*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_8⃣3⃣ - 8⃣4⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
*Kamar yadda yau ta zama ranar mai tarihi wato ranar da aka haife ka a shekarun baya masu yawa ina maka addu'a akan Allah ubangiji yasa wannan ranar ta zama rana mai daraja da farin ciki a gareka. Allah ya kara maka wasu shekarun masu yawa da albarka, Allah ya albarkaci zuri'ar ka ya sa ka gama da duniya lafiya Amin. Happy birthday to the Admin of Admins. May your birthday be filled with graces, blessings and favours of the Lord and may your laughter never cease. Also may your life be renewed with crackles of laughter and the great feelings of affection; I wish you the best of your dreams. _HAYATU BABA ZUBAIRU (YAYA HAYAT)*
Kallon Fauwaz yayi yace
"Before an taba fada maka kana da ciwon zuciya ne?"Da sauri Abbas tare da Faywaz suka dago suka kalli Doctor, Doctor ya gyada kai yace
"Uhmm?"Kai ya girgiza yana fade kan sa da kirjin sa dake masa zafi.
"Am sorry Fauwaz condition din da kake ciki yayi worse dan haka dole na fada maka dan fada masa zai sa ka dauki shawarar da zan baka tare da kiyaye lafiyar ka. Shawarar da zan baka in har abinda kake so zaka iya samun sa kasan yadda zakai ka samar wa zuciyar ka nutsuwa da burin ta. Zan baka magani amman maganin ba zai taba warkar da kai ba har sai ka taimaka kai ma. Wato ka daina saka damuwa da abu a zuciyar ka in wani abu kake so ka samar wa kan ka shi to ta wannan hanyar ne maganin zai maka aiki in ba haka ba kuwa am telling you zakana shan maganin a banza ne wallahi, dan haka ka kiyaye ka dage da kula da kanka da kuma cin abinci dan naga ulcer ta kama ka kaji!"Kasa ko da motsi yayi sai Abbas ne yace
"Ok mungode!!
Doctor ya mike yana dafa Fauwaz yace
"Komai zai zama normal idan kaso. Fatan alheri da fatan samun lafiya mai daurewa a gareka"
Ya juya ya fita.Da kallo Fauwz ya bishi hakikanin gaskiya a yanzu bai san yaya zai yi ba bai da wata damuwa in ba ta tunanin yadda zai mallaki Yasmeen, ido ya lumshe wanda sukai masa nauyi da zafi. Numfashi yake ajiyewa a hankali a hankali, Abbas ya dawo kusa dashi ya zauna yace
"Fauwaz tashi muyi magana!"Ido ya bude yabi Abbas da kallo sannan ya gyara zaman sa. Zama ya gyara ya ce
"Fada min damuwar ka? Me kake so?"Ido ya lumshe ya kara budewa a ransa yace
"How can i tell you that all my problem is about Yasmeen, after all I tell you dat I didn't love her any more. Ya Allah see me through!"A hankali yace
"Abbas ban da wata damuwa fa. Ciwo ne kawai Allah ya kawo!"Wani Kallo Abbas ya bisa da shi yace
"Shikenan daman nasan baka dauken yadda na dauke ka ba amman ba komai zan ta taya ka da addu'a."Ya mike zai har wajen hannu sa fauwaz ya kamo yace
"Ba haka bane ka fahimce ni."Wani murmushi Abbas ya saki yace
"Never mind!"Ya koma can gefe har ya kwanta ya mike yace
"I forget to tell u that an bani Yasmeen sun saka rana amman ban san time in ba in naji I will tell you, ka tayani murna Yasmeen ta amshe ni."Wani irin tari ne ya taso masa dan haka yai tayi yana dafe kirji da sauri Abbas ya nufe shi aman jini yaga yana yi wannan yasa yai saurin dannan wata 'yar bell dake dakin ba a jima ba nurse's da likita suka shigo dakin a guje nan suka rufu akan sa.
Bayan sun ceto rayuwar sa Doctor ya dinga fada akan a daina sa fada masa abinda zai tada masa da hankali ko tina masa da wani abun. Nan dai aka lallaba akai masa allurar bacci.
Sam jikin Fauwaz yaki yai sauki, Hankalin Abbas duk ya tashi bai da nutsuwa dan sam Fauwaz ko idon sa ya daina budewa komai yi masa ake, in kaga yana abu sallah ce itama daga zaune yake yin ta.
