*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_9⃣ - 1⃣0⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_Ina mika sakon gaisuwa ga *Amina (Mommy nah) tare da yaran mu, Fatima (Binafa) da Nafisatu (Neenah, Our mommy's namesake)* Allah ya raya ku yai muku albarka Ameen
Gaban ta ne ya fadi dan ganin yadda yai fresh ya kara haske da kyau. Waye in ba Yaa Fauwaz ba. Kofar motar ya hude ta zagaya ta shiga. Ta sakar masa murmushi ya dago hannun sa da nufin tabawa dimplen dinta nan da nan ta kauce tana fadin
"Ba na hanaka ba "
Yayi dariya yace
"Au na manta."
Ta kalle shi tace
"ban zaci kai bane."
Fuska ya hade yace
"Oh kin zata wani saurayin naki ne ko?"
Murmushi tayi tace
"Lah ba haka bane Yaa Fauwaz."Bai saki fuska ba yace
"Kinga Yasmeen bana son ki tsaya kula samari tin yanzu ki bari nan gaba amman karatun ki da saura kinji ko? In lokacin yayi ni da kai na zan zaba miki dai dai dake mai hankali da nutsuwa."
Bataji dadin kalaman sa ba, dan ba haka taso yace ba. amman sai ta daure tace
"Toh! Big bro saukar yaushe?"
Murmushi yayi yace
"Yanzun nan zuwan naki ne dan ke na ajiye komai na taho ina ta kira kin ki daukar wayata ba dole na taho ba, tinda ana fushi dani."
Murmushi tayi tace
"Mota ka sauya kenan."Kallon cikin motar yayi yana murmushi Yace
"Eh guda biyu na siyo ni dake to naji Alhaji Babba yace ba yanzu zaki rike mota ba dan haka nace a barta ana kai ki unguwa but kudin motar ki na miki transfer dan nasan tinda ba ke zakina tukawa ba ko su ishaq daukar miki zasu nayi."
"Big bro kai dai baka gajiya ko?"
Yai murmushi yace
"Ai responsible dina ne."
"Kai big bro abin yai yawa amman. duk month fa sai kai min transfer kudi."
Murmushi yayi yace
"Yasmeen daban kike aguna banda Mommy ba wacce nake so a duniya kamar ki. Ina son ki u re my everything. best sis, best friend, komai fa zan iya kashe miki all I have,"Ta daga kai tana kallon sa, da kwalla ta cika idon sa, ita kam taso yace yana son ta da aure. Saurin goge idon ta tayi dan kar ya gani. Yace
"Ya maganar fushi an daina ko sai nayi frog jumping."
Kafin tai magana wayar ta tai kara tana dubawa taga Aisha ce
"Kina ina sis?""Kin ganni a wata golden kalar mota." nan mata kwatance. Dan key na gun ta na dakin su. Kallon ta yayi yace
"Ya son jikin ki? Yanzu kin saba da ckul ko?"
"Kai big bro nice mai son jiki."
Zai magana kenan Aisha ta karaso tana musu sallama amsawa sukai ta durkusa ta Gaishe shi, nan Yasmeen ta gabatar da Aisha ga Yaa Fawaz itama haka. Ganin ta a nutse yasa ya sake da ita har da yar hira sun jima gun Aisha kuwa ganin gata ga superstar kuma fans din yayen ta taji kamar tai tsuntuswa taje ta fada musu. Sai da suka dade sannan ta tafi hostel bayan ta amshi key din dakin su. Tana shiga hostel ta kira yan gidan su tana fadin yau taga Ahmad Fauwaz. Tin basu yadda ba har suka yadda sukai ta hirar tace ba ruwan su. Sun jima sannan ta kashe ta shiga tai wanka. A ranta tana fadin
"No wonder yadda Yasmeen ke bani labarin Yaa Fauwaz ashe saurayin tane. Lallai bari ta dawo."Yasmeen da Ya Fauwaz daga can fita sukai ta rakashi unguwa sai karfe takwas suka dawo makaranta bayan yai mata siyayya mai yawa da gasassun kaji yace gobe zai dawo haka ta debi kayan niki niki ta isa dakin su. Lokacin Aisha na kwance a kan gado Yasmeen ta shigo mikewa tayi ta amshi kayan hannun ta bandaki Yasmeen ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci. Kayan ta bude ta fito musu da kajin da lemuka suka fara ci sai da suka ci suka koshi sannan ta mike ta wanko bakin ta, tazo ta haye godo. Aisha da ke jiran ta dawo ta rutsa ta tace
"Ba dai bacci zakiyi ba?"

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiaLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.