https://my.w.tt/IN6bSSsjq9
KWARKWARAH
{ITAMA MATAR SARKI CE}
HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.
Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹*Ina matan Alfarmar! Ina matan shiga gaban mota! Ina matan da basu kaunar a rena su a gidan biki, Cancadi rangadi! Hmmm kaji wani kirari tangaɗin maɗiɗi me gida mi kace! Wai tabizaro wannan kirarin na meye ne! Hmmm! Shin baki da labarin LA Fashion trend ne! Wayyo ni 😱 a ina yake? Ji min Dambuje buje! Toh ai suna kawo hadaddun kayan zamani! Irinsu Lace! Material! Ke har da manyan gyalulluka irinta manyan mata da na Yan mata adon gari! Wayyo Allah na! Tabizaro 🤭 zan fasa asusuna! Haba ina ai kayana sun tsinke a gindin kaba! Jama'a ga dama tasu ga masu bukatar kayan irin Laces! Materials! Da Veils zaku tuntube wannan Number, Domin samun ingantaccen kaya masu zube da zamani!+234 907 144 2935*
Sai munji ku! Sayan na gari mai da kudi aljuhu dan baza ce gida ba🌹😍🤝
7️⃣9️⃣
Ji tayi kamar bazata iya tsayawa da kafarta ba, dakyar ta koma dakin da jannat karama take.Tana shiga ta rufe kofar d'akin tare da sake wani irin kuka, me mugun ciwo.
Me yasa sai ita Jannart zatawa haka! Ta rabata da mijinta, ta hanata samun nutsuwa da gidan aurenta. Kuka take tare da tuno wasu abinda yayi ta shiga tsakanin su, haka tayi ta kuka.
A ganinta basu damu da ita ba, shi yasa suka banzar da ita bayan Jannart taci amanar ta, tayi kuka har kanta ya fara sarawa.
Dakyar ta tashi zuwa ban daki ta wanke fuskarta, tare da zama a jikin yarta. Sai yanzun take da nasanin, kwashe sirrinta tana gayawa Jannart, kome tayi zata gayawa Jannart.
Kai hatta idan ta sami ciki kafin Jaamal ya sani, Jannart ta riga shi sani. Wani lokacin ma a bakin Jannart yake jin.
Ashe kashe kanta take bata sani ba, ashe lalata rayuwarta take bata sani ba, ga baki daya ta shiga rudani da mugun tashin hankali, dan haka taci alwashin sai ta hana Jannart farin ciki.
...
"Raihanah!"
"Dakata Jaamal kaja bakinka ka min shiru! Kuma kabar dakin nan ko kuma wallahi na dauki Jannart na mai data gida. Na rasa me zan gaya maka naji sauƙin abinda kayiwa Jannart!Haba Jaamal, meye yayi zafi haka da kake jin a ranka ka cutar da yarinyar da bata ji ba bata gani ba, toh hankalinka ya kwanta ka sami abincin ruhinka shi kenan! Zaka iya amfani da sonka da take ka cutar da ita, amma har abada bazata tab'a cutar da koda karenka ne.
Yarinya tun bata san ciwon kanta ba, take jigila da soyayyarka amma kayi fatali da..."
Cikin jin haushi tare da gajen hakuri yace.
"Wai ke Raihanah! Meye matsalarki da abinda ya faru damu ne? Ga baki daya shi yasa ba tsani na zauna ina miki bayani.Domin baki baki da fahimtar kome, idanunki rufewa suke kiyita gayawa mutane magana, Wallahi idan kika daukar min Mata sai na miki haukar da sai kinji mamaki na"
Haka kawu ya gama bugawa Raihanah rashin mutunci, aikuwa dake ta fishi zafin rai, wallahi koran shi tayi fata-fata, tare da gayawa malaman jinyar kar su kuma barin shi ya shigo d'akin.
Hakuri sosai Aswad ya bata, tare da nuna mata laifin ba na Jaamal kadai bane, har da shi a cikin alamarin.
Shima bai sha daga cikin faɗar ta ba, domin ta kore shi daga d'akin
Zama tayi cikin damuwa da tausayin Jannart, tana rike da hannun ta. Wanda yayi fari sol.
Dakin dasu Sarah suke, ya isa tana ganin shi, ta faɗa jikin shi tana jin wani irin kuka yazo mata, matseta yayi a kirjin shi yana jin babu dadi.
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...