ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT😊*Kwanta ka mutu ka ga mai ‘kaunarka*
NAGAWURTA🌹
1️⃣3️⃣
Yana shiga zauren yaje gaban Shamaki ya zauna, sannan yaja tumtum ya kishingid'a akai yana kallon shamaki, wanda yake rike da bakin shi da hannun shi na dama, sannan hannun shi na hagu rike da wuka, kurawa Jamal ido yayi, sai gani yayi a idanun shi kamar yana caccaka mishi wukar a wuyar shi, ga Jamal sai motsi yake, tafi Jamal yayi sannan yace.
"Kawu Shamaki! Farka daga mafarkin da kake yin nan ba dagaske bane, ajiye wukar muyi magana da kai, idan kuma ka d'aga muryanka zan maka ba dad'i, na fi karfin na tsorata"Ya fad'a mishi haka, yana kuma kafe shi da idanu.
Tashi zaune Jamal yayi sannan ya diba mishi ruwa, ya mik'a mishi, sannan yace.
"Ban damu ka cigaba da mulki ko karka cigaba ba"Cikin fusata Shamaki yace.
"Kai har ka isa ka min kashedi ne! Ko Ubanka bai isa ba! Balle ke da baka san waye kai ba."Murmushin sosai Jamal yayi sannan yace.
"Kowa ka gani da tabarmarsa sai dai ya rasa wurin shimfi’dawa! Dan haka sanin Ni bai da muhimmanci! Abinda zan iya aikatawa shine me muhimmanci! Zaitun!!"Zaro ido Shamaki yayi waje, murmushi Jamal yayi sannan ya tura mishi ruwa gaban shi yace.
"Sha!"
B musu ya dauka ya sha, yana kallon Jamal.
"Ban so bakwai ga haka! Kawai abinda na sani, zan iya d'anna tarko! Mace ta fad'a, kuma nayi wasa da zuciyarta! Naji ance itace karama a cikin gidan nan kuma y'ar da aka fiso! Toh ya zaka ji idan nace maka sirikina! Abbana yayiwa Jamalah miji! Dan haka salin alin zasu zo niman aurenta a cikin saba'ar watan nan shine nake son tun wuri ka cire wancan zarerren d'an naka a layin da ka shatawa Jamalah! Domin kuwa idan hakan bai samu ba, ba abin mamaki bane agwagwa da kin ruwa! Yare na gaba kai zaka bada labarin yadda muka yi dakai!"Yana gama fad'ar haka ya mike zai fita aikuwa Shamaki ya daka mishi tsawa.
"Kaii!"
Cak ya tsaya sannan ya juya a fusace ya d'aga murya yace.
"Nafi karfin na tsorata!!!"Sai da zaure na uku suka ji ihun Jamal, shi kansa Shamaki sai da ya razana, dan sai da ya tashi zaune.
Sannan ya nuna mishi hannu yace.
"Karka kuma kira na da Kaii! Jamal nake! Idan kuma hakan ta kuma faruwa zan cire maka harshenka, wannan itace kashedi na ta karshe da kai in ba haka ba zanyi maka abinda bakai tsamani ba, ba'a d'aga min murya dan Ni zaki ne! D'aya gayya ne! Iya Ni ke zuwa farauta bana niman y'an tayi! Bana cin sauran kowa sai dai a ci saura na! Na gaya maka matukar ka nace tabbas zan mai da maka d'anka mace, Zaitunah kuma zan shafa mata bakin fentin wanda bakin cikin haka zai sanyan ka barin daura da kafarka! Karka Kure ni, dan matuƙar nayi fushi bana saurar kai na! Bana ji bana gani sai nayi abinda nayi niyya"Wukar da ya dauka lokacin da Shamaki yake shan ruwa ya wurga sai da ta caki wani tumtum, sannan ta tsaya a tsaye.
Fita yayi daga zauren ya samu bayi cirko cirko, yana fita suka shiga gulma abinka da gidan sarauta masu jiran tsegumi har amfara yawo da abin wai Jamal yayiwa Shamaki tijara.
Cikin bakin ciki Shamaki ya kwana, kwanciya zai farka zubur ya zauna kalmar Jamal na karshe tana mishi yawo akan shi,
*Nafi karfin na tsorata!!!"
Da zaran yaji kalmar hatta hantan cikin shi kad'awa take, dan haka gari na wayewa ya tura aka kira mishi duk wani shugaba dake cikin masarautar, sai da suka taru. Sannan ya fito niman guri yayi sannan ya zauna, yana kallon su kamar yadda suke kallon shi, su kallon yadda yake muzurai yake.
Shi kuma yana niman wanda zai nad'a ne yaje yaci mutuncin Jamal shi yasa sukewa juna kallon biri, shi kuma yana musu kallon ayaba,
STAI LEGGENDO
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Narrativa StoricaA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...