*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_3⃣3⃣ - 3⃣4⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Zakuji na dan dawo baya ayi hakuri*
Zama yayi yana binta da kallo wanda duk taji ta tsargu kallon Ishaq yayi ya mika masa hannu suka gaisa sannan suka gaisa da Aisha.
Nan ya juyo yace
"Jiya kuma sai naji ki shiru. Daga kina zuwa. Nai ta jira, na tambayi Yayan ki bai kula ni ba yau ma na zo gidan da yamma amman ban ganki ba duk na rasa nutsuwa ta Baby, Ya kike? Ya da fatan kema kinyi missing dina."Murmushi tayi kawai. Yace
"Beauty muyi maganar gaskiya. wallahi son ki nake kuma da aure. Ki taimaka mun ki amshi tayi na.""Ni fa ba son ka ne banayi ba Yaa Abbas Ya Fauwaz ya fada maka gaskiya dan haka kayi hakuri ka bari nan gaba in kana cikin mazan da Yaa Fauwaz kemin sha'awa zai zabar min kai."
"Oh Yayan naku shi xai samar miki miji ko ya?"
Baki ta dan turo tace
"Ai yana da kyau na gaba ya maka zabe ko?""Haka ne! Toh yanxu in ya zabar miki Ni zaki amshi soyayya ta."
"Me zai hana? Duk abinda Yaa Fauwaz ke so nima ina so kamar yadda shima yake son duk abinda nake so."Dariya yayi yace
"Gaskiya ne Yaa Fauwaz naji dake ko acan bai da magana sai taki da farko ma na zata ke zai aura, jin ba ke bace yasa na fara kwadayin ki dan ba abinda ban sani ba akan ki. Ina fata ki zama uwar yaya na. Wallahi da gaskiya nake son ki Yasmeen!"
Murmushi tayi tace
"Nagode!"Juyawa tayi ta kalli Yaa Fauwaz wanda ya cika kamar zai fashe. Dauke kai tayi. Abbas yace
"Kinga Yayan ki sai hrara ta yake. Ban san meyasa baya son ace ana son ki ba!""So yake na gama karatu na!"
Dan murmushi yayi Yace
"In har za aban dama nai miki alkwarin har sai kince kin gaji da karatun nan da izinin Allah kuma sai kin zabi kasar da kike so kije kiyi karatu."Mikewa Aisha da Ishaq suka shiga fili suna shan rawar su. Muna zaune yana ta min wayo akan sai na amshi son sa. A gaskiya Abbas bai da makusa dan haka zan iya zama da shi wato zan iya auren sa.
Sosai ta sake da Abbas suna ta hira yana bata abun dariya sai dariyar take yi dimple dinta yana ta lotsawa ya kallen yace
"Inason wannan abin naki!"Na kai hannu ina taba wajen nai murmushi. Zan yi magana kenan naga mutum akan mu dagowar da zanyi naga Yaa Fauwaz ne. Shiru nayi yace
"Ke tashi a kai ki gida sha biyu saura!"Ba yadda zanyi na mike amman a raina ina son nace tare da su Aisha zamu tafi. Abbas yace
"Haba Fauwaz menene haka ne? Ka barta na mai da ta gida da kaina."Ko kallon sa bai ba bare ya sa ran zai kula shi. Muna fita ya nufi motar sa dani. Budemin yai yace
"Shiga!"
Ba musu na shiga ya kunnan AC ya rufe ya juya ya tafi.Haka na zauna ni ka dai a cikin motar tin ina jin dadin zaman har naji na gaji da zaman kadaicin. Abin mamaki har karfe sha biyu da rabi ba Yaa Fauwaz ba alamar sa. A haka har bacci ya dauke ni.
Karfe daya da rabi naji ana taba ni da sauri na bude ido na bude baki da shirin kwala ihu sai naji yana fadin
"Matsoraciyya nine!"wata wawar ajiyar zuciya na sauke ina bin wajen da kallo. sai lokacn na tuna a inda muke. Kallo na na dawo dashi kan sa yana zaune ya zuba min ido. Ganin da yayi har lokacin jiki na rawa ne yasa ya janyo ni jikin sa ya rumgume yana shafan baya a hankali sai da na samu nutsuwa sannan na janye jikina na koma jikin kujera na kwanta. motar ya tayar muka bar wajen. Wajen ba kowa kamar ba biki akai ba kowa ya tafi. Sai biyu saura muka karasa gida yana tsai da motar na fice ina fadin
"Sai da safe!"
Da kallo kadai ya bini har na shige sannan ya fita yana mika yayi bangaren sa.Sai da yai wanka sannan ya haye gadon sa. Ido ya lunshe zai bacci amman sam bacci ya gagare shi Yasmeen yake gani kawai zaune da Abbas suna hira har da dariya. Abinda ke kona masa rai kenan. Shi fa sam Abbas bai da aibu dan yasan shi sosai abokin sa ne ya tabbata in har maganar nan taje gun Alhaji Babba kamar an bashi ne. Da kyar bacci ya dauke shi.
