*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na abar alfahari na. Allah ya raya Auta Al amin Ameen. Allah kara budi da rayuwa mai albarka.*
3⃣ - 4⃣
Yasmeen tana tafe gidan tsit dan lokacin dayan dare har ta gota, tana shiga babban compound dakin ta nufa. Kan gado ta fada ta fashe da kuka, mesosa rai tana son Ahmad tun da ta taso da son sa ta budi ido duk wata hanya da zata soshi sai da ya koya mata ya nuna mata zasu shaku sun kuma shaku har ya zamana bata da kawa ko amini sama dashi. Amman kuma yanzu yana neman nuna mata abin da ake zato ba haka bane gashi ko saurayi bai bata damar yi ba domin jama'a da dama sun gama yanke hukuncin auren gida za ayi musu, a can baya duk sanda akai tuntube da zancen takan cewa 'nima ban sani ba,' amman a ranta dadi take ji, to yanzu tana ganin wannan maganar na neman tsayawa. To waye zata so kamar yaa Ahmad wato Yaa fauwaz? Waye zata aura ta ganshi kamar Yaa Fauwaz? Sai ta kuma fashewa da kuka lallai babu shi. Yaa Fauwaz kadai take so shine ta girma da sonsa tana sonsa koda shi be son ta, tana tsananin sonsa.
****************** *TUSHEN LABARIN* ******************
Alhaji Ahmad Bafulatani ne usul da yazo daga garin katsina da mai dakin a Hafsa fatauci ne ya kaso garin Kanon dabo, fari ne sol har da wani da siririn billensa na bangaren hannun hagu a fuskar sa, sanda ya iso kano bai da 'da ko daya sai dai ba wai haka daga ya shigo kanon ba a'a daman yana zuwa yana kawo fatu yana komawa abun ya shahara ne ya taho da mai dakin sa bayan ya sayi gidansa a unguwar dan agundi.
Anan kanon ya haifi ya'ya Hudu maza uku da mace daya ta dawo kano da nasibi dan kasuwancin sa ya habbaka idan ya barwa dan uwan gidan da yake ciki ya gina nasa a sharada tunda yafi kusa da inda kamfanin sarrafa fatu yake. Ya'yan sa hudu Suleiman, shine babba sai Abubakar sai Abdulkadir. Sai autar su Fatima. Rayuwar gidan rayuwa ce ta kaunar juna kowa nason dan uwansa da zumunci daya. kusan katsinawa da son karatu duk ya'yan nasa yasa su a makarantar duk da shi iyakacin sa secondary nan ya tsaya amman ya tsaya tsayin daka dan su samu karatu mai zurfi. Hakan nan ya sanya duk basuyi aure da wuri ba, musamman Suleiman da shine babbansu sai da ya kammala masters lokacin shima Abubakar Ya kammala anan ya baro maganar aure, nan fa aka hau Suleiman da gori Allah ya sanya shima yana da tashi a hannunsa don haka yace shima fa ya shirya, wannan ne ya sanya aka tsaida ranar biki daya.
Alhaji Ahmad ya gina musu gida guda biyu kowa da nashi, gidane mai kyau wanda dakunan dake gidan sunyi goma da ko wanne part 3-3 ne a gidan.
Part daya na matansu, daya na mazajen dayan part din aka rufe dan ya'ya maza in Allah ya basu. A kowane part akwai bedroom guda biyu da falo da kitchen sai wani daki a nan compound din bayan bangaren masu gadi. Dan gidaje gate daya ne, sai kowa hanyar da za'a shiga gidan nasa.
Zaman su suleiman da Abubakar zamane na kwanciyyar hankali da son juna, Suleiman da matar sa Amina shi kuma Abubakar da matar sa Aisha, sun nunawa matan nasa soyayya da nuna son yan uwansu, dan haka suma suka tashi da zumunci sam basa tada hankalin mazajen su, sun zama ya da kanwa. Duk kan su suna da hankali da ilimi dan haka kowa na kokarin yiwa mijin sa biyayya da zaman lafiya a junan su.
kusan lokacin daya Allah ya basu ciki inda Amina ce ta fara haihuwa ta samu dan ta namiji me kama da mahaifinsa. Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Wato Ahmad ake kiransa da Fauwaz yaron yaga gata kowa na sonsa gashi tibarkallah kyakyawa dashi. Yana samun kulawa satin sa biyu Aisha ta haihu, danta namiji inda shi kuma yaci sunan kanin kakansa Abdullahi suke kiransa da Ayman, yaran sun tashi cikin koshin lafiya, sai dai watan su biyar Allah ya amshi rayuwar Abdullahi wanda ciwon ciki ya tasar masa cikin daren lokaci daya ya rasu. Haka akai kuka akai masa addu'a bayan nan suka cigaba da rayuwar su suna kula da Fauwaz.
Shekarar Fauwaz uku Allah ya sake basu ciki shima kusan a tare inda Amina ta haifi Ishak Aisha kuma ta samu Nasir daga nan haihuwa ra tsayawa Aisha inda Amina ta kuma haihuwa cikin shekara tara Amina na da yara hudu inda Aisha keda yara biyu daya ya rasu sai Nasir, tun daga lokacin ta haihuwar ta tsaya musu. Yadda yaran suka tashi baza ka iya ban bance dan wannan da wannan ba kowa na son dan uwansa, suna kiran Suleiman da Alhaji Babba, shi kuma Abubakar suna kiran sa da Alhaji Karami inda suke kiran Amina da Mommy, Aisha kuma da mie mie, Alhaji Babba yana aiki a hukumar kudadden haraji ta kasa, Alhaji karami kuma a NNPC yake aiki. Dan haka ya dan dara yayan sa a samu duk da dai dukansu suna hadawa da kasuwanci musamman hannayen jari. Inda yanzu Suleiman shima yana da company sa na kashin kansa, anan sharada.

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.