*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣7⃣ - 1⃣8⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_Not Edited
Tana gama komai ta hau azalzalar su akan su taso su tafi asibiti. Ai kam Aisha tace ta tafi sa taho da Anty Binta, wannan yasa ta fita driver ya tafi da ita. A asibitin ma daga Yaa Nazir sai Yaa Fauwaz. Tana zuwa Yaa Nazir yace shima tafiya zai yi tinda ya samu mai tayashi hira. Yana fita ya yafito ta da hannu alamar taje. Gefen sa taje ta zauna tace
"Ya jikin?"
"Da sauki Princess ya school din taki?""Alhamdulillah!"
Ta bashi amsa. Nan ya dinga jan ta da hira tin bata sake da shi ba har ta sake suna yar taba hira.Wajen karfe sha biyu sai ga Billy nan, tana shigowa, Yanayin Yasmeen ya canja. Shi kam Yaa Fauwaz duk hankalin sa na kanta. Yasmeen ta kalla tace
"Sister ya me jiki?"
"Da sauki."
Ta bata amsa suka gaisa. Ba kunyar Yasmeen ta karasa kusa ta dashi tana taba wuyan sa tace
"Ya jikin My Fauwaz?"
A share ya amsa mata da sauki. Wannan yasa Billy ta kalli Yasmeen tace
"Sis kisa baki Ur big bro fushi yake dani "Murmushin karfin hali Yasmeen tayi tace
"Big bro ayi hakuri."Ta mike tace
"Ina zuwa."
Ta fita ba tare da ta jira me zai ce ba.Da kallo ya bita dan yaga ta canja cikin lokaci kadan. Tana fita ya dauke kai daga kallon Billy. dawowa tayi gaban sa ya kuma juyawa ranta ya dan baci amman sai ta danne tace
"Ta gaban goshin ka fa ta baka hakuri "
"Wa yace miki hakuri shine abinda nake bukata."Kallon sa take cike da so dan ita kanta tasan tana son Fauwaz dan kwana biyun nan da sukai ba waya ba chat duk ta shiga damuwa dan haka tace
"To me zan maka?""Just accept my request."
Dan murmushi tayi tace
"Fauwaz bana son din our relationship to break.""Me kike tunanin zai karya alakar mu?"
"Wannan auren da kake so muyi man.""Kinga Billy ki tsaya ki gane mai aure yake nufi, ke kanki ki aure zai saki samu nutsuwa sosai da kwanciyyar hankali. A gaskiya in ba zaki yadda muyi aure ba dole ko wacce irin mu'amala tamu ta yanke."
Kai ta langwabe dan sam bata son rabuwa da shi.
"Zan yadda na aure ka bisa sharadi daya dan ka ruguza min all my plam ban san when zuciyata ta canja akan ka ba. Anya bakai min asiri ba."Ta fada tana dariya. Wani sanyi yaji yana ratsa sa dan shi yaddar ta ita yafi bukata ba jin wani sharadin ta ba.
"Fauwaz a rayuwa ta ban taba kawo zanyi aure yanzu ba dan ban sha'awar sa ko ra'ayin sa, dan haka dole in zamuyi aure ka kula dani and most abinda bana so shine takura yadda nake a gida haka nake so na cigaba dayi and also about my work zanci gaba da aiki na and also zan koma 'karo karatu duk ka yadda if not let say gud bye."Hannun ta ya kamo yace
"No dear please don't say dat word please. all u want I will do it for ur happiness I love u Bilkisu, I really love u."Ya fada yana jin kamar ya hadiye ta. Rumgumeshi tayi tana masa kiss a kumatu wani iri yaji a jikin sa. ido ya lumshe sannan ya bude yana kallon ta ba abinda yake so sai auren su ya gansu a matsayin mata da miji duk kanta ta zama tashi da yafi ko wanne namiji sa'a a duniya.
Yasmeen kuwa tana fita can bayan dakin ta koma ta zaune tana ta kuka ta dade tana kuka sannan ta wanke fuskar ta. Tana zagaye harabar asibitin. Bata dawo dakin ba sai da Ta tabbatar a time din ta tafi. Tana shiga ta sameshi idon sa a lumshe sai murmushi yake. Bandaki ta shige tayo alwala ta tada sallah tana cikin sallah su Anty Binta suka zo. Abinci suka zuba masa yace
"Yasmeen zo ki ban abinci."
Zama tayi tana bashi yana ta mata surutu. Daga kallon yanayin sa yana cikin farinciki dan sai murmushi yake a haka su Mommy suka shigo suka same su. Yinin ranar waya ya yini yana yi bayan Sam Yaa Fauwaz ba ma'abocin waya bane. Kuma yadda yake kasa kasa da murya daga gani da mace yake yi abinda ya bata ran Yasmeen kenan har tace zata tafi gida da su Mommy zasu koma. Anty Binta taso ta bita tace yau gun Mommy zata kwana. Haka suka tafi ita da Aisha. Tin daga ranar bata kara zuwa asibiti ba sai dai kullum zatai masa abinci na safe, rana da dare in yace tazo zata tai masa kwana kwana. Dan ana bata labarin kullum sai Billy taje har da Mum da Dad dinta ma sun kara zuwa. Wannan yasa bata kara zuwa ba sai ta waya take masa sannu. Yana mamakin me ke damun Yasmeen dake gudun sa haka. Amman sai yace ko dan ta fara girma ne oho.Yasmeen kuwa tunda ta koma makaranta ta kara mai da hankalin ta kan karatun ta dan yawanci yanzu suna asibiti ma ko da yaushe. Duk namiji mai hankali da zai ga Yasmeen sai yayi kwadayin ta. Amman sam ita sai dai ta basu hakuri wannan na batawa Aisha rai har tayi fadan tayi fadan ta gaji sai addu'a take mata.
Yaa Fauwaz kuwa soyayya suke sosai shi da Billy dan ko da yaushe suna tare in basa waya suna tare da juna. Daga yadda yake tafiyar da ita ta kuma aminta da son auren nasa.
Don't forget to comment and vote
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.