7️⃣7️⃣

2K 453 76
                                    

KWARKWARAH

{ITAMA MATAR SARKI CE}

HAZAKA WRITERS ASSOCIATION.

Baki daya labarin
Sadaukarwa ce ga
ZAHRAN Addah Ramlat 🌹

    _Haka kawai Fannah zata sauya min salon labarina da wani☹️ shirmen t_

7️⃣7️⃣
Sake kuka dokin tayi Fannah ta kauda kanta tare da cewa.
"Ba fa zan yafe miki bane! Kawai ki gama bada hakurin ki na dirka miki rashin mutunci.

        Bawai dan Kinga ina kallon ki kina kada min jelarki, ke gaki me gashi,"

         Bai san iya adadin lokutan da ya bata yana murmushi tare da kallon zallar danyen yaranta dake damun ta ba.

   Tana gamawa ta wanke hannun ta ta juya ta kalle farin dokin tace.
"Dan Mutunci kai ai dole ma nayi ta zuba maka abinci kana ci, dan baka da wulakancin irin na wancan goɗiyar, ki bar harara na, dan ba yarda zanyi ba kina cigaba da cin min fuska, bafa tsoronki nake ji ba.

     Yar bakin ciki kawai, shi yasa ka nime ji min ciwo, mara kirki kawai."

     
          Haka fannah ta gama karawa dawakai rashin mutunci, tare da nunawa goɗiyar cewa sai ta gabza mata rashin mutunci da ita take zancen.

Kamar dai jiya sake fita tayi da gudu, tsabar yarinta, akala zata kai shekaru goma sha uku, yarinya ce karama, sai tsabar shirrita.

        Tana tafiya ya sake labulen tagar shi.
         A hankali ya fahimci zallar shiriritar fannah, babu abinda ya dame ta, zata iya b'ata lokaci akan dabbobi ba tare da taji damuwa ba.

             ---
A daura kuwa..
Zuri'ar Moɗi suka amshi mulki har zuwa lokaci me tsayi.

           Babu wani danganta da yake nasaba shi da wani jinsin sai dai masana tarihi sun tabbatar da dole za'a sami iri biyu da zasu fito a cikin masarauta.
             Sarki Abdullahi wanda shi ya kasance jika ga moɗi, daga nan har zuwa sarki Aminullah, baban Sarki Jalaludeen..
(Ku koma farkon Labarin zaku fahimci haka.)

     Ba a kuma samun wani sarkin da ya kafta rashin mutunci irin na Zulum ba.

     ---
  Kacoka Sarki Kazeem ya tattara hankalin shi akan Fannah, wacce Allah ya daura mata niman tsokana, jan rigima. Shiga abinda babu ruwan ta.

         Uwa Uba, hira da dawakai. Kuma har da shara'a ake musu wanda ya cuci wani a gaya mishi bai da gaskiya, koda kuwa zai Harare ta tare da hura mata hanci.

    Zata gaya mishi gaskiya, wannan yanayin da take yawan shirmen ya haifarwa da Sarki Kazeem, wani irin bakon yanayi, wanda ya gaza fahimtar haka. Sai da Ya gayawa Bana.

       Yadda yake ji, akan Yarinyar da take kula dabobbi, har ya kawo shi dakin shi ya ganta ta taga, shima sai da yayi dariya sannan yake gaya mishi ai sonta yaƙe. Kuma babu yadda zai da ita tunda matan shi hudu ne.

       Murmushi yayi tare da cewa.
"Duk mata hudu babu zabina a cikin su, sai ita taya zan yi wasa da damar da nake da shi, kasan Yadda nake ji akanta. Hmm ko a saɗaka zata zo min, dan haka ka Nima min Baba galadima da Baba Waziri zan aureta."

       "Ka manta da Innah ne?" Bana ya tambaye shi.
 
         " Ina sane da ita."ya bashi amsa a takaice,
   Lokacin da sarki Kazeem ya bayyanawa dangin shi abinda yake bukata, bori aka mishi. Shima kuma ya kafe, dakyar aka amince mishi tare da niman Baban Fannah.
  Karku manta duk wannan abu dake faruwa bai ma san sunan ta ba, balle ya kai da ya kebe da ita.

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Onde histórias criam vida. Descubra agora