21-22

555 39 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

2⃣1⃣ - 2⃣2⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

Daga nan gun Abba ya isa mahaifin Yasmeen Abba ya amshi batun sa hannu bibbiyu dan bai nuna komai ba duk da shima yasan Fauwaz din na son Yasmeen amman bai sani ba ko sun daina soyayyar. Dan haka yace zai yi wa su Baba da Alhaji Babba da Karami magana. ita kuwa Ummi kanwar Maman Yasmeen matar Abba a yanzu a ranta tace
"Kenan Fauwaz ba son Yasmeen yake ba lallai abin mamaki."
Haka tai shiru dai.

Abba kuwa a lokacin ya tafi gun Alhaji karami da zancen. Alhaji Karami dake falo tare da Mie mie ya zauna bayan sun gaisa ne  yace
"Yaya mai sunan Baba ne ya sameni da batun aure yake so."

Alhaji karami yai dariya yace
"Toh yanzu kuma da karatu yai wa kawar tashi yawa ai da bari yai ta karasa ko?"

Abba yace
"ai ba da ita bane. Yace min yar gidan Alhaji Ibrahim da sukazo dubashi a asibiti yake so."

Alhaji Karami cikin mamaki yace
"Au ba yar gida za ayi ba."
"Ni dai abinda ya fada kenan."

Waya Alhaji karami ya dauka ya kira Fauwaz yace ya same shi a falon sa. Ba a jima ba sai gashi ya shigo. bayan sun gaisa ne Alhaji Karami yace
"Naji wani batu gun Babanka."

Kan sa a kasa yace
"Eh ni na same shi da batun."
Kai Alhaji Karami ya jin jina yace
"Ai na zaci yar gida za ayi da kanwar ka Yasmeen."

Kan sa a kasa dan sai yanzu yaji kunyar Abba mahaifin yasmeen da yakai wa maganar duk da dai shi bai taba cewa wani yana soyayya da Yasmeen ba ko yana son ta. Amman sai yaji kunyar yace baya son Yasmeen a gaban idon mahaifin ta. Dan haka kai a kasa yace
"Alhaji wallahi ba soyayya a tsakani na da Yasmeen sai shakuwa da zumunci kawai ka kirawo ta ka tambaye ta kaji."

Alhaji Karami yace
"A'ah mai yayi zafi. Allah taimaka. Bari muje gun Baba muji yadda mukai shawara zan gaya maka."
Kai a kasa ya mike yayi godiya sannan ya tafi.

Abba da Alhaji Karami suka tafi gidan Baba yana zaune shi da mama a falo suna hira tana dama mishi fura suka shiga. Sai da suka gama gaishe gaise sannan Abba yace
"Baba takwaranka ne ya aiko mu."
Baba ya mike zauna yece
"Ja'iri ku ya aiko da kan sa. Menene aiken da shi ba zai iya ba."

Nan Abba yace
"Daman lokaci ne yayi yazo yace yanzu ya shirya zai yi aure."

Baba ya hau cewa
"Alhamdulillah Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Lokaci yayi kenan. Shi da yadauko aure kuma matar tana tsaka da karatu. Amman ba yadda za muyi haka za ayi tinda ya bukata."

Abba yace
"Baba wacce matar?"
Baba yace
"Uwata mana."

Shiru Abba yayi sai Alhaji Karami ne yace
"Ai Baba ba da ita za ai ba. Wata ya gano da ban."

Mama da batai magana ba sai a yanzu da taji wani zance sannan tace
"Me kuke fadi ne haka? Shi Mai gidan nawa ne yace ba Uwata zai aura ba wata yake so?"

Kan su Abba a kasa Alhaji Karami yace
"Haka ne Mama. Nima da Abdulkadir yazo min da magana na zata da Yasmeen din ne sai da na kira shi ya fada mana da kansa da nace na zata yar gida za ai sai yace a'ah shi ba zancen soyayya tsakanin sa da Yasmeen. Amman ko a kira shi a tambaye shi."

Mama ta kalli Baba tace
"Me zaka ce Alhaji"
Baba yai shiru na mintina kafin yace
"Ni duk abin ya dauren kai ne. Amman ina son a kira min Yasmeen da shi Ahmad din tukkunna."

Abba yace
"Insha Allahu gobe da safe zasu zo."
Baba yace
"Har daku gaba daya zaku zo."
Nan sukai sallama suka tafi.

