*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_6⃣1⃣ - 6⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Washe gari su Yaa Fauwaz suka sauka har da su Abbas wanda sam Yaa Fauwaz bai so yazo ba. Dan sai wani bata rai ma yake. Anan gida suka sauka tsohon bangaren sa shi a bakin sa. Bai ma saka a ransa zai je gidan sa ba. Sai gidan sa dake CBN quarters ya shirya tafiya dan kar ma suce ina matar sa. Anan akai ta hidima dasu sai da suka ci suka koshi suka baje ana hira kuma ana ta wasa da dariya. Ya shiga cikin gjdan yafi sau biyar yana son ya ganta dan shi kadai yasan azabar da ya sha na rashin ta da tunanin ta ya rasa saboda me ya kira wayoyin ta duk basa shiga nan bai san layin ta ajiye ba kuma saboda shine. Dan tace koya ta ganshi tana jin sabon abu a tare dashi ko in ya kira ta sai kirjin ta ya buga.
Sai wajen uku suka dawo dan ma sunce kayan da zasu saka yana gida da kyar Asiya ta bar su suka taho sai da sukai mata alkawarin zasu zo da wuri. Shima dan Aisya ta rantse ne amman tasan in dan ta Yasmeen ne ba zuwa ma zatai ba.
Wanka kawai sukayi Aisha ta fara kwalliya Yasmeen kuma ta saka wani less din ta fari tas da shi sai green din mayafi da takalmi da jaka sai daukar kamshi take. Tana fesa turare tayi gun Mommy nan fa Mommy ta hau cewa
"Kai masha Allah. Kinyi kyau Allah kawo min lokacin bikin ki nima dai!"Murmushi kawai Yasmenn tayi na kunya ta shige jikin Mommy tana sunne kai. Anan Aisha tazo ta same ta Mommy itama ta yabe ta sannan suka fita dan Yaa Ishaq zai kai su inda za'a yi acan Ahmad Musa ne za ayi hotoro CBN quarters
Yana tsaye a jikin motar sa suka fito suka shige motar Yaa Ishaq ganin ta da yayi a yanzu ba karamin rudashi yai ba ta kara kyau da girma da cika.
Sunje an fara biki dan amarya ma tazo tayi kwalliya ana ta pictures masu rawa nayi taji wayar ta tana kara, dubawa tayi ganin number Yaa Fauwaz yasa kirjin ta bugawa da sauri ta danne shi.l. A Ranta yace
"Ya dawo ne?"
Dan ko a mafarki aka tashe ta tasan numver Yaa Fauwaz akan ta. gefe tayi ta dauka.
"Ina bakin gate ki zo!"Tsaki tayi ta ce
"Me zan maka to?"
Kin tashi tayi tana zaune ya kara kiran ta abinda yasa, ta mike ta nufi bakin gate din. Da motoci a gun da yawa dan haka ta daga waya ta kira shi
"Ni ban ganka ba.""Ina cikin wata maroon kalar Vibe!"
Ya fada dan shi tinda ta fito ya ganta ya zuba mata ido dan tayi masa masifar kyau tayi wani fresh da ita jikin ta ya murje bakace karatu take ba. Motar ta kala sannan ya isa gefen drivern kofar dake can gefe ya bude mata. Bata so ta shiga ba amman ta karasa ta shiga. Tana shiga yaja motar a guje ya yi bayan layin da ake bikin dai dai wani katon gida yai horn mai gadin ya bude. Tin daga harabar gidan zaka san gidan ya hadu dan kamar a ture haka tsarin gidam yake. Yana fitowa yai gaba dan haka itama ta fito tabi bayan sa. Da sauri sa yake tafiya har ya shige harabar gidan ya nufi wai corridor sannan ya bude kofa ya shiga wani katoton falo da zai iya cin kujeru set hudu bai cika ba. Gefe kuma dining ne babba shima. Dakin ya sha tiles da labulaye da royal furnitures duk golding kala. Dakon sai tashin kamshi mai dadi yake. Kan kujera ya fada yana fadin
"Washhh!"

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasíaLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.