1️⃣9️⃣

3.3K 329 29
                                    

ƘWARƘWARAH!!?

{ITAMA MATAR SARKI CE}

_HAZAKA WRITERS ASSO...._

ʍaɨ_ɖaʍɮʊ
օʊʍ ʍʊաaɖɖaɦ

#MY ZAHRAH🌹
Gabaki d'aya Labarin sadaukarwa ce gareki😍
ZAHRAN-ADDA RAMLAT🌹

1️⃣9️⃣

    .......
Tunda ya bata abinda zata yi jikinta yayi mugun sanyi ita tazata, tafi kowa sharri sai akayi rashin dace akwai wanda ya fita, mik'a mata kwaryar zuma yayi sannan yace.
"Ki bawa wani ya kaiwa Rumanah!"

Zaro ido tayi cike da fargaban abinda zai je ya dawo, bakinta na rawa tace.
"Sarki Jalaludeen bai san tana raye ba! Idan aka fahimci da saka hannunta cikin wannan lamari wallahi komai zai iya faruwa, kawai ka bada wata shawara amma banda wannan"

   "Kece kika ce zaki bada rayuwarki dan fansa amma yanzun kice min! Kina tsoro! Anya jakadiyar da nasani ce kuwa ko wata Sahurar ce! Kece kika da Has! Ya shiga jikin dokin Sarki Jalaludeen!"

"A'ah Shamaki! Kaine ka bani abinda na tadda shi karka juya min baya, sabida buƙatarka mana! Koma me zan maka amma banda."

     "Ba zaki iya kisan kai ba! Toh sabuwa da kika kashe fa?!"
Shiru tayi ta rasa ta inda zata kub'ucewa Shamaki domin duk inda tabi yana da hanyar tsare Mishi ya toshe!

    Kaskantar da kanta tayi sannan tace.
"Umarnin ka nake jira!"
"Toh kiyi yadda nace, idan aka samu matsala akanki zan juye komai, kibi Ni a sannu"

    Gyad'a kai tayi sannan ta dauki kayan ta ficce, sannan ya fashe da dariya yace.
"Idan gamba tana da dadi a nono, nono ma yana da dadi a wuri'n gamba" cikin farin ciki yake hango Ya kawo karshen Jamal.

          ---
Ciwon kan da yake damuna shi ya haifar min da zazzaɓin me zafi, kafin wani lokaci na fara fita hayacina, dake an kwanta. Rufe kaina nayi sabida sanyi da nake ji, can da zazzaɓin yayi kamar ya sauka sai na samu barci.

              Cikin barci naji sautin da na manta dashi a rayuwata, domin tunda na daina saka b'acin rai na daina mafarkin Nan, jin karar sarkar tare da jan rigarta, buɗe idanuna nayi. Naganta dab dani ana jan wuyarta da wani sarka. Sai mika min hannu take, tana magana cikin jan numfashi jini na zuba a hancinta da bakinta, sai idanunta da kuma jikinta, wanda yake jeke da jinin.

"Ki...je.. ki...ce... Shi! Karki bari su..."

     Haka aka jata ba tare da ta karasa maganar ba, binsu nayi suna janta, har can ganuwar nan suka, daureta sannan suka fara gineta.

"Yaya! Sannu tashi ki bar ihun nan mafarki kike babu wacce aka gine."

    Inji Aliyah, wacce take rike dani. Sakamakon mafarkin da nayi ina ta ihu, tashi nayi zaune.

"Addu'a zaki yi sai ki koma ta hannunki na dama ki kwanta." Kamar yadda tace, haka nayi sannan muka koma barci.

          ---
Washi gari.
Za ayi hawan Sallah, dake ina barci ban tashi ba duk sun gama shiryawa, har zan tashi sai naji am matsani tashi.

        Zuba min duka akayi na buɗe ido dakyar, kuka take jini na zuba a idanunta.
"Kije ki dakatar dashi! Kar ya amshi kyautar da zasu bashi, kuma ki hana shi hawa d..."

    "Jannart wannan wani irin shashanci ne haka, zamu tafi kallo amma kina kwance har yanzun"

Tashi nayi zaune ina kallon ta, a zahirin gaskiya ba ita nake kallo ba, matan nan nake kallo a jikina, d'aga kanta tayi ban san lokacin da na fasa ihu, tare da zuɓewa a kasa.

          A rikice tayo kaina, tare da d'ago ni, tafita da gudu ta kira wasu bayi biyu suka d'agani zuwa falo, ruwa suka watsa min har na farka, kuka na tashi dashi ina cewa..
"Mama kice Kawu kar ya tafi.."
Makalewa maganar tayi sakamakon fitowa da yayi cikin shigar sarauta, zuba min ido yayi cikin mamaki, kafin ya janye daga kaina, rike mama nayi sakamakon sarawa da kaina yayi,  da karfi nace.
"Karka fita!!!!"

K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE)Where stories live. Discover now