Washe gari da safe Abba da kansa yaje ckul din su Yasmeen ya dauko ta gaban ta sai faduwa yake dan bata san me ya faru a gida ba har Abba yazo daukar ta. Har da hawayen ta. Hankalin ta bai tashi, tashi ba sai da tagan sunyo hanyar gidan su Baba na. Ta tsorata kar dai ace yan tsofafin tane suka rasu wanda duk zuri'ar bada wanda ta shaku bayansu Mommy sai su kamar yadda suma suke son ta. Sai da suka shiga taga Baba da Mama ne ta fada jikin su tana kukan dadi dan da duk hankalin ta ya tashi.

Sai da suka zauna sai ga Yaa Fauwaz nan da Alhaji Babba da Alhaji karami. Gaishe su tayi gaba daya sannan suka zauna. Sai da Abba ya bude taro da addu'a sannan Baba yace
"Batun auren Ahmad ne, naji ana magana daban da ban san ta ba."

Alhaji Babba kai a kasa yace
"Wallahi Baba nima haka naji."
Kai Baba ya jin jina yace
"Ahmad shin ba soyayya kuke da uwata ba tun da?"

Kan Ahmad a kasa yace
"A'ah Baba sam ba soyayya tsakani na da Yasmeen sai dai shakuwa ta zumunci. A tambaye ta ma gata nan."

Baba sam bai ji dadi ba amman sai ya kalli Yasmeen yace
"Uwa ta fada min gaskiya kinji."

Ran Yasmeen in yayi dubu ya baci yanzu daman aure zai yi shine aka ce ya aure ta yace yana da wacce yake so. Akan haka aka kira ta tai sheda. Ita kam ko son Yaa Fauwaz zai ajalin ta ba zata ce tana son sa ba. Dan haka tace
"Baba gaskiya ya fada ba soyayya a tsakani na dashi sai zumunci."

Mama ta hau salati da tafa hannu. Tace
"Uwata zo nan fadamin gaskiya kinji."
Matsawa kusa da ita tayi. Zuciyar ta na tukuki ta kama hannun Mama ta kwantar da kanta a cinyar ta. Hakan da tayi sai ta bawa kowa tausayi tace
"Mama ku bar Yaa Fauwaz ya auri Anty Billy sam ba ruwan ta tana da kirki."

Kanta Mama take shafawa tana mai jin son yarinyar na ratsa ta. Abba yace
"To shikenan magana ta kare kai Baba na ka fadawa iyayen yarinyar ranar litinin zamu zo. Allah ya sanya alheri ke kuma Allah baku miji na gari."

Baba yace
"Amman gaskiya ni da uwata naso na hada shi."
Mama tace
"Ina uwata ba ita ba gidan kishi dan yadda yake son waccen sai azalunci yarinya ba ruwan ta ga hakuri."

Shi dai Fauwaz sai godiya yake ga Allah da yasa Yasmeen tace bata son sa. Har da yabon Billy sai Kuma da yaga Mama tace uwar ta bata zuwa gida kishiya amman yasan da Baba ne sai ya idda nufin sa.
Dan haka Abba yace
"Tashi kaje Abin ka Baba na."

Ya durkusa yai godiya yabar dakin Yasmeen kam ko kallonsa bata kara yi ba.

Baba yai ta sawa Yasmeen Albarka yana fadin
"Allah kema ya kawo miki mijin."
Su Alhaji babba da karami suka amsa da amin.

Mikewa tayi tai ciki tana fadin
"Mama me zan samu a dakin naki ne?"

Tai ciki. Tana shga bedroom din Mama fada saman gado tana sakin wani kuka mai cin rai. Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta sai ajiyar zuciya take saukewa.

A can falo kuwa sai abin suke jajantawa dan kowa yasan yasmeen da Fauwaz soyayya suke. ko da basayi to a zuciyar su akwai son junan su. Baba so yayi a hada masa mata biyu amman Alhaji Babba yace
"Sam saboda yana son yar sa kuma yana son kwatar mata yancin ta dan ni kai na nasan Fauwaz na son Yasmeen."

Wanna yasa Baba ya bar zance hada su auren. Mama ma tace bata zuwa gidan kishiya. Haka suka bar wajen rai ba dadi ba ma kamar Baba da Mama.

*Don't forget to comment and vote*

Antyy ce🥰🥰

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now