Washe gari lunching akai, na gidan amarya su Yasmeen da yan gidan su, su Mie mie da Ummi duk sun je sunyi ankon wani maroon din less me adon golding sunyi kyau sosai. An karrama su a matsayin su na dagin Ango kuma suma sun yi banjinta dan sunyi masa liki kamar basu san zafin kudin ba. Ranar ma kyan da Yasmeen tayi har tai yawa. Kowa ya ganta sai ya yaba. Sai magariba suka tafi gida a gajiye dan ita Yasmeen har ga Allah har ta gaji da wannan hada hadar bikin ace kwana wajen biyar ana yi.
Gobe za ai daurin aure da yinin gidan ango dan haka ta lallaba Mommy akan cewa ita bata son zuwa Make up din nan. Mai make up da ta cankashi kudi tace zata zo har gida tai mata.
Da safe kan a tafi dauri aure tai wankan ta tai kwalliya cikin wata dakakiyar shadda orange kala, an mata dingin riga da siket tayi kyau batai make up ba amman tayi bala'in kyau powder kadai ta shafa sa man lebe Aisha tai mata dauri mai kyau ta saka dan kunne da sarkar gold har da abin hannu. Ta hade jikin ta cikin turare farin mayafi ta dauka da farin takalmin ta mai dan tudu. Ta sauko daga sama kenan waayar ta ta fara kara tana dubawa taga Yaa Fauwaz ne.
Tsaki ta saka tace
"To menene kuma?"
Bata dauka ba amman tana katsewa ya kara kiran ta. Wannan yasa ba yadda zatai ta daulko.
"Hello!"
Ya fada."Assalamu Alaikum!"
Tai masa sallama
"Wa'alaikum salam!"
Ya fada yana murmushi. Wani haushi ya bata wato yau sai murna yake zai angwance ko."Ina kwana?"
Ta fada murya ba yabo ba fallasa.
"Kina ina? Kizo ina daki!"
Ya fada yana kashe wayar. Dakin Mommy taje Mommy tace
"Kai masha Allah Yarinya ta tayi kyau sosai."
Murmushi Yasmeen tayi ta rumgume mommy tana fadin
"Nagode Mommy na."Ta sake ta tace
"Bari naje gun Yaa Fauwaz yana nema na."
Ta fita ta nufi bangaren sa. Yana zaune a falo sanye da farar shadda wacce tai masa kyau sosai. Bai saka babbar rigar ba sai yar cikin hular sa da takalmin sa na gefe. Tana shiga ya bita da kallon yadda tai kyau sosai. Murmushi ya sakar mata yace
"My princess tafi ta kowa!"Murmushi tayi tace
"Ango kasha kamshi."
Tsuke fuska yayi yace
"Fita zanyi nasan in na fita da kyar xanga wannan kwalliyar!"Dan murmushi tayi ta nemi gu ta xauna tace
"Au shine kiran!"
Wayar sa ya dauka ya fara aikin nasa wato daukar ta hoto, inda sabo ta saba ko da ma haka yake mata sai dai batai wanka ba amman yai ta daukar ta yana yabon kwalliyar ta bare yanzu da tasan ita kan ta tayi kyau.Sai da yayi yayi dan kasan sannan ya kyale ta yana fadin
"Bari nazo na tafi ana can ana ta jira na."
Ya mike ya saka babbar rigar sa ya daura hula ya zura takalman sa. Wani kyau yayi mata wanda bata taba ganin yai mata kamar sa ba. Ta sani Yayan ta me kyau ne amman yau kyan nasa ya wuce yadda take zato ko dan yau ranar sace. Bata an kara basai jin sa yayi ya dago ta yana fadin
"Bari muyi hoto!!Nan ya hau daukar ta. Daki ya shiga yai wanka da ruwan turare sannan ya fito sai kyalli yake. tare suka fita zatai cikin gida ya kira ta ta karaso wajen sa.
"Please princess anjima ki tayani hada kaya na man!"Kai ta gyada masa. Yai murmushi ya kama hannun ta sukai babban compound din gida tana biye dashi. Su Abba da Alhaji Babba da Alhaji karami da Baba da kannen suna compound suna jiran su suna zuwa suka gaishe dasu, iyayen sai kallon su suke dan ba karamin dacewa da juna sukai ba. Tana tsaye har suka tafi tana musu bye bye. Suna zuwa an taro abokan Yaa Fauwaz dana su Abba da dagin ango da amarya dan haka aka daura auren Bilkisu Ibrahim da Ahmad Suleiman Ahmad akan sadaki dubu dari biyar anan aka shaida aka tashi. Daga nan reception aka tafi akaci aka sha akai hotuna sannan suka tafi gidan su amarya.
*Wannan shine karashen page din jiya da na dan yi shi.*

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.