A ransa fadi yake shikenan ya rasa Yasmeen, tabbas sai yanzu yasan Yasmeen ce mahadin rayuwar sa in har ya rasa ta ya rasa rayuwar sa. Ya yadda ya amince ya gama kamuwa da son Yasmeen kuma ya yadda dacewa son ta a jinin sa yake. Wannan abun in ya tuna da an saka mata rana dawani kan daga masa hankali har jikin bai gaba bai baya.
Ganin haka yasa Abbas Tunanin ya kira gida amman sai yaga in ya fada hankalin su zai tashi sosai dan haka ya yanke shawara ya kira Marzuk ya fada masa. Hankalin Marzuk ya tashi sosai dan haka ya fara shirin zuwa. Lokacin da yazo yaga Fauwaz ba karamin kaduwa yayi ba da yaje gun doctor ya fada masa duk abinda ke damunsa sai hankalin sa ya kuma tashi shin me yake damun Fauwaz da har ya shiga wannan halin yake barazana ga rayuwar sa.
Lokacin da Fauwaz yaga Marzuk ya bude masa hannu ya rumgume shi, kuka ya saka yana fadin
"Marzuk na rasa ta na rasa ta nasan ba zan taba samun ta ba. Nasan waye Abbas bai taba giving up a kan hope din sa in dai yana son abu Allah sai ya bashi sa'a. Marzuk ka fadan yaya zanyi, ka tayani addu'a akan Allah ya dauki raina ko na hu......"Bakin sa Marzuk ya danne yana fadin
"Ka daina fadar haka Fauwaz, kasaka tawakalli a ran ka ka sani in har Yasmeen matar kace ko mu jima ko mu dade zata zama taka abinda zan fada maka daya ne shine ka dage da addu'a akan in Yasmeen Alheri ce Allah ya baka ita in ba Alheri bace Allah ya cire maka ita a ranka ya saka maka dangana da tawakalli, a rayuwa in har zamu na yadda da kaddara komai zai zo da sauki, ka rike addu'a ita ce madafa kawai, sai shawara ta biyu ka sanar da Mommy da shi Abbas din!"Kai ya girgjza yace
"Bazan iya ba bazan iya ba Marzuk."Saman dakin ya kalla yace
"Allah kai ka dauran Son Yasmeen, Allah ina rokar ka akan ka kawon mafita a rayuwa ta Amin."Ya koma ya kwanta yana zubar da hawaye. Marzuk yace
"Ka daina kuka in kai bazaka iya ba ni zan sanar da Abbas din."Da sauri ya mike yana fadin
"Marzuk wallahi nasan a duniya ba wanda zai nunan son Yasmeen, dan ni tin tana yarinya nake jin ta a jini da tsokar jikina hakika ban san me ya rufen ido akan soyayyar Yasmeen ba. Bazan taba yiwa Yasmeen dole ba, tinda ita da kanta ta amshi soyayyar sa ba zan so taki samun farin cikin ta ba. Na jima ina tauye Yasmeen domin a rayuwar mu da Yasmen tafi son farin ciki na akan na ta, ta yadda take bin doka ta ko da hakan zai bata mata rai dan haka daga yanzu bazan kara takurawa Yasmeen akan wani abu ba. Zan so takasance cikin farin ciki har karshen rayuwar ta. Ina son Yasmeen nasan da son ta zan mutu, dan haka ina mai neman alfarma a gun ka da kar ka taba yiwa Abbas magana akan ina son Yasmeen dan Allah dan Annabi na roke ka dan Allah."Kallon tausayi Marzuk ke bin Fauwaz dashi jikin sa yai sanyi da maganar Fauwaz din tabbas Fauwaz yayi sanyi kuma ya yadda yana son Yasmeen dan gashi yau yana fifita son Yasmeen akan nasa. Dafa shi yayi yace
"Allah yana tare da mai rokar sa kuma da sannu zai amsa masa dukkan bukatun bawansa addu'a zamuyi tayi Fauwaz!""Nagode Friend Allah ya bar mana zumunci!"
Suka rumgume juna Fauwaz na share hawayen idon sa. Dagosa Marzuk yayi yana goge masa hawayen dai dai lokacin da Abbas ya shigo, ya bisu da kallo yana mai sha'awar yadda suke son junan su da amintar su, murmuashi yayi yace
"Amini yazo yau naga idon Fauwaz har yana iya kuka lallai Alhamdulillah! But ka sani Doctor yace ka daina saka damuwa ko?"Hararar sa Fauwaz yayi yace
"Sharri ko?"Nan suka zauna suna ta ban baki har ya kara sakewa. Zuwan Marzuk ya kara masa nutsuwa dan yana bashi shawara da kwantar masa da hankali. Kwanan Marzuk goma aka sallame su daga asibiti dan haka yace gida zai yo.

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.