103-104

979 44 1
                                        

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣0⃣3⃣ - 1⃣0⃣4⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*






Da dare kuma ta dafa masa jallop taliya wacce ta wadata da hanta ta masa farfesun kayan ciki. Sosai yaji dan Yasmeen kadan taci dan yadda ya cika mata ciki da abinci da rana

Daga nan falo suka koma suna hira tara da rabi ta tashi ta kalle shi tace
"Yayan mu bacci nake ji sai da safe."

Kallon ta yayi cikin so da kauna yace
"Allah ya tashe mu lafiya!"
Ya fada yana binta da kallo. har ta shige bangaren ta.

Tayi cikin dakin. Kayan jikin tata cire ya shiga tai wanka tare da dauro alwala tana fitowa ta saka sleeping dress din ta ta fashe jikin ta da turare ta haye tayi addu'a ta tofe jikin ta taja bargo dan tayi bacci. Tunanin rayuwa ta dinga yi da yadda komai ya faru har yau da ta zama matar wanda ta fiso lallai Allah yana son ta ashe shiyasa kullum tana addu'ar Allah ya cire mata son sa taga addu'ar kamar batayi wannan yasa ta dage da addu'ar zabin Allah da miji na gari kenan Yaa Fauwaz shine zabin Alah kuma zabin iyayen ta da ita kan ta.

Shin meyasa Alhaji karami yace mata wanda aka aure mata me son tane, me hakan yake nufi Yaa Fauwaz yana son ta ne kome? A'ah ya fadi haka ne ganin shi ya rike ta tin tana karama son da yake mata na jini ne ba na soyayya ba.

Ajiyar zuciya ta sauke tina abinda Abban ta ya fada mata shima ya jima yana mata kwadayin mijin ta kuma mijin ta me son ta ne da gaske. Lallai ko dan farin cikin Abba ta zauna da Yaa Fauwaz bare itama tana son sa. Abba yana son ta da Yaa Fauwaz kuma yana fadin Yana son ta da gaske. Amman ko soyayyar yan uwa yake min Allah ka juyar da ita ta dawo ta......"

Dakin taji an bude da sauri ta dago tana kallon sa daga gani yayi wanka kayan bacci ne a jikin sa farare sun masa kyau shigowa yayi ya zauna a gefen ta yace
"Bakiyi bacci ba?"

Kai ta gyada mishi tace
"Yanzu zanyi!"

Kai ya gyada yai mata addu'a ya tofa mata sannan yai mata kiss a goshin ta ya mike yana fadin
"Sai da safe!"

Kai ta gyada sannan ya fita ta bishi da kallo. Ido ta lumshe tana mai jin dadi a ranta ta samu zabin ranta. Tunanin me yasa aka boye mata wanda ta aura ta fara yi can tace
"Koma dai menene yanzu nagani kuma ina godiya a gareku iyaye na Allah ya ja kwana ya kara muku lafiya ya saka muku da aljanna. Hakika ko ba Yaa Fauwaz kuka ban ba zan kasance mai wa miji na biyayya bare kuma Yaya na mai sona wanda muka shaku. Allah nagode maka."
A haka bacci mai dadi ya dauke ta.

Yana shiga daki kan gado ya kwanta ya fara tunanin ta yadda zai samu ya nunawa Yasmeen son da yake mata ya nuna mata kulawa da soyayyar sa. Ya godewa Allah da ya bashi Yasmeen ya kuma godewa Abba da ya jajir ce har yasmeen ta zama rabon sa. Hakika duk wannan silar abokin sa ne kuma amini dan uwa da ya dinga masa kwadayin yar uwarsa. Yana son Marzuk domin aboki na gari ne. Da haka yai bacci yana mai mafarkin Yasmeen din sa cikin soyayyar su.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now