*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_4⃣5⃣ - 4⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy da Mommy nah)*
Washe gari karfe goma a gida tai masa. Lokacin Yasmeen na gyarawa Mommy daki ya shiga. Zama yayi yana fadin
"Mommy ina kwana?"Amsawa tayi. Yasmeen tana yin hanyar bedroom tace
"Ina kwana?"Ba tare da ta kalle shi ba. Oh shi ya ga ta kan sa. Wai meke damun Yasmeen ne duk ta canja masa. Sai ya tuna da lokacin baya taba karama yadda take yi da ta ganshi zatayi gun sa. Amman kalli yanzu ko arzikin kallo bai samu ba.
Mikewa yayi ya bita dakin Mommy ta bishi da harara. Zaune ya same ta a gefen gadon mommy ta zuba tagumi. cire mata hannun yayi ya durkusa a gaba ta rike da hannayen nata yace,
"Me yake damun ki?"Kai ta girgiza masa tana zare hannayen ta daga rikon da yai mata. Komawa yayi ya zauna a kusa da ita yace
"Kin hada kayan naki ne?""Nifa bana son naje wallahi Big bro zan zo dai na yini na dawo!"
"A'ah gaskiya princess zuwan ki akwai abubuwan da zai gyara min da yawa. Nayi kewar ki kanwata ina da damuwa da yawa na rasa wanda zan fadawa. Ke kuma mai ban shawara kin juyan baya. Dan Allah fada min me nayi miki?"Ya karasa maganar cikin lallashi. Kai ta langwabe tace
"Ni kam me zakai min Big bro! Rayuwa ce ta canja kawai.""To naji yanzu zaki zo din?"
Shiru tayi yace,
"Ba zan boye miki halin da nake ciki ba dan ke masoyiya tace, ina cikin matsala tsakani na da Billy sam Billy ba abinda ta iya please in kinzo kina sata kuma kina koya mata abu nasan kan ki dawo zata iya wani abun please my princess!"Ya karasa maganar yana mai lankwasar da kan sa abin tausayi. Kasa magana tayi dan ita har yau sai dai in bata ga Yaa Fauwaz ba amman indai taga Yaa Fauwaz ji take mikin dake zuciyar ta ya dawo sabo dan haka bata son tana ganin sa dalilin da ya hanata zuwa gidan sa kenan. Gashi yanzu yazo yana son taimakon ta taje tai masa hutun ta acan kenan kullum cikin jinya zata kasance.
Ta sha yin sabo akan meyasa har yanzu son Yaa Fauwaz bai fita a zuciyarta ba. wanda ita kanta haushub kan ta take akan son da take masa bare kuma wani in yasan a halin da take. Tasha boya tai kuka in abin ya taso mata dan tasan in har Aisha tasan akan me take kuka ta shiga uku. Dan haka yanxu ya zatai.
Murya sa ta katse mata tunani da yace
"Dan Allah kada kice A'ah!"Sam ba zata iya cewa Yaa fauwaz A'ah ba dan yadda yake da daraja agun ta dan ita ba zata so ta ganshi a wani hali mara kyau ba. Dan haka tace
"Shikenan! Amman sai Mommy ta yadda!"A ransa yace
"Allah yasa ta yadda!"Mommy na falo duk tana jin su. Tai murmushi tace
"Fauwaz kenan zama ka dawo kan hanya ne!"Nan ya dauko wata katuwar trolley din ta ya bude wardrobe din Mommy yana dibar kaya ko wanne yana zubawa. Mommy ce ta shigo ta saya kallon sa tace
"Kai kuma lafiya kake dibar kayan ta."

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.