KYAUTA TA BIYAR

886 95 6
                                    

https://my.w.tt/HhAx5ish69

MAGAJIN IZZAH!!!

{CIGABA KWARKWARAH}

*Ban yarda wani ko wata ta juya min koda Harafi daya ne na Labarin! Ko kuma a samun wani kafar Sadarwa! Yin haka zai sanya wani ya fuskanci b'acin rai!*

Mallakin
Mai_Dambu

Sadaukarwa ta gare ki bazata kare ba! Mab'allin zuciyata! Zahran Addah Ramla☺️

Fatan Alkhairi Fans din KWARKWARAH da MAGAJIN IZZAH ga Pagen ku nan gaisuwar taku ce😍🙈

BIYAR.

Idan nace zan baku labarin yadda garin calgary yake zamu kwana mu wuni ban gama bada labarin yadda garin yake, dan matuƙar haduwa ce, koda muka. Isa gidan wanda yake.

Preston town, anan motar su Kawu Muddam ya tsaya, a hankali ya karasa jikin kofar gidan ya tsaya, sannan muka fito. Ina kallon Unguwa, yayi min kyau, musamman iskar da take kad'awa.

Cikin gida suka mana jagora shi da Umma Fouzan, tunda muka shiga nake kallon yadda tsarin gidan yake, bayan munci abinci muka yi wanka na kwanta kenan Baabi ya turo min yar Karamar yarinyar Umma Fouzan me suna.

Ablah, da sauri na mike na fita gurin shi.
"Baabi na gaji ne! Na kwanta na huta."

Murmushi yayi sannan ya kalli agogon hannun shi yace.

"Zamu shiga jami'ar Alberta ne, mu gama miki kome zuwa nan da jibi na koma gida!"

Gyada kai nayi, sannan nace mishi.
"Baabi ko nazo muje ne?!"

"Idan zaki iya muje mana!"
Murmushi nayi dukda na gaji sosai, amma bana son rabuwa da Baabi na ya sani shiryawa zan fita sai ga Umma tashigo.

"Ba fa inda zaki domin nace su tafi! Ko kunya baki ji ba, ƙatuwar Uwar mata, zaki bishi zokai-zokai toh sai ki kwanta ki huta"

Tura baki nayi idanuna suna kawo ruwa nace.
"Ni wallahi mutum ba yazo ba, a hana rayuwar shi sukuni."

Dariya tayi, abinta dan mun saba fadar mu da ita. Fita tayi yanar ni, nayi kwanciya ta..

---
A cikin kwanaki biyar suka gama min, kome sannan Baabi yayi min nasiha. Tare da ja min kunne kar naga bana gida nace zanyi abinda rai nake so.

Naji nasihar shi, amma bazan iya bari a ci min mutunci na kyale ba, dan haka ranar da na cika sati daya, ya koma nima kuma a ranar zan fara zuwa makarantar. Da wuri na shirya cikin doguwar rigar, tare da nad'e kaina. Da farin mayafin.

Sai takalmina baki shigen kayan jikina. Tare da jakar da nad'ebi abinda zanyi amfani dashi. Na nufi waje inda Kawu Muddam ke jira na, sai danna ansakuwar shi yake.

Koda na isa waje, na kalle shi a hankali. Nace mishi.
"Kayi hakuri!"

Kallon agogon shi yayi, na shiga tare da gyara zaman agogona, ina son agogona domin gadon Mahaifiyata ce, dan agogon ta zinari ce hadi da Lu'lu'u, Baabi yace shi ya sayawa Maaminah, lokacin zuwan su, Madina bayan auren su.

Shi yasa nake son agogon dan yace min, na rike shi da kima. Mun isa makarantar, shi da kanshi ya kai ni har cikin ajin bayan mun biya wani ofishin mun ajiye bayyanan na fara karatu, har kofar aji ya ajiye ni tare da bani wata takarda da zata kaini unguwar da muka fito.

... Bayan tafiyar shi na shiga ajin na zauna, duk da kowa harkan gaban shi yake. Nima na zauna tare da nutsuwa guri guda. Ina kallon yadda suke hidimar gaban su. Dake nima ba ma'abociyar son magana bane, ban kuma kallon kome da suke yi ba.

Shigowar wani bature, wanda zai dauke mu a darasin lissafi. Ya gabatar da kanshi. Sannan ya fara abinda ya kawo shi, yana gamawa ya fita, a hankali naga daliban nata fita, nima daukar jakata nayi na fito.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now