*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_5⃣ - 6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_Lokacin da Fauwaz yaji abinda su Alhaji Babba suka ce dariya ya dinga yi dan shi a lokacin ko budurwa bai da ita ball dinsa ita ce budurwar sa. Amman sai yaga da gaske su Alhaji Babba suke wannan ya tada hankalin sa sosai dan har yaji Alhaji Babba na cewa zai samar masa mata inbai da wacce yake so. Gashi har Baba ya shiga maganar wanda yasan ba mai taimakon sa. Da yasmeen ta ga halin da ya shiga da kanta taje gun Baba falo ta same shi ta marairaice tace
"Baba a gida ba wanda aka tsana sai Yaya nah, Baba shi fa ba aure zai yi yanzu ba amman Alhaji Babba duk ya takura masa Baba kasaka baki dan Allah."
Har da kukan ta Mama na lallashin ta. Nan fa Mama tace
"Gaskiya Baba kasa baki dan ni da akwai abinda ya na gano tsakanin Mai gida na da Yasmeen."
Nan suka lallabata ta tafi sai bayan tafiyar ta Mama tace
"Ai ni a gani na Mai gidan nawa Yasmeen yake so dan yadda suke kaima kasan da alamar tambaya"
Dariya Baba yayi yace
"Kaga ja'ira kace ita sani tama shine take kukan kishi."
Nan Baba ya kira ta yace
"Ta kwantar da hankalin ta inda Fauwaz ne ba za ai masa aure ba har sai lokacin da ta girma a musu tare."
A lokacin bata gane abinda ake nufi ba amman dai sai taji kirjin ta ya buga. Dan haka ta dinga godiya. Ai kam Baba ya dakatar da son ayiwa Fauwaz aure da Alhaji Babba yake shirin yi. Fauwaz kuwa da yaji labarin Yasmeen ce aje ta sawa Baba kuka sai ya kara jin kaunar ta na kara shigar sa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin kwanciyyar hankali. In har Fauwaz yazo gida ya kan dauki Yasmeen su ta zagaye gidajen yan uwa har da abokan sa. Kuma in ka gansu ka rantse da Allah masoya ne.Yasmeen yarinya ce mai nutsuwa da hankali hayaniya ma bata son ta magana sai ta ga dama. Ba'ka ce amman bakin ta mai kyau ne, tana da diri mai kyau da tsari dan kirjin ta a cike yake haka nan mazaunan ta. Sai gashi kamar me dan duk fuuskar ta ma gashi ne a kwance, haka kanta yana da cikar gashi mai yawa da tsayi. Bata son kitso sai Yaa Fauwaz yayi da gaske take yadda, ko ya kai ta da kanshi take yadda ai mata tana kuka da komai zai hade fuska har sai an mata. Sai kuma yai ta yabawa. Wani lokacin da kan sa yake tsefe mata kai ya wanke yayi drying kitson ne dai bai iya ba amman har kalba yana mata. Tun tana primary ta sauke alkur'ani inda tana jss ta haddace sa. Yanzu haka tayi graduation tayi jamb inda ta cike medicine a nan BUK sam bata da kawa in ba Yaa Fauwaz ba komai shi kadai take fadawa daga shi ba wanda take fadawa damuwar ta.
****************** *Cigaban Labarin* ******************
Karfe tara na safiyya ya shigo bangaren iyayen sa bayan yayi wanka yana sanye da kananun kayasa baki wando da farar riga sai tashin kamshi yake shi sam ma ya manta da sunyi fada jiya. Dan haka yana shigowa ya fara kwada mata kira yana fadin
"Princess! Princess!"
Mommy dake kitchen ta leko tana fadin
"Kai kada ka cika mana kunne, bacci ina jin ta koma tinda jiya ka gajiyar da ita ko karfe nawa kuka dawo ma oho. In abinci ne ta barwa dela ta baka."
Kai ya sosa yace
"Tuba nake Mommy. Ina kwana."
Hararar sa tayi ta amsa ta koma kitchen din. Jim ya tsaya dan yasan inda Yasmeen taki kawo masa abinci to ya mata wani laifin ne. Dan yasan indai yana garin ita take kawo masa abinci daga na safe, na rana da dare. In kuwa bata kawo masa ba to sunyi fada ne amman shima bazata ki yi masa ba zata girka ta bar sallahu in yazo a bashi. Murmushi yayi saboda ya tina abinda yai mata.
"Princess kenan!"
Ya fada yana yin saman bene inda dakin ta yake a ransa yana fadin
'iya fushin fa kenan.'
Dan in dai tai masa haka to ta huce kenan.
Mommy ganin yai sama ta leko tana fadin
"Kada ka tashe ta, haka kawai jiya baka barta ta huta ba yau ma kace bazata huta ba da kasamu ma tayi maka girkin ai sai ka godewa Allah."
Ta fada tana kallon sa.
"Mommy bari na dubo dai kinsan Baby bata baccin safe kila bata jin dadi kinsan ba son shan magani take ba."
Ya fada yana bude dakin. Girgiza kai tayi ta fito ta nufi bangaren Alhaji Babba.
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.