwashe dashi."

BINABASA MO ANG
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...