7️⃣

3.9K 448 39
                                    

🌹🥀🌷
*K'WARK'WARAH*
                  🌼🏵️🌺
     '''{ITAMA MATAR SARKI CE}'''

         _LOVE TRIANGLE♥️_

Oum Muwaddah
   Mai_Dambu

      _Wannan Shafin sadaukarwa ce ga Daliban HAUSA, tun daga kan Degree har zuwa kan N.C.E musamman masu kishin Hausa da zaurance nagode da kara min ilimi akan Hausa 😊_

   '''Wanda aka haifa 29 ga wannan watan ba ya kara shekaru sai ko wane shekara hudu kenan? Ko ya'''

     *Fatan Alkhairi Hajiya Maryam Jikalukun🤣😂*

       

7️⃣
   "Raihanah!"
   Tsuke fuska tayi tare da kau da kai ta had'e hannunta duk biyu tace..
"Ka mai da ita gurin da zata zauna cikin damuwa, tunda sharad'i na yayi tsauri."

       Lumshe idanunshi yayi cikin damuwa sannan ya mike tare da kallon agogon hannunshi yayi sannan ya mike, ya d'an saci kallon kofar da suka wuce.

   "Toh zamu wuce Zaria"
 
Share shi tayi sannan ta kalli Aswad tace.
"Ko zan kira maka ita ne kuyi sallama."
     Bada Aswad take ba, da Jamal take,
Fita yayi abin shi da ya fahimci da shi take, Aswad yace.
"Maman Aliya zamu tafi, duk yadda ake ciki zamu ji daga gare ki tunda gashi nan mun dawo nan zaria."

   "Hmm! Kace mishi barin kashi a ciki bai maganin yunwa wannan zurfin cikin ya ajiye a gefe idan yace zai min katsalanda zan tattaro mishi kayan shi na watsa a waje yasan halina."

  "Haka ma bazai faru ba."
Aswad yace,

      Sallama yayi mata ya fita,
    
  A cikin mota Aswad ke  gaya masa sakon Raihanah. Kauda kanshi yayi.
    
      -----
Bayan tafiyar su ta saka karamin d'anta ya kirani, nan naje na zauna can gefen ta.
  
     Shiru tayi tana duba takardun gabanta.
"Sunnaki Junnuh ko?!"
   Gyad'a mata kai nayi, murmushi tayi sannan tace..
"Daga yau sunan zai koma Jannart sabida Junnuh ba dad'i, amma idan kina so a bar miki abinki."

      Sake gyad'a kai nayi.
"Me yasa baki magana."
   D'ago kai nayi sannan nace.
"Ina yi."
"Masha Allah! Zaki fara karatun ki idan koyar da yaran yazo akwai me zuwa da magariba yana koyar dasu ɓangare Arabia. Sai me musu na bokon dake ana huta, zan saka a mishi magana yazo yana daukarki kafin a saki a makaranta."

         
   Gyad'a kai nayi, a hankali hawaye ya shiga saukowa daga idanuna.
      Zaro ido tayi cikin mamaki tace.
"Mi aka miki? Ayya kin tuna da mamanki ne kiyi hakuri Allah ya jikanta."
    Kamar dama jira nake aikuwa na sake kuka, sosai kallona tayi sannan ta kauda kanta kamar tana wani abu, dan sam babu tausayina a fuskanta, sai ma share Ni da tayi har na gama kukan sannan tace min.
"Kije ki huta! Zuwa anjima sai ki fito."

  A hankali na mike na bar falon ina share kwalla.
           Tunda suka fita a gidan yake jero tsaki kamar tsaka. Kallon shi Aswad yayi cike da mamaki.
"Lafiya! Sai tsaki kake ja."

"Mantuwa nayi a daura,"

  Murmushi Aswad yayi cikin zolaya yace.
"Koda A gidan Maman Aliya!"
    Juyawa yayi ya kafe Aswad da ido, yaga hankalin shi na kan tuki,
       "Malam irin wannan kallon da"
         Kauda kanshi yayi ya maida jikin tagar motar.

    Har suka isa zaria babu wanda ya kuma cewa kala.
Suna shiga garin zaria kallon juna suka yi Aswad yace.
"Iska ba nauyi gare ki ba sai dai ka da itace."

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang