ƘWARƘWARAH!!?
{ITAMA MATAR SARKI CE}
_HAZAKA WRITERS ASSO...._
ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹3️⃣1️⃣
Ganin da nayi tunanin makomata zai hana Ni! Sukuni sai na mike tare da zubawa tagata idanu.
Tare da mai da hankali ga abinda ke gibtawa ta tsakanin taga na da, wani gurin kamar wacce aka wani na d'aga labulen
Ina d'agawa kuwa naga wasu irin mutane sun zuba gwiwar su a kasa, duk jikin su ya b'aci da jini.Wasu irin taurari naga suna yawo a tsakanin idanuna ban san lokacin da na zube a gurin ba. Su mammiya.
---
Kura mishi ido tayi cikin damuwa, sannan ta sauke a jiyar zuciya ji take kamar babu wata cutar makanta a tare da shi, sabida Yadda yake zaune idanun a bud'e."Jamal!"
Ta kira sunan shi a hankali.
"Na'am Umma!" Ya amsa mata a sanyayye,"Zan zauna naga yadda jikin naka zai kaya!" Tace mishi,
Murmushi yayi sosai, sabida jin daɗin yadda Umma ta nuna damuwarta akan shi, ko Umma Fulani bata damu da halin da yake ciki ba.
"Umma Na gode! Akwai Yarinyar nan tana kula dani, babu wani matsala."
Murmushi tayi itama sannan tace.
"Yarinyar tana da hankali! Sai dai akwai abinda yake bibiyar alamarinta!"Mik'ewa tayi sannan ta dauki lulluben da ta rufe kanta dashi.
Tana kallon shi, sannan ta cigaba da cewa.
"Tsinuwar da aka yi na shekaru aru aru, yana bibiyarta! Me yasa sai ita? Meye alaƙarta da masarautar nan? Kai na ya kulle! Na rasa mafita. Ina jin tsoron kar nan gaba abubuwan su ta'azara.""Insha Allah! Babu abinda yafi karfin Allah, ki kwantar da hankalinki!"
Yace mata a sanyayye!Juyawa tayi ta kalle shi sannan ta fice daga d'akin.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tsurawa wani gefen can idanu, yana nazarin abubuwan da suke faruwa.
---
Hmm wannan Kawun nawa kamar me almatsotsai! Yanzun yanzun zamu shirya zuwa anjima zai birkice min har sai ya sani kuka, kowacce rayuwa akwai jarabta yawa rayuwar Jamal ne jarbta na, gashi kamar wanda yayi min asiri wallahi bani ganin ganin laifin shi sai ma burgeni da yake.Musamman idan yaci magani yana shan kamshi, a raina nakan ce Izzar ta motsa. Dole ya nuna min Ni ba kowa nace.
Yau kam wanzami mai martaba aka kawo ya Mishi gyaran fuska, sai dai tunda naga mutumin raina ya b'aci, shima kuma na fahimci ya razana da ganina. Dan sau uku yana kuskuran kawun.
Da ya gama Askin zai tafi na mika mishi hannuna, dan wani abu nake hango a cikin jakar shi.
Diririce min yayi yana cewa.
"Ke bani son damuwa me zan baki."
YOU ARE READING
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)
Historical FictionA zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun...