23-24

599 37 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

2⃣3⃣ - 2⃣4⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlight and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Maman Abdul with number 07038****00 from _Masarautar zeedan fans_ and Our group _Hakuri da juriya online writers fans,_ tnc for ur concern with my buk nd for comment. Ina jin dadi kuma ina godiya*



Ta jima tana bacci sannan ta farka da wani sabon kukan tana me tambayar kanta shin menene aibun ta da Yaa Fauwaz bai son ta, menene lafin ta. Allah ya daura mata son sa. Amman tana addu'a Allah ya cire mata sonsa. Lallai dole ta hakura dashi. Tasan Allah yana cikin lamarin ta. Ji tayi an dafata wannan yasa ta juyo taga mama ce.

Mama tace
"kiyi hakuri Yasmeen tabbas na sani kuna son junan ku ke da wannan yaron amman kyale kyale ke dibar sa. Amman nasan zai gane bambancin aya da tsakuwa ba fata nake masa. Kiyi hakuri Allah na tare da ke."
Kai ta jinjina. Ta mike tace
'Ina su Abba ko sun tafi."

"Yanzu dai zasu tafi."
mikewa tayi tace
"Bari naje naga Mommy na daman na jima ban gan ta ba."
Ta fada tana goge fuskar ta. Mama ta bita da kallo dan Yasmeen ba dai hakuri da zurfin ciki ba. Duk da tana jin ciwon abun amman ta danne shi a zuciyar ta kamar bata ji.

Tare suka tafi dasu Alhaji Babba sai da ta fara zuwa ta gaida ummi sannan tashiga babban gida ta je gun mie mie. Sun jima sannan tayi bangaren su tana fadin
"Mommy na ina kike mommy na nayi kewar ki."

Mommy kuwa tana daki ta sha kukan ta dan Alhaji Babba ya fada mata komai. Dan haka tana jin ta, ta fito ta rumgume ta. Daki suka shiga nan Mommy ta hau lallashin Yasmeen.
"Kiyi hakuri Yasmeen nasan Yayan ki shiya saka miki son sa a ranki sannan yanzu yace baya son ki. Kiyi hakuri shawara daya zan baki shine ki rike addu'a Allah cire miki shi daga ranki. Kuma wallahi na sani ko kaffara ba zan ba Yayan ki yana son ki. Wani abun ne ya rufe masa ido har ya kasa gane hakan. nasan miji na gari nanan zuwa gareki dan ko gaba ana fatan Yayan ki ya same ku dan na fiso yai nadama ace kamar ki ake 'ki. Menene da wannan Bilkisu take ko wa? Nasan ya yaudare ki amman ki barwa Allah. Allah zai saka miki. Nasan wata rana da bakin sa zai sanar dake yana son ki. Lokacin zan so ace *Bakin alkalami ya bushe* "

Kai ta gyada hawaye na zubo mata. Mommy tace
"ki daina bana son kukan ki Yasmeen kukan ki na taba zuciya ta. "

Haka mommy tai ta kwantar mata a hankali da yamma ta shirya ta tace
"Ki tafi makaranta bana so ya dawo ya ganki har ya gane kina cikin damuwa kinji. Kicigaba da daurewa. Allah natare dake."
Mommy da Driver ne suka kai ta har school sannan ta juyo.

Duk yadda Aisha ta dinga tambayar ta lafiya dan taga duk ta canja bata fada mata ba sai cewa tayi Baba ne ba lafiya Kawai. Kuma nasihar Mommy ta shige ta dan sosai ta dage da addu'a kuma tana jin dadi sosa. Dan haka ta maida hankalin ta kan karatun ta ba ji ba gani.

Kamar yadda Abba ya fadawa Yaa Fauwaz Monday suka tafi gidan su Billy, an karbe shi hannu bibbiyu inda mahaifin Billy ya saida bikin nan da wata biyu kamar yadda Billyn da Yaa Fauwaz suka tsara ita kuma ta fadawa mahaifin ta ya sanar da iyayen Yaa Fauwaz. Sun amsa inda suka ajiye kudin komai har da sadaki dubu dari biyar kamar yadda Abba ya tambaye shi nawa yake so abayar. Da Abbah yace shi zai biya Alhaji Babba yace sam shi ya bayar da kansa. Dole saboda biyayya ne bai biya din ba ya amshi na Fauwaz din. Amman yaiwa Fauwaz transfer kudi masu yawa yace gudunmawar sa